Alkalami

Alkalami

Share

15/06/2026

A Gaggauce: Kotu ta umarci INEC ta soke rajistar ADC, Accord da wasu jam’iyyu uku

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, wato Independent National Electoral Commission (INEC), da ta soke rajistar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da wasu jam’iyyun siyasa huɗu.

Sauran jam’iyyun da kotun ta ce a soke rajistarsu sun haɗa da Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP) da Zenith Labour Party (ZLP).

Wannan umarni ya biyo bayan hukuncin da Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke.

Ƙungiyar Tsoffin ’Yan Majalisu ta Ƙasa ta shigar da ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/2637/2026, inda ta roƙi kotu ta tantance ko INEC tana da nauyin kundin tsarin mulki na cire rajistar jam’iyyun siyasa da s**a kasa cika sharuddan nasarar zaɓe da ke cikin Sashe na 225A na Kundin Tsarin Mulkin 1999 (wanda aka yi wa gyara), tare da tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2022 da ƙa’idojin INEC.

Masu ƙarar sun bayyana cewa waɗannan jam’iyyu biyar sun dade suna kasa cimma sharuddan da kundin tsarin mulki ya gindaya domin ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyyun siyasa masu rijista.

Sun ce sharuddan sun haɗa da samun aƙalla kashi 25% na ƙuri’u a wata jiha a zaɓen shugaban ƙasa ko kuma samun aƙalla kujera ɗaya ta zaɓe a matakin tarayya, jiha ko ƙaramar hukuma.

A cewarsu, ADC da sauran jam’iyyun huɗun sun yi rashin nasara a zaɓen 2023 da kuma zaɓukan cike gurbi da INEC ta gudanar, inda s**a kasa samun kujeru a muhimman matakan gwamnati.

Masu ƙarar sun dage cewa ci gaba da amincewa da waɗannan jam’iyyun a matsayin halattattun jam’iyyun siyasa ya saɓa wa doka kuma yana raunana ingancin tsarin zaɓen ƙasar.

Sun kuma roƙi kotu ta ayyana cewa wajibi ne INEC ta soke rajistar irin waɗannan jam’iyyu, tare da umartar ta yin hakan kafin shirye-shiryen zaɓen 2027 su yi nisa.

Bugu da ƙari, masu ƙarar sun nemi kotu ta hana waɗannan jam’iyyu biyar shiga zaɓe ko gudanar da harkokin siyasa kamar kamfe, gangami da zaɓen fidda gwani.

Haka kuma sun nemi a hana INEC ci gaba da hulɗa da ko amincewa da waɗannan jam’iyyu a hukumance har sai sun cika dukkan sharuddan kundin tsarin mulki.

Wannan hukunci na iya shafar damar wasu ’yan takarar jam’iyyun da abin ya shafa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wajen tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Kano
700251