Katsina Reporters
11/07/2026
TUNATARWA GA DUK MASU HALARTA
Hukumar National Social Investment Program Agency (NSIPA) tare da haɗin gwiwar Rotex Consulting Limited na tunatar da duk waɗanda s**a yi rajista, masu ruwa da tsaki da kuma ‘yan jarida da su halarci taron wayar da kai da ganawa da masu ruwa da tsaki kan Shirin Horar da Sana’o’i da Koyon Ƙwarewa na jihohin Kano, Katsina da Jigawa.
Rana: Talata, 14 ga Yuli, 2026
Lokaci: Karfe 10:00 na safe
Ana gudanar da shirin ne ƙarƙashin jagorancin Dr. Bernard M. Doro, Ministan Jinƙai da Rage Talauci na Tarayya, tare da goyon bayan Assoc. Prof. Badamasi Masi Lawal, Shugaban Hukumar NAPA.
Jigo: Ƙwarewa a Aiki Domin Gobe: Ƙarfafa Matasa, Gina Nijeriya Mai Ƙarfi.
Wannan shiri na daga cikin manufofin Renewed Hope Agenda na Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, domin bai wa ‘yan Najeriya ilimin sana’o’i da dabarun kasuwanci da za su taimaka musu su dogara da kansu.
A taimaka an iso da wuri domin yin rajista da fara shirin a kan lokaci.
Tallafa Wa Al’umma, Samun Ingantaccen Rayuwa, Gina Nijeriya Mai Ƙarfi.
11/07/2026
Yadda Gwamnatin Dikko Radda ke ci gaba da aikin sake ginda hanyar Filin Polo zuwa Ring Road a garin Katsina.
10/07/2026
Hotunan bikin Khalifa Bishir Mangal da amaryarsa Surayya Sani Yakasai Allah Ya bada zaman lafiya.
📸 -BP Photography.
10/07/2026
Ministan Gidaje na Najeriya Engr. Muttaqa Rabe Darma, Ya Karɓi Baƙuncin Tawagar GIZ Ta Jamus a Abuja
Ministan Gidaje da Raya Birane na Najeriya, Injiniya Muttaƙa Rabe Darma, ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga Hukumar Haɗin Gwiwa da Raya Ƙasashe ta Jamus (GIZ), a wata ziyarar girmamawa da aka kai masa a Abuja.
Tawagar ta samu jagorancin Dr. Karin Jansen, Sakatariya ta Farko kuma Shugabar Haɗin Gwiwa ta GIZ, inda s**a kai ziyarar ne ranar Juma'a, 10 ga Yuli, 2026. Ziyarar ta kasance wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da GIZ a fannin gidaje da raya birane.
Ana sa ran tattaunawar da bangarorin s**a gudanar za ta ƙara bunƙasa haɗin gwiwa kan shirye-shiryen raya birane da samar da ingantattun gidaje, tare da tallafa wa manufofin gwamnatin tarayya na bunƙasa ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.
— Katsina Reporters.
10/07/2026
Shugaban APC Na Ƙasa Nantawe da Masari Sun Ƙaddamar da Kwamitin jagorancin kungiyar Tinubu Door-to-Door a Abuja
Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, tare da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, sun ƙaddamar da Kwamitin Zartarwa na Ƙasa na Ƙungiyar President Bola Ahmed Tinubu Door-to-Door Movement, a wani mataki na ƙarfafa shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Katsina Reporters ta samu cewa, manufar ƙungiyar ita ce tattara jama'a daga matakin ƙasa zuwa unguwanni da rumfunan zaɓe domin wayar da kan al'umma da kuma ƙarfafa goyon baya ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027.
Shugabannin ƙungiyar sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryen wayar da kai da haɗa kan magoya baya a sassa daban-daban na ƙasar, domin bunƙasa ayyukan ƙungiyar da tallafa wa manufofin jam'iyyar APC.
— Katsina Reporters.
09/07/2026
Bola Tinubu yafi kowane dan takara cancanta a zaben 2027 - Sheikh Abu Ammar
Shugaban Hukumar Hisbah ta jihar Katsina Sheikh Abu Ammar, ya bayyana cewa shugaba Tinubu shi ne ya fi cancanta da ci gaba da jagorantar Najeriya bayan zaɓen shekarar 2027.
Sheikh Abu Ammar ya ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarori musamman a fannin tsaro, inda ya ce an samu raguwar matsalolin rashin tsaro idan aka kwatanta da shekarun baya.
Ya ƙara da cewa matakan da gwamnati ke ɗauka sun fara haifar da sauyi fiye da baya a sassan Najeriya
Malamin ya buƙaci 'yan Najeriya da su ci gaba da bai wa gwamnati haɗin kai wajen tunkarar ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
A cewar Abu Ammar Tikitin Muslim-Muslim da aka samar na Tinubu/Kashim ya biya shi.
— Katsina Reporters.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
No. 12, Ramadan Plaza Ƙwaɗo Ring Road Katsina
Katsina