Abadio
12/09/2024
02/05/2024
الحمد الله على كل حال
Ina Mai amfani da wannan dama da Kuma lokaci wurin mika godiya ta zuwa bangarori da al'uma da Su ka taimaka wurin halarta Da jibintar al'amarin biki na da ya gudana ranar Juma'ar 26-04-2024 17 Shawwal 1445 AH.
Godiya zuwa ga al'uma musamman Mai gida kuma uba Mal. Ado Sule Lampo bisa girmamawa Da karamci da ya nuna min wurin amincewa da Ni ya bani damar aurar 'Yar sa. Allah ya saka da mafificin alkhairi ya sanya ya zama sanadiyar Shiga aljannah gidan aminci kamar yadda Manzo صلالله عليه و سلم ya fada .
Sai kuma Daraktan Kungiyar Agaji na Aliyu Ban Abi Dalib Islamic Organization Mal. Hassan Abdussalam wadda ya yi iya kokarin sa wurin ganin wannan al'amari ya tabbata, Allah ya saka ya kuma sanya a mizanin ayyukan alkhairi.
Daga Yan uwa akwai Aisha Jibril 'yar uwa kuma abokiyar shawara Allah ya saka da alkhairi tare da 'yar uwa Maryam Jibrin
Daga cikin abokai kuwa ina mika godiya gare ku baki daya wanda sanadiyar ku al'amarin ya gudana fiye da yadda na ke tsammani. Daga cikinsu akwai Yakubu Audu Ibrahim YKB Mohammed Hussaini Mohammed da Abdullahi Adamu Usman Serzey, Adamu Garba Ali Big boy Yahaya Abdullahi Org. Sec. FAG OF Abadio Zakariya Abdullahi Baba Det. Leader FAG OF ABADIO, waɗannan ba abin da zan iya saka mu ku da shi sai da na ce Allah ya saka mu ku da alkhairi. Da dai waɗan da ban samu damar ambaton sunayen su ba. Allah ya saka da alkhairi ya kuma karbi addu'o'in ku. Allahumma ameen.
Musa Abdullahi Maina
Follow the WhatsApp channel of ABADIO Media. For more updates, videos, Audio and many more:
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the school
Telephone
Website
Address
Aliyu Bn Abi Dalib Islamaic Organisation Potiskum
Potiskum