Darul Islam
12/05/2019
Ramadan day 7
12/05/2019
Day 6
12/05/2019
Day 5
09/05/2019
Day 4
Mafi hankalin mutun shine wanda ya saki duniya tun kafin ta sake shi, kuma ya gyara kabarinsa tun kafin ya shiga cikinsa; kuma yaji tsoronAllah tun kafin ya hadu da shi; kuma yayi sallah a cikin jama'a tun kafin su sallace shi; Sannan kuma ya yi wa kansa hisabi tun kafin ayi masa, domin yau ranar aiki ce, ba hisabi, gobe kuwa Hisabi ne ba aiki ba. Allah Ya sa mu dace
Ina rokon Allah Ya saukar da Albarka, Alkhairi,Falala, Wadata, Ni'ima, Gafara, Rahama, Lafiya mai amfani, Kwanciyar Hankali Nutsuwar zuciya a garemu da Zuri'armu, da Musulmai Baki daya Ameen ya ALLAH. JUMAAT MUBARAK
ABIN LUR
DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA, KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA BAKWAI:
1. Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangininka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka.
2. Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka Zunubanka, ko kuma ya daukaka maka darajarka.
3. Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da Manzanni da Salihan bayin Allah wadanda s**a zo kafin ka.
4. Ka tuna cewa Tun kana cikin mahaifiyarka kafin ta haifeka an riga an rubuta maka duk abinda zaka samu aduniya, da kuma dukkan abinda zai sameka. Mai dadi ko Kishiyarsa.
5. Ka tuna cewar rungumar Qaddara kowacce iri, yana daga cikin Ginshikan Imaninka. Gwargwadon yadda kake rungumar Qaddara, gwargwadon haka imaninka yake.
6. Ka tuna cewar kowanne tsanani yana tare da sauki guda biyu. (Ga lada, ga kuma yayewar tsananin).
7. Ka tuna cewar Allah shine ARHAMANUR RAHIMEEN (MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYI) kuma yafi komai kusa dakai, Kuma yafi kowa tausayinka. Kuma zai amsa dukkan rokonka.
Ya Allah ka yaye mana dukkan Tsanani don hasken Alqur'aninka, don Rahamar nan taka wacce ta yalwace dukkan halittunka amin
( Barkammu da war haka)
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kofar Gadon Kaya Masjid Mal. Jaafar Mahmud Adam Gwale Local Govt
Kano
700241