RADIO IDI
Matsalar gaba....
Daga bakin Sheikh Ja'afar Mahmud Adam (Rahimahullah).
Ayi sauraro lafiya, kuma in har an ƙaru, a yaɗa ko zamu faɗakar da juma.
26/08/2021
26 ga watan Agusta.
Wacce karin magana kuke da ita a yau ta .
08/08/2021
Shugaban Ƙaramar hukumar Amuwo Odofin a jahar Legas yayi alƙawarin naɗin muƙamai ga Al'ummar Arewa, a lokacin da s**a ziyarce shi.
Ƙungiyar Arewa Community Ta Gaskiya Association dake yankin ƙaramar hukumar Amuwo Odofin a jahar Legas, ta taya shugaban karamar hukumar Amuwo Odofin, Dr Valentine Oluwaseyu Buraimoh murnar sake zaben sa. A lokacin da s**a ziyarci Shugaban, kungiyar ta gabatar da Sabo kuma Zaɓaɓɓeɓen Sarkin Hausawa na Festac H.R.H Alh. Mustapha Musa ll (Uban Tafiya), wanda kuma shine shugaban kungiyar Arewa Community Ta gaskiya Association ƙaramar hukumar Amuwo Odofin, ga Dr Buraimoh .
Da yake jawabi, Sarkin Yakin Festac, Dakta Isa Jimeta ya ba da tabbacin cikakken biyayya ga al’ummar Arewa a karamar hukumar Amuwo Odofin, ga sabuwar gwamnatin Dr Buraimoh. Da yake ba da gudummawa, Sabon Sarkin Hausawa na Festac, H.R.H Alh Mustapha Musa ll (Uban Tafiya) ya sake tabbatar wa Shugaban cewa membobinsa za su tallafa wa Gwamnatinsa ta hanyar ba shi cikakken haɗin kai. Sarkin Hausawa ya shaidawa Shugaban cewa mutanen sa za su kasance masu bin doka da oda.
A nashi jawabin Shugaban Ƙaramar hukumar ya shaidawa
membobin kungiyar Arewa Community don nuna goyon bayan su ga All Progressive Congress, APC, da kuma addu'o'i da s**ayi a zabukan da aka gudanar kwanan nan a jihar. Shugaban ya yi alƙawarin tallafa wa membobin Ƙungiyar Arewa kuma ya tabbatar musu cewa zai naɗa ɗaya daga cikinsu don ya kasance cikin Gwamnatin sa. Dangane da rushe kasuwar (2nd gate) da aka fi sani da kasuwar Agboju, shugaban ya yi alƙawarin dubawa da kuma yin wani abu game da rushe wannan kasuwar ga membobin Arewa Community, waɗanda abin ya shafa .
06/08/2021
"Yaɗa hotunan da bidiyoyinta da Ire-iren hotunan laifi ne"
"Ɗiyar Sarkin bata fi ƙarfin doka ba, kuma ya kamata ace ta nuna ita ƴar gidan manya ce idan tana neman al'barka a aurenta."
A faɗar Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Harun Ibn Sina.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Lagos
Opening Hours
| Monday | 10:00 - 17:00 |