Ad One Zee Rk

Ad One Zee Rk

Share

05/03/2026

SHAWARA DA MATSAYA TA...

A yau din nan na gabatar da wata shawara ga ‘yan uwa da abokan arziki, inda na bayyana musu tunanina na dakatar da magana ko rubuce-rubuce kan harkar siyasa. Na yi hakan ne domin neman shawarwari da kuma jin ra’ayoyin mutane masu alheri, domin shawara hanya ce ta samun fahimta da kuma gujewa kuskure.

Alhamdulillah, sakonni da na samu sun kasance masu matuƙar armashi da karfafa zuciya. Wasu daga cikin ‘yan uwa sun tunatar da ni da tsoron Allah da taka tsantsan, suna roƙona da in cigaba da abin da nake yi amma cikin natsuwa da kula da iyakar kalmomi. Wasu kuma sun bayyana cewa suna ganin al’umma na amfana da sakonnin da nake wallafawa, musamman wajen wayar da kai kan zaben nagarta, domin a samu shugabanci nagari wanda zai taimaka wajen samun saukin rayuwa da adalci a wannan ƙasa tamu.

Hakika irin waɗannan sakonni sun sanya na sake yin tunani bisa wancan tunanin nawa na bawa. Domin idan abu yana da anfani ga al’umma, kuma ana yin sa cikin gaskiya da niyyar alheri, to ya kamata a yi kokarin ci gaba da shi cikin tsari da kiyaye sharia da doka.

Saboda haka, bayan nazari da shawarar da na samu daga gare ku nayi shawara ga wasu malaman addini, na yanke shawarar zan cigaba daga inda na tsaya. Kuma In sha Allah zan cigaba da bayyana gaskiya gwargwadon iko, tare da wayar da kai kan mutanen da s**a cancanci a zaba saboda nagarta, amana da kuma anfani da za su kawo wa al’umma.

Wannan shawarar da na ɗauke ta ne ba don na raina ra’ayoyin sauran ‘yan uwa ba ne. A’a, na yi hakan ne saboda wasu daga cikin shawarwarin da aka bani sun fi kusanci da addini, gaskiya, da kuma abin da zai anfani rayuwata a duniya da lahira. Iina miƙa godiya ta musamman ga dukkan ‘yan uwa da s**a dauki lokaci s**a bani shawara, s**a karfafa min gwiwa, s**a yi min fatan alheri. Hakika wannan alaka da goyon bayan da nake samu daga gare ku abu ne mai girma da nake matuƙar darajantawa.

Allah ya saka muku da alheri, ya haɗa zukatanmu kan gaskiya, ya kuma sa abin da muke yi ya zama sanadin alheri ga al’umma da ƙasar mu baki ɗaya.
Duk wanda yaji dadin wanan matsaya tawa ya daure ya rubuta GOMBE TA MALAM, IN SHA ALLAHU.

Prof. Isa Ali Pantami National Supporters Forum.
Abdussamad Tijani Sani...✍️

Want your public figure to be the top-listed Public Figure in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Kano