HNN Hausa

HNN Hausa

Share

15/04/2024

Buni ya mayar da martani ga kazamin fada da ya faru tsakanin sojoji da mahaya Keke

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi kira da a kara samun daidaito tsakanin sojoji da fararen hula a Gashu’a.

Buni ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake mayar da martani kan wata arangama tsakanin sojoji da mahaya Keke NAPEP a ranar Lahadi a garin Gashu’a wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku, tare da jikkata da dama.

Ya bayyana da cewa abin takaici ne yadda irin wannan lamari ke faruwa a daidai lokacin da jihar ke samun zaman lafiya a fadin jihar.

"Abin bakin ciki ne kuma abin takaici ne yadda ake asarar rayuka a cikin wani yanayi da za a iya kaucewa," in ji shi.

08/04/2024

BAYANI AKAN ZAKKAR FIDDA KAI (ZAKÃTUL FITR)

Tare da: Dr. Jabir Sani Maihula (Hapizahullah)

06/04/2024

'Yan sanda sun ceto mutane 100 da aka yi garkuwa da su a Katsina

28/03/2024

Duk manufofin gwamnati Tinubu alama ce na raba Najeriya ne, ba hada kan Najeriya ba, wannan dalilin yasa Tinubu ya ɗako na uku a kasa daga yankin inyamurai don tabbatar da manufarsa ta Raba kasa. Kowa ya sani cewa, Akpabio yana da zarge-zarge da ake masa na cin hanci da rashawa amma duk da haka ya dako shi ya bashi mukamin shugaban majalisar Dattawan Najeriya.

Kowa yaga yadda ake kwashe wasu muhimman ma'aikatu daga Arewacin Najeriya ana kaisu kudancin kasa, kamar wasu sashi na babban Bankin kasa, da wasu sashi na zirga-zirgar jirgin saman Najeriya.

Idan ba haka ba taya zai zama ana cikin zaman lafiya zai kwashe muhimman wurare ya mayar da su yankinsa duk da cewa, ba kaunarsa akeyi ba a kudancin kasar. Inji Shu'aibu Mungadi.

Ya bayyana haka ne a wani shirin talabijin na farin wata da ake gabatarwa a gidajen Rediyo Vision FM kwanakin baya.

Want your business to be the top-listed Media Company in Zaria?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Zaria