Arewa Daily Updates

Arewa Daily Updates

Share

Photos from Arewa Daily Updates's post 05/02/2026

KADAN DAGA GUDUNMAWAR DA HON. BASHEER ABDULLAHI (A.A BASHEER FUNTUA) YA KE BA DAWA A BANGAREN TAIMAKON AL’UMMA, MUSAMMAN GA WAƊANDA IFTILA’IN ’YAN BINDIGA YA SHAFA.

A tsawon lokaci daban-daban, Hon. Basheer Abdullahi, wanda aka fi sani da A.A Basheer Funtua, ya kasance a sahun gaba wajen ba da gagarumar gudunmawa ta jin ƙai da tallafi ga al’umma, musamman ga mutanen da iftila’in ’yan bindiga ya rutsa da su. Wadannan mutane s**an tsinci kansu cikin mawuyacin hali, ba tare da wata mafita ko ƙarfin yin wani abu ba.

A irin waɗannan lokuta masu matuƙar wahala, Hon. A.A Basheer Funtua ya nuna kyakkyawar zuciya da tausayi ta hanyar shiga tsakani domin rage raɗaɗin da al’ummar ke fuskanta. A wasu lokuta, ya ɗauki nauyin biyan kuɗin fansa domin kubutar da waɗanda aka sace, tare da tallafa wa iyalansu ta fuskar ciyarwa da kula da buƙatunsu na yau da kullum a lokacin da suke cikin damuwa, Haka kuma, bayan fitowar waɗanda aka sace, an kula da lafiyarsu ta hanyar ɗaukar nauyin jinya da sauran buƙatun lafiya domin tabbatar da walwalarsu.

A baya-bayan nan, Hon. Basheer Abdullahi ya ɗauki nauyin fansar kimanin mutane goma (10) da ke hannun ’yan bindiga. Daga cikin waɗannan mutane akwai mata masu juna biyu, mata masu jarirai ƙanana (har da jaririn da bai wuce watanni huɗu ba), da kuma tsofaffi maza da mata. Mutanen sun fito ne daga yankuna daban-daban da s**a haɗa da Unguwar Shanu, Bakori, Bagari, da sauran Unguwanni na cikin garin Funtua, da kuma wasu bayin Allah daga Unguwar Kurami ta Bakori Local Government.

Domin samun ’yancin wadannan mutane, Hon. A.A Basheer Funtua ya kashe kuɗaɗe masu yawa da s**a kai Naira Miliyan Goma Sha Biyu (₦12,000,000), tare da bayar da sabbin babura guda biyar (5) ƙirar Boxer, domin cika sharuddan da aka gindaya wajen kubutar da su.

Wannan aiki na alheri ya ƙara nuna irin tausayawa, jajircewa da sadaukarwa da Hon. Basheer Abdullahi ke nunawa ga al’umma mabukata, maza da mata, a kowane lokaci, ba tare da neman yabo ko bayyanawa ba. Ayyukansa na jin ƙai suna kasancewa cikin natsuwa da gaskiya, domin faranta ran Allah da tallafa wa bayinSa.

Muna miƙa godiya da addu’a ga Allah Maɗaukakin Sarki, muna roƙonSa da Ya ƙara ba shi lafiya, nisan kwana da ikon ci gaba da ayyukan alheri da yake yi wa al’umma a kowane lokaci. Allah Ya saka masa da alheri, Ya kuma sa waɗannan ayyuka su zama sanadin zaman lafiya, haɗin kai da kwanciyar hankali a cikin al’umma baki ɗaya.

Photos from Arewa Daily Updates's post 31/12/2025

KUNGIYAR CI-GABAN GARIN DIKKE TA KARRAMA SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR FUNTUA HON AUDU GOYA DA HON BARA'U YUSUF MAIKWAI DIKKE....

Kungiyar Ci gaban Garin Dikke, Mai Suna Dikke Consultative Forum DCF
Dake Karamar Hukumar Funtua Ta Karrama Shugaban Karamar Hukumar Funtua Hon Abdulmutallab Jibrin Sulaiman Goya da Hon Bara'u Yusuf Maikwai Dukke Supervisory Councilor Health Department Funtua Local Government Council Da Lambobin Girmamawa bisa kyakkyawan Jagoranci da Cigaban karamar Hukumar Funtua.

Kungiyar Dukke Consultative Forum (DCF) ta karrama Mai Girma Hon. Abdulmutallab Jibrin Sulaiman Goya, Shugaban Karamar Hukumar Funtua, da kuma Hon. Bara’u Yusuf Maikwai, Supervisory Councilor mai kula da Sashen Lafiya na Karamar Hukumar Funtua, da Lambobin Yabo na Girmamawa.

Wannan karramawa ta zo ne bisa gagarumin ƙoƙari, jajircewa da sadaukarwar da suke yi wajen inganta ci gaban Karamar Hukumar Funtua, musamman a fannoni daban-daban na raya kasa, kula da jin daɗin al’umma, bunkasa harkokin lafiya da tallafa wa marasa ƙarfi a kowane lokaci.

Shugabancinsu ya kasance abin koyi, domin suna ci gaba da nuna nagartaccen jagoranci, gaskiya da kishin al’umma, tare da ɗaukar manufofi masu alfanu da ke ƙarfafa ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar Funtua baki ɗaya.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara musu hikima, lafiya da ƙarfin guiwa, Ya tsawaita musu rai cikin hidima, Ya albarkaci dukkan ayyukansu, tare da ba su ikon cigaba da jagorantar al’umma bisa adalci da gaskiya domin ci gaban Karamar Hukumar Funtua da ƙasa baki ɗaya.

Ubangiji Allah yasa Alkairee 🙏

Photos from Arewa Daily Updates's post 22/12/2025

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR MULKI TA FUNTUA,
HON. ABDULMUTALLAB JIBRIN GOYA YA SAKE SANYA WASU BAYIN ALLAH CIKIN FARIN CIKI.

Alhamdulillahi, a yau Litinin 22 ga Disamba, 2025, Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Funtua, Hon. Abdulmutallab Jibrin Goya, ya sake nuna jajircewarsa wajen tallafa wa al’umma, inda ya kai gagarumin tallafi ga al’ummar Unguwar Dahiru Dake karkashin Makera Ward.

Tallafin da aka bayar ya kunshi daukar nauyin magunguna, raba kayan abinci, bayar da kudaden cefane, tallafin kudin jari domin kananan sana’o’i, raba buhunan masara, tare da daukar dawainiyar karatun ‘ya’yan wasu daga cikin al’ummar yankin, tun daga matakin firamare har zuwa jami’a, a matsayin kyauta domin karfafa gwiwa da inganta rayuwar al’umma.

An tabbatar da wadannan ayyuka ne karkashin jagoranci da kulawar Ma’aikatan ASW (Auxiliary Social Workers) na Sashen Jin Kai (Social Welfare Funtua), tare da hadin gwiwar Hon. Alh. Bara'u Yusuf Maikwai Dukke, Supervisory Councilor Health Department na Karamar Hukumar Funtua, Alh. Lawal (P.A), Alh. Isiyaku Milloniya, ‘yan kwamitin Jam’iyyar APC na Unguwar Dahiru, da kuma ‘yan kwamitin Hon. Audu Goya na Makera Ward.

Al’ummar da s**a ci gajiyar wannan tallafi sun bayyana godiya da farin cikinsu, tare da yin addu’o’i ga Ubangiji Allah da Ya saka wa Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Funtua da mafificin alkhairi, Ya kara masa lafiya, tsari da kariya daga duk wani sharri ko zagon kasa, sannan Ya ba shi ikon ci gaba da fita kunyar al’ummar Karamar Hukumar Funtua baki daya.

Al'ummar da s**a ci gajiyar tallafin Sun hada da; Mallam Sani Danta-Aya ya samu jarin kuɗi ₦150,000. Mallam Shuaibu, Mustapha Amfani, Mallam Sani Makaho, Mallam Salisu Mai Gwanjo, Mallam Sa’idu, Mallam Hussaini Gurgu, Oga Rabe da Audu Gayu sun amfana da buhun masara, kuɗin cefane da kuma ɗaukar nauyin jinyarsu, yayin da aka ɗauki nauyin magunguna ko aikin jinya ga waɗanda ke fama da lalura.

Haka kuma, an tallafa wa mahaifiyar wata yarinya mai lalurar ƙwaƙwalwa da kuɗin sayen sabulu da buhun masara. Bugu da ƙari, an tabbatar da kulawa da makarantar ‘ya’yan Mallam Sani Makaho, Mallam Salisu Mai Gwanjo, mahaifiyar yarinya mai lalura da Mallam Sa’idu. Duk tallafin an bayar da su ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Karamar Hukumar Funtua, Hon. Abdulmutallab Jibrin Goya.

Want your business to be the top-listed Media Company in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Katsina