Yusuf Rabeh Jibia

Yusuf Rabeh Jibia

Share

14/05/2026

Mu 9 ne sojojin da Yan tawaye s**a K**a a lokacin da muka je yaqin kwantar da tarzoma.

A cikin mu 9 ni kadai ne MUSULMI, sai kiristoci 6 sai mutum 2 da ba su yarda da samuwar Allah ba watau Atheists. Aka Kai mu sansanin ajiye fursunonin yaki mun Kai mu 500.

Wajen da aka rufe mu ko dabba ba za ta iya haqurin kwana a wajen ba. Duk dare wasun mu a tsaye suke kwana don sauran su samu wajen kwanciya. Ga Tsananin sanyi da sauro.

Duk Rana babban sojojin da ke tsaronmu zai sa su fiddo mu su kashe na kashewa sannan Kuma su yi ta wulaqanta mu.

Bayan wata 3 na tsananin wahala a wajensu sai layin Wanda za a harbe ya zo kan mu. An fiddo mu za a kashe sai babbansu ya tambaye mu "Shin yanxu akwai wanda za ku Kira ya Hana mu kashe ku?". Duk mu ka yi tsit saboda kowa na tsoron yin magana don Kar a fara da shi. Sai Kuma a Raina na ga to ai ko mu amsa ko kar mu amsa sai dai an kashe mu, kawai sai na daga murya na ce "eh muna da Wanda zai iya Kare mu". Cikin mamaki Oga Bunda (Shugaban sojojin da ke tsare da mu) ya kalle Ni, kowa sai ya Sha jinin jikinsa saboda na 6allo ruwa. Abin da ya fi bani mamaki sai na ga ba fushi a idon Bunda, sai ya ce in matso kusa da shi. Na zo, ya ce min "waye gareka da zai Kare ka?". Bansan lokacin da na ce Masa "Allah Mai girma da izza shi kadai ne zai iya ceton mu".

Jin amsa ta sai Bunda ya fashe da dariya 🤣 ya tambaye Ni wane addini na ke bi? Na ce Masa Ni MUSULMI ne. Ya ce min shi bai da Addini saboda har yanxu duk addinan Duniya sun kasa nuna shi wannan Allahn da suke taqama da shi.
Tabbas ba Allah,duk Wanda ya ce Maka akwai Allah to maqaryaci ne. Cikin zumudi wannan abokan nawa da aka k**a mu tare Wanda Suma ba su da Addini s**a ce ma Oga Bunda "yalla6ai mun Sha fada masu wannan maganar ta ba Allah Amma sun qi yarda" Bunda ya tambaye su shin Suma Atheists ne? S**a eh. Ya ce su koma gefe, ba za a kashe su a yau ba sai watarana. Jin haka sai 3 daga cikin kiristoci su ka ce su ma Atheists ne watau ba su da Addini😂. Su ma aka ce an fasa kashe su a ranar.

Bunda ya dube mu mu 4 ya ce " Kuna da yaqinin cewa Allahnku na iya cetonku a yanzu"? Na ce "kwarai Kuwa, ai ba abun da ya gagari Allah." Ya ce "ba abin da ya gagare shi? To shikenan"ya dubi yaransa Sojoji da Yan fursanar sun Kai mutane Dubu ko sama da hakan ya ce "tun da wannan mutumin ya ce Abin bautarsa Yana iya yin komai, gobe k**ar yanxu zan yi Masa jarabawa, in har Ubangijinsa ya ba shi Nasara to ku shaida cewa Ni Bunda na Yi rantsuwa da uwata zan sake su su tafi gida, Amma in ya Fadi, to Zan yi masu azaba sannan in daure su a Rana har sai sun mutu don ungulu su Sami abinci.".
Na ce "na yarda da hakan".

Aka tarkata mu zuwa dakunanmu. A daren ba mu yi barci ba, su kiristoci na Addu'ar Nasara Nima Ina kalar tawa ibadar da rokon nasara.

Washegari aka fiddomu zuwa wajen da ake taruwa, amma abun mamaki sai muka ga tsakiyar filin an ajiye wata jib sabuwa fil, ko leda ba a cire ma kujerun ba. Full option.
Mu ka hau layi muna jiran oga ya fito. Sojoji sun tsare mu k**ar guduwa za mu yi, bayan sun San ko kyale mu s**a yi yunwa da qishi ba zasu bar mu mu iya guduwa ba.

Can sai Oga Bunda ya iso. Ya ce ina nake? Daman Ina layin gaba kawai sai na je wajensa. Ya ce "Mai Allah ai ka iya mota ko?". Na ce ",eh".

Ya sa hannu aljihu ya fiddo makullin jip ya damqa min ya na murmushin mugunta ya ce "je ka gyara parking din motar can mu ga in Allahn ka zai iya cetonka". Sauran sojoji s**a fashe da dariyar mugunta.

Ina ganin dariyar muguntar su sai na gane cewa wataqila bom ne s**a hada da motar yanda kunna ta zai tayar da bom din. Na fara tunanin ko dai in haqura, Amma sai nayi tunanin cewa ai qara mutuwar bom akan azabar da Zan Sha kafin su kashe Ni. Wata zuciyar sai ta raya min cewa da bom ne da tsohuwar mota za su kawo ba sabuwa fil ba. Wannan tunanin Shi ya bani qwarin gwuiwa na nufi motar.
Kafin in sa makulli sai da na yi bisimillah. Cikin mamaki qofa ta bude na Shiga. Na qara yin bisimillah na sa makullin a ignation na murda, kawai sai mota ta tashi, na sa giya na yi ribas na gyara parking din. Sannan na fito na nufo oga. Ha'a, ai sai na ga oga yana ja da baya, duk sojojin sun tsorata, Kuma na kasa Gane abin da ya firgita su. Su Kuma Yan gidanyari sai Kiran sunana suke suna jinjina.

Oga ya zo gabana sai na ga ya duqa gwuiwa biyu Yana cewa " na yarda akwai Allah, na yarda abun bautarka ya Kai maqura".

Na ce"oga Ni ban Gane ba, miye abin mamaki don na tuqa mota?"

Ya ce "ai motar da ka kunna,ka Kuma tuqa,ba ta da Inji!

Yusuf Rabeh Jibia

09/03/2026

Tsautsayi ko son banza?

Muna cikin motar haya da abokina sai wani da muke zaune a seat guda ya fiddo iPhone 14 pro max, ya ce ma abokina mamansa ce ba ta da lafiya Kuma suna buqace da kudi shi ya sa ya ke son ko Dubu 75 ne don su biya kudin da za a Yi ma ta tiyata.

Ko da Aboki na ya ji an ce dubu 70 sai ya kar6i wayar ya na duba ta don ya tabbatar ko jabu ce. Amma abun mamaki sai mu ka ga komi na ta lafiya Lau ne, ga Kuma hoton gayen a wallpaper. Ko da na ga haka sai na ce ma abokina "anya wannan wayar ba ta sata ba ce?". Sai ya ce min ai ko ta sata ce in ya saye ta zai je a yi Mata flashing ne, sannan ya sake mata kes sai ya yi saurin sayar da ita.

Shapshap s**a yi ciniki abokina ya nemi ragi aka sayar Masa da ita dubu hamsin. Take abokina ya Yi ma gayen tiransifa, Ni dai Ina riqe da waya a tsorace ina Tunanin ba abin da zai sa mutum ya sayar da iPhone dubu 50 in har ta sa ce.

Muka sauka daga bus din muna daga ma abokin cinikin mu hannu har s**a tafi.

Muka zauna qarqashin wata bishiya abokina na qara dudduba wayar, Yana cikin dubawa sai wayar ta dauke, sai muka yi tunanin qila chaji ne, na qar6i wayar na dan duba kwatsam Kuma wayar sai ta kunnu da kanta, sai mu ka ga screen din ya nuna "searching... Sai abokina ya yi murmushi ya ce "yawwa ta kunnu😁. Da ma wayar tana hannuna, ba a yi minti 2 ba sai rubutun ya 6ace wani ya fito. Tracking.. Tracking... Tracking kawai ta ke nunawa🙄 Ina ganin haka sai na miqa Masa wayarsa, Amma sai ya Yi k**ar bai ga Ina miqo Masa ba. Sai na ce Masa "amshi wayarka!". Wai sai ya ce min "ba hannunka take ba, ka riqe ta har ta gama tracking din ta Mana"🙄. Na ce Masa "tayi tracking din mi🙄? Malam dalla riqe wayarka". Sai ya ce "haba bar ta wajenka har ta gama tracking din network dinta, ba Ina Nan ba,ko guduwa zan Yi ne?🙄". Na ce "Kai Malam amshi wayarka ta Yi tracking din network din a hannunka, na tura Masa ita cikin aljihu na Yi gaba na bar shi baya.

Ha'a! Kawai ba sai na ga abokina ya wuce ni a sukwane ba🤔 ai Nima sai na b

18/10/2025

🤣

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Katsina