Muryar Arewa Reporters

Muryar Arewa Reporters

Share

Photos from Muryar Arewa Reporters's post 18/01/2026

Matar Bahaushe Ta Fi Kowace Mace Gata A nahiyarmu ta Africa Amma Ita Ce tafi Gasa Wa Namiji Aya A Hannu

Matar Malam Bahaushe tana da gata sosai sama da sauran matan kabilunmu, domin Malam Bahaushe bai yarda ya ga matarsa ta fita tana aikin karfi ko wahala ba.

Shi duk talaucin sa ya fi son matar sa ta zauna a gida shi ya fita ya yi aikin karfin ko wahalar domin ya nemo musu abin da za su ci shi da ita da yaransu.

Ada da wuya ka ga matar Malam Bahaushe tana zuwa Daukan ruwan da zasu sha koh nemo abin da zasu ci, ko daukar nauyin karatunta ko daukar nauyin gidanta da na yaranta koh da kuwa mai hali ce

Malam Bahaushe idan mai hali ne
hatta girki da wanki koh wanke-wanke ya haramtawa matarsa sai dai ya dauko masu yi mata hidima... Ita sai dai ta kwanta ta ci ta sha tayi ibada sai kuma kula da tarbiyyar yaransu kawai... Ko Unguwa za ta akwai direba idan ba mota a ba ta kudin keke napep.

Amma wallahi abin takaici da haushi sai kaji Malam Bahaushe kullum yana kuka da matarsa... Sam ba ta bashi had'in kai kullum cikin neman tashin hankali k**ar America
Da yawa daga cikin ire iren wadannan matsalolin ne kan sa wani namiji dake da hali karin aure ko Allah zai sa ya dace koh kuma yayi tunanin tsallakawa ya Auro wata kabilar ta daban wacce yake tunanin zai samu zaman lafiya da ita.

Wai kuwa matanmu na kasar hausa suna lura da yadda matan wasu kabilun ke fama da aikin karfi domin daukar nauyin mazansu da yaransu?
Ta dalilin aikin karfin da suke yi har jikinsu ya murde ya zama irin na maza

Kuma duk da haka suna girmama mazajensu duk da irin yadda suke gallaza musu kuwa?

Wasu matan kabilun fa su fita kiwon dabbobi ko yin itacen girki, wasu suyi aikin kafinta ko daukar bulo ko gini koh kankare wasu da ciki ko goyo suke wannan aikin kuma su samo kudin su dawo gida su girka abinci su ci su da mazajensu da yaransu... Ke kuma matar Malam Bahaushe mai ki ka sani game da irin wadannan aiyukan wahalar

Ni dai wallahi na kasa fahimtar me yake damun wasu daga cikin matan hausawa yak**ata ku chanza tunani

16/01/2026

16/01/2026

Manjo Donatus Okafor Wanda (a ramuwar gayya) sojojin Arewa s**a bunne shi da ransa

Manjo Donatus Okafor shi ne sojan da ya bai wa Tafawa Balewa giya nau'in burkutu da taba sigari, ya tilasta masa cewa sai ya kwankwada, ya ce masa idan ya sha za su kyale shi. Da sauran cin zarafi da s**a rika yi wa manyan Arewa a lokacin da s**a k**a su kafin su karkashe su, kisan wulakanci da tozartawa.

Tafawa Balewa yaki shan bukatun ya ki shan sigarin, yace addinin sa ya hana, kafin su kashe shi Tafawa Balewa yace: Inyamuri inyamuri kai da da mulkin Najeriya har abada da yardar Allah.

A matsayinsa na kwamandan rundunar da ke kula da tsaron Firayim Minista Abubakar Tafawa Balewa, Okafor saboda cin amana, ya yi amfani da saninsa da Firayim Minista don shirya dabarar yadda za a halaka shi.

An gano Okafor a matsayin daya daga cikin masu shirya makirci kashe Tafawa Balewa tare da su Manjo Emmanuel Ifeajuna da Kyaftin Ogbo Oji, waɗanda s**a fara shirin juyin mulkin tun daga watan Agusta na 1965.

A daren juyin mulkin, Okafor ya jagoranci sojoji zuwa gidan Birgediya Zakariya Maimalari, wanda daga ƙarshe s**a kashe shi. Duk da cewa bayanai sun bambanta game da hannun da ya ke da shi kai tsaye game da kisan Firayim Minista, wasu rahotanni sun ce shi da Ifeajuna sun sace Firayim Minista s**a harbe shi.

Bayan gazawar juyin mulkin da kuma kwace iko da Janar Aguiyi-Ironsi ya yi, an tsare Okafor a gidan yarin Abeokuta.

Mutuwar Manjo Donatus Okafor batayi kyau ba.

A lokacin juyin mulkin ramuwar gayya da aka yi a watan Yulin 1966, sojojin arewa sun kutsa cikin gidan yarin in da aka tsare Donatus Okafor don neman ɗaukar fansa kan mutuwar shugabannin arewa, in da s**a k**ashi s**ayi masa dukkan kawo wuka, s**a binne shi da ransa.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Kano