Blueprint Hausa
Blueprint Hausa jarida ce mai kawo ingantattun labarai cikin harshen Hausa domin ilimantarwa da faɗakarwa da nishaɗantarwa daga gida Nijeriya da ƙasashen waje don sanin halin da duniya take ciki.
09/02/2026
Kogunan Gusa Shine Amsa A Jihar Zamfara 2027
A yau Jihar Zamfara na bukatar shugaba nagari, mai hangen nesa, mai tausayi ga talaka, kuma wanda ya san halin da al’umma ke ciki.
Ba kowa ba ne zai iya ɗaukar wannan nauyi, sai mutumin da Allah ya horewa baiwa da basira, kwarewa, da kuma kishin jama’a. Daga cikin irin wadannan mutane, sunan Kogunan Gusau ya fito fili ba tare da shakka ba.
Kogunan Gusau mutum ne da ya shahara wajen taimakon jama’a, gina al'umma, da tsayawa tsayin daka wajen kare muradun al’umma. Tarihinsa ya nuna cewa shi shugaba ne mai sauraron jama’a, wanda ke da fahimtar matsalolin tsaro, tattalin arziki, ilimi da walwalar al’umma. Ba wai kawai a iya magana ya tsaya ba, faɗa da aikatawa sunanshi.
A tsawon lokaci, Kogunan Gusau ya nuna jajircewa, hakuri da kwarewa a harkokin shugabanci da siyasa. Yana da fahimta mai zurfi game da jihar Zamfara daga karkara zuwa birane, kuma yana da zuciyar haɗa kan jama’a ba tare da nuna bambanci ba. Wannan shi ne irin shugabancin da Zamfara ke nema a wannan lokaci mai muhimmanci.
Muna kira gare ka, Kogunan Gusau, da ka amsa kiran al’umma. Ka tsaya ka fafata domin karɓar kujerar Gwamnan Jihar Zamfara a 2027 insha Allahu, domin mutane da dama sun yarda kai ne mutumin da ya dace da wannan aiki.
Zamfara na bukatar shugaba mai tsoron Allah, gaskiya, hangen nesa da kuma karfin gwiwar kawo sauyi, kuma wadannan siffofi suna tare da kai.
Allah Ya taimaka, Ya ba da nasara, kuma Ya sanya abin da ya fi alheri ga Jihar Zamfara da al’ummarta.
Muhammad Nura
Chairman Koguna Alheri Ne
07/01/2026
Masu Yada Karya Akan Gwamna Bauchi Bala Muhammad Ba za su yi nasara ba - Arewa Democratic Agenda
Muna jan hankalin jama’a game da wani labari na ƙarya da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin cewa an bai wa wata ƙungiya da ake alaƙantawa da ta’addanci kuɗi daga Gwamnatin Jihar Bauchi. Wannan labari ba shi da tushe, b***e Malama, babu hujja, kuma ƙarya ce tsagwaronta.
Babu wani lokaci da Gwamnatin Jihar Bauchi, ko Mai Girma Gwamna Sanata Bala Mohammed, ya amince ko ya ba da umarnin bai wa kowace ƙungiya da ke da alaƙa da ta’addanci kuɗi, ko ta kowace hanya. Wannan zargi an ƙirƙire shi ne kawai domin ɓata suna, yaudarar jama’a, da tayar da fitina.
Haka kuma muna kira ga jama’a da su yi watsi da irin waɗannan labaran ƙarya, su kuma guji yaɗa bayanan da ba su tantance ba.
Gwamnatin Jihar Bauchi ta himmatu wajen tabbatar da tsaro, zaman lafiya, da bin doka da oda, tare da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro na ƙasa.
Duk wanda ke yaɗa wannan labari na ƙarya, yana da niyyar ɓata sunan shugabanci da ya samu amanar jama’a, kuma hakan ba zai hana gwamnati ci gaba da ayyukan alheri da ci gaban jihar Bauchi ba.
Gaskiya ce za ta yi nasara a kowane lokaci.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Katsina