Legal Friend Initiative

Legal Friend Initiative

Share

Legal Friend is established to cater for the need for guidance and assistance to the general public on their legal rights and responsibilities. Many people chose to live their lives in peace with their neighbourhood and sorroundings. Hence, they are able to take off their sights virtually from all negative advances by simply ignoring or forgiving any misgiving towards them. This leads to their rig

Scandal Rocks Jigawa Savings and Loans: MD Accused of Fraud, Nepotism, Abuse of Office 29/07/2025

https://www.dailystruggle.ng/2025/07/scandal-rocks-jigawa-savings-and-loans.html

Scandal Rocks Jigawa Savings and Loans: MD Accused of Fraud, Nepotism, Abuse of Office Jigawa State Governor, Malam Umar A. Namadi By Our Reporter The Noble Youth Mass Support Association (NYMSA) has called on the Jigawa Stat...

19/02/2024

SHARI'AR MURJA KUNYA DA ABINDA YA BIYO BAYA

Mutane na kuna son rudani, musamman a wannan fage namu na shari'a. Ga lauyoyin Gidan sun zama busy, ba lokacin da zasu fayyace muku komai.

A kullum mukan ce ya k**ata a fahimci matakan sharia kafin a fara sharhi.

Ita wannan baiwar Allah Murja Kunya, ai ba wani bakon abu ne ya faru ba. Shi Mallam Aminu Daurawa yayi aikin sa, ya k**a ya kai kotu. Allah Ya saka masa fa khairan.

Shi alkali yace a ajiye masa ita kafin ya kammala nazarin bada belin ta. Ba wai ya hukunta ta bane.

Ana haka sai wata bukatar bincike akan ita Murja Kunya ya taso. Su dama jami'an tsaro ai suna da dama a sharia su gayyaci mutum don suyi bincike a kansa. In bukatar hakan ta taso, sai suje kotun da ta tsare ta, a basu aron ta. To fa shine abinda ya faru. An bada aron ta ne don bincike. Khalas!

Tunda kotun tace gobe Talata zata zauna akan case din, to mu jira zuwa goben mana. In an ga bata zo kotu ba, to an samu abin magana kam. In tazo kuma shikenan, komai normal.

Amma ba bukatar zargin Mallam ko wasu jami'an gwamnati akan wannan dan karamin case din.

Allah Ya kaimu goben.

28/12/2023

ILMIN SHARI'A KAN TUHUMAR LAIFIN CAPITAL OFFENCE

Kun san me ake kira CAPITAL OFFENCE?
Shine laifin da idan aka tabbatar dashi akan wanda ake tuhuma, to za a zartar masa da hukuncin kisa ne ko daurin rai da rai.
To tuhumar kisan kai ta fado cikin Capital Offence.

TAMBAYA
Wace kotu ce take da hurumin yin shari'ar Capital Offence?
AMSA
High Court ko Upper Sharia Court.
Magistrate Court bata da hurumin taɓa Capital Offence.

TAMBAYA
To in haka ne, me yasa ake fara kai masu laifin Capital Offence Magistrate Court tunda basu da hurumi?
AMSA
Kundin tsarin mulkin Nijeriya ya haramta ajiye me laifi a wajen 'yan sanda sama da kwana 2.
To fa!
Sai ga shi an kawo me laifin Capital Offence wajen 'yan sanda. Wanda binciken case din ba zai kammalu a kwana 2 ba.
Meye abin yi?
A irin wannan yanayin, ana daukar wanda ake tuhuma din ne a kai shi Magistrate Court, amma ba don gabatar da shari'ar ba, sai dai kawai don a samu order da za a tsare shi a kurkuku kafin a gama bincike a gurfanar dashi a High Court ko Upper Shari'a Court.
Wannan shi ake kira HOLDEN CHARGE.

AMSA LAIFI
A tsarin shari'a, idan aka je kotu, sai wanda ake tuhuma ya amsa laifin sa, shikenan huta roro, waken gizo ya ƙi 'ya'ya. Sai ayi abinda ake cewa summary trial, a yanke masa hukunci nan take, babu bukatar kiran shaidu.

TAMBAYA
Haka abin yake a Capital Offence?
AMSA
A'a, ba haka bane.
A shari'ar Capital Offence, koda wanda ake tuhuma ya amsa laifin sa, to bisa ƙa'ida ta shari'a dole ne za a rubuta cewa 'ya musanta zargin da ake masa.' Ba a yin summary trial a Capital Offence. Dole ne sai an gabatar da hujjojin da zasu tabbatar da cewa yayi kisan. Na'am, amsa laifin sa yana iya zama shaida.
To haka ake a sharia. Idan kuka ji an ce mai laifi ya musanta zargin da ake masa, ba abinda yake zuwa zuciyar ku ne yake kasancewa ba. Wata ƙa'ida ce ta shari'a wadda dole sai an bi ta.

Mun gode.
Legal Friend Initiative.

18/03/2014

"Dan Sanda Abokin Kowa."

Shin ya wannan karin magana yake a yau a Nijeriya?
Shin 'yan sanda sun amsa sunansu 'abokan kowa?'
Shin 'yan sanda a yau suna kare hakkin al'umma ne, ko akasin haka?

Want your practice to be the top-listed Law Practice in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Hujjah Chambers. Zoo Road
Kano