Kabo Reporters

Kabo Reporters

Share

28/05/2026

Kwankwaso na shirin ayyana Aminu Abdussalam a matsayin ɗan takarar gwamna na NDC a Kano

Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa jagoran Ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin bayyana tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Comrade Aminu Abdussalam, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar Kano.

A tuna cewa Abdussalam ya yi murabus daga mukaminsa na mataimakin gwamna a watan Maris, makonni kaɗan bayan Majalisar Dokokin Jihar Kano ta aika masa da takardar tsige shi daga mukamin.

Majiyoyi sun shaida wa DAILY NIGERIAN cewa an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa ta sirri da aka gudanar a tsakanin jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da abokan siyasa na kusa da Kwankwaso.

Tun da fari dai tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Nasiru Yusuf Gawuna, na daga cikin waɗanda ake ganin su ne na gaba-gaba wajen samun tikitin takarar gwamnan.

Sai dai rahotanni sun ce daga ƙarshe Kwankwaso ya amince da Abdussalam a matsayin wanda zai baiwa takarar.

Rahotannin sun ƙara da cewa Kwankwaso ya yi wa Gawuna tayin kujerar mataimakin gwamna ko kuma tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, amma ana ganin Gawuna ya ƙi amincewa da tayin tare da jaddada biyayya da ci gaba da aiki domin nasarar jam’iyyar.

Majiyoyi sun ce Gawuna ya shaida wa Kwankwaso cewa ya shiga tafiyar Kwankwasiyya ne ba tare da wani sharadi ba, saboda haka rashin samun tikitin gwamna ba zai sa ya fice daga tafiyar ba.

An kuma rawaito cewa ƙin amincewar Gawuna da tayin ne ya jinkirta sanar da Aminu Abdussalam a hukumance, yayin da wasu masu ruwa da tsaki ke matsa lamba kan a sake duba cancantar Gawuna saboda ƙarfin siyasarsa.

Wasu daga cikin masu goyon bayan Gawuna sun bayyana cewa ya k**ata ɗan takarar da zai fafata da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito daga Kano ta Tsakiya, kasancewar yankin ne ke da mafi yawan ƙuri’u a jihar.

Sai dai masu goyon bayan Aminu Abdussalam suna ganin tsohon mataimakin gwamnan ya nuna cikakkiyar biyayya, jajircewa da sadaukarwa wajen bunƙasa tafiyar Kwankwasiyya.

Daily Nigerian Hausa

26/05/2026

Fubara ya janye takarar sa ne don biyayya ga yarjejeniyar da aka kulla a zaman sulhu - Wike

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa janyewar gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, daga takarar gwamna a 2027 ya yi daidai da yarjejeniyar sulhun da aka cimma domin dawo da zaman lafiya a jihar.

Wike ya bayyana haka ne bayan duba wasu ayyukan more rayuwa a Abuja, inda ya ce tun farko an cimma matsaya cewa za a dakatar da barazanar tsige Fubara, amma shi kuma ba zai nemi wa’adi na biyu ba.

Fubara dai ya janye daga zaben fidda gwani na jam’iyyar APC, yana mai cewa ya dauki matakin ne domin zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali a Rivers bayan tuntuba da iyalansa da magoya bayansa.

Wike ya ce bai yi mamakin matakin ba, yana mai zargin cewa daukar fom din takara tun farko ya saba da yarjejeniyar sulhun da aka cimma bayan rikicin siyasar jihar.

Haka kuma, ya bayyana ɗan majalisar tarayya, Kingsley Chinda, a matsayin wanda ya dace da kujerar gwamna saboda kwarewarsa a bangaren zartarwa da majalisa.

A gefe guda, kungiyar Rivers Professionals ta yaba da fitowar Chinda a matsayin dan takarar APC, tana mai cewa yana da kwarewa da nagartar da za su tabbatar da shugabanci mai adalci da hada kan al’umma a jihar Rivers.

Rikicin siyasar Rivers dai ya samo asali ne daga sabanin da ke tsakanin Wike da magajinsa Fubara kan iko da tsarin siyasar jihar tun bayan hawan Fubara mulki a shekarar 2023.

Daily Nigerian Hausa

21/05/2026

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya a rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin sauya sunan Najeriya zuwa “United States of Nigeria” tare da soke tsarin Shari’a a jihohin Arewa.

A wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar 21 ga Mayu, 2026, ya ce labarin ƙarya ne da wasu yan siyasa ke yaɗawa domin haddasa rikici da tayar da hankalin jama’a gabanin zaɓen 2027.

Sanarwar ta ce shugaban ƙasa ba shi da wani shiri na tura wata doka mai suna “Project True Federation” zuwa majalisar dokoki kafin babban zaɓe mai zuwa.

Fadar shugaban ƙasar ta kuma bayyana cewa sauya kundin tsarin mulkin ƙasa ba abu ne mai sauƙi ba, domin yana buƙatar amincewar kashi biyu bisa uku na majalisar tarayya da kuma amincewar majalisun jihohi 24.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban ƙasa Tinubu na mayar da hankali ne wajen aiwatar da gyaran tattalin arziki da samar da ci gaba ga yan Najeriya maimakon shiga batutuwan da za su raba kan al’umma.

19/05/2026

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta k**a tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman.

An k**a Mamman ne a yankin Rigasa da ke jihar Kaduna da safiyar Talata 19 ga watan Mayu, 2026 bayan makonni ana sa ido da tattara bayanan sirri a kansa daga jami’an hukumar.

Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya ce tsohon ministan ya ɓuya ne bayan Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifin karkatar da kuɗaɗen ayyukan lantarki.

Ya ce a ranar 7 ga Mayu, 2026, Mai shari’a James Omotosho ya same shi da laifi a kan tuhume-tuhume guda 12 da s**a shafi karkatar da kuɗaɗen ayyukan lantarki na Zungeru da Mambilla.

Olukoyede ya ce kotun ta yanke hukuncin ne ko da babu Mamman a gabanta bayan EFCC ta tabbatar da hujjojinta ba tare da wata shakka ba.

Radio

19/05/2026

Samun takarar mataimakin shugaban kasa da na yi a NDC zai buɗe kofar Kano ta samar da shugaban ƙasa nan gaba - Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa ya na da kwarin gwiwar samun tikitin takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar, ya na mai cewa hakan zai iya bude hanya ga jihar Kano ta samar da shugaban kasa a nan gaba.

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi kai tsaye da gidajen rediyo daban-daban a karshen mako a Kano.

Kwankwaso da Peter Obi, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, sun koma jam’iyyar NDC daga ADC a farkon wannan wata.

Rahotanni sun nuna cewa Obi da Kwankwaso sun amince su shiga NDC ne da sharadin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 a karkashin tikitin hadaka, inda ake sa ran tsohon gwamnan Anambran zai tsaya takarar shugaban kasa, yayin da tsohon ministan tsaro zai zama abokin takararsa.

Kwankwaso ya yi nuni da cewa idan aka zabi Peter Obi a matsayin shugaban kasa a 2027 kuma shi ya zama mataimakin shugaban kasa, hakan zai ba shi damar maye gurbin Obi a shekarar 2031.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address


Kano