Caliphate Ambassadors Initiative

Caliphate Ambassadors Initiative

Share

04/06/2025

*JADAWALIN YADDA ZA KA RIBACI RANAR ARFA,
GA SHI NAN KAMAR HAKAN :-

1. Bayan Ka yi barci a kan lokaci
2. Ka tashi Ka samu falalar sahur
3. Ka yi addu'a kafin alfijir ya keto
4. Ka yi Istigfari Ka nemi tuba
5. Ka halarci sallar Asuba cikin jam'i
6. Ka zauna bayan salla kana azkar
7. Ka daure cikin Ibada har Rana ta hudo
8. Ka tashi Ka yi raka'a biyu Ka samu ladan Hajji da Umra
9. Ka Dan kishingida don samun karfin yin Ibada a wannan yini
10. Kana tashi Ka yi sallar Walaha, raka'a 4/6/8
11. Nau'anta salon Ibadarka;
yi salla
yi karatun Kur'ani
yi kabbara
yi addu'a
yi zikirai
12. Jeka sallar Azahar Ka yi "Sunan Rawatib" kafin salla da bayan salla
13. Samu lokaci Ka Kara karanta AlKur'ani
14. Ka yawaita Hailala "La'ilaha Illal Lahi Wahdahu La Sharika Lahu Lahul Mulku wa Lahul Hamdu wa Huwa ala Kulli Shai'in Kadir"
15. Halarci salla La'asar a jam'i,
16. Yi Azkar din yamma
17. Yi karatun Kur'ani har zuwa yamma likis
18. Koma ga addu'a, roki duniya da Lahira, Kada Ka roki duniya kadai
19. Yi addu'ar Ka zama cikin 'yantattun wannan yini
20. Ka kaskantar da kanka ga Allah, Kada ka yi zaton ka sha gaban wasu a wajen Allah don ibadarka
21. Yi buda Baki Ka Kara da addu'o'i ga kanka/iyalanka/yanuwanka/ Musulmi/ kasarka

Allah Ya karba mana kadan, Ya ba mu Mai yawa Ya Kareem.

28/05/2025
Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Sokoto?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Fodio Road
Sokoto