Danbaiwa Collection
25/07/2019
🔴 DA DUMI DUMI - Shugaban kasar Tunisia Beji Caid Essebsi ya mutu yau ya na da shekaru 92 bayan fama da rashin lafiya
05/07/2019
Barrister Audu Bulama bukarti yayi karin haske akan shari'ar Abba da Ganduje.
Yaushe za a kammala shari'ar?
Barrister Audu Bulama Bukarti ya yi mana bayanin abubuwan da za su faru daga ranar 13 ga watan Yuli idan kotu ta koma zamanta kamar haka:
Masu kara za su gabatar da shaidunsu
Daga nan kuma sai a bai wa wadanda ake kara su ma su gabatar da nasu shaidun
Kotun za ta saurari abin da ake kira jawaban karshe, inda wadanda ake kara za su fara jawabin karshen
Daga nan ne kuma sai a bai wa bangaren masu kara su gabatar da nasu jawabin na karshe
Kotun za ta sake bai wa wadanda ake kara damar mayar da martani kan jawabin karshe da masu kara s**a yi
Bayan sauraron jawaban karshe da martani sai kotu ta sa ranar yanke hukunci.
Daya daga cikin hukunci uku da kotu za ta iya yankewa
Kotu za ta iya korar karar da Abba Kabir Yusuf, inda za ta tabbatar da Gwamna Ganduje da cin zabe
Kotu za ta iya ayyana Abba Kabir Yusuf da wanda ya ci zabe
Kotun za ta iya soke zaben domin a sake
Idan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben ta yanke bai gamsar da daya daga cikin bangarorin ba, sai su garzaya kotun daukaka kara.
Yaushe za a yanke hukunci?
Ita dai wannan kotun ta sauraron kararrakin zaben na da kwanaki 180 ta yanke hukunci daga ranar da aka shigar da karar.
Kotun Daukaka Kara na da kwana 60 ta yanke hukunci, inda ita ma Kotun Koli take da kwanakin 60 ta yanke nata hukuncin.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Lagos
DEIRAHDUBAI