Daily True Hausa
(MANUFA) – BISA TSORON ALLAH DA KISHIN KASA:
Kare hakkin talakawa da masu rauni ta hanyar watsa gaskiya, ba wai abin da masu iko ke so a ji ba.
09/07/2026
Australia da Indiya Sun Cimma Yarjejeniyar Uranium, Sun Ƙara Ƙarfafa Haɗin Gwiwa
• Yarjejeniyar za ta ba Australia damar fitar da uranium zuwa Indiya domin samar da makamashi
• Shugabannin ƙasashen biyu sun kuma tattauna tsaro, kasuwanci da fasahohi masu tasowa
• Ana kallon yarjejeniyar a matsayin wani sabon ci gaba a alaƙar ƙasashen biyu
Australia da Indiya sun sanar da wata muhimmiyar yarjejeniya da za ta ba Australia damar fitar da sinadarin uranium zuwa Indiya domin amfani da shi wajen samar da makamashin nukiliya na zaman lafiya. Hakan na daga cikin matakan da ƙasashen biyu ke ɗauka na ƙara ƙarfafa alaƙar tattalin arziki da haɗin gwiwa a yankin Indo-Pacific.
Kamar yadda Daily True Hausa ta tattaro daga Reuters, an sanar da yarjejeniyar ne yayin ziyarar aikin da Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya kai Australia, inda ya gana da Firaministan ƙasar, Anthony Albanese. A cewar shugabannin biyu, yarjejeniyar za ta taimaka wa Indiya wajen cimma burinta na faɗaɗa samar da makamashin nukiliya domin biyan buƙatun makamashi da rage fitar da hayaƙin da ke sauya yanayi.
Rahotanni sun nuna cewa baya ga batun uranium, shugabannin sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi da s**a shafi tsaro, makamashi mai tsafta, ma'adanai masu muhimmanci, fasahar zamani da bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu. Haka kuma, an ƙarfafa kamfanonin Australia su ƙara zuba jari a manyan ayyukan raya ƙasa a Indiya.
Firaministan Australia ya bayyana cewa dangantakar ƙasarsa da Indiya na ƙara ƙarfi, yana mai cewa haɗin gwiwar zai amfani tattalin arzikin ƙasashen biyu tare da ƙarfafa zaman lafiya da tsaro a yankin. A nasa ɓangaren, Firaministan Indiya ya ce ƙasashen biyu sun zama "abokan hulɗa na amana", yana mai jaddada cewa za su ci gaba da aiki tare wajen bunƙasa kasuwanci, fasaha da makamashi.
Masana harkokin ƙasa da ƙasa na ganin cewa wannan yarjejeniya na nuna yadda Australia da Indiya ke ƙara kusantar juna ta fuskar tattalin arziki da tsaro, musamman a lokacin da ake fuskantar sauye-sauye a tattalin arzikin duniya da kuma buƙatar samar da makamashi mai ɗorewa.
Rahotanni sun fito daga: Reuters.
Cliquez ici pour réclamer votre Listage Commercial.
Site Web
Adresse
Dakar