Samaha SMCS

Samaha SMCS

Share

14/04/2024

Mu Koma Gona

MATASA DA AGRICULTURE

Abdullahi Abubakar Lamido

Da sunan Rabbi wanda ya kagi nature
Ya aiko Annabawa da scripture
Ya baiwa duniya best architecture
A yau zan wake harkar agriculture

Cikin Enghausa ne zan tsara baiti
Gama Enghausa yaren na da beauty
Ana yi yau cikin kauye da city
Da Hausa da Ingilishi anka mixture

A yau a Arewa ko ta ina talauci
Da kidnapping da tsabar cin mutunci
A kullum rayuwarmu cikin takaici
Gaba daya al’umar sam babu future

Kudanci dogaronsu yana ga fetur
Arewa ko ga kasar nomarmu lebur
Mu dau noma mu daina batu na fetur
The new oil fa shi ne agriculture

A noma mun tsaya kyam a production
Gaba daya ba batun value addition
Muna noma kwai bisa wrong assumption
Cikin nomarmu dole mu canza culture

Matashi dan Musulmi za ka ganshi
Yana nan zaune ba aiki gabanshi
Kawai sai tsabaragen Ingilishi
Zugum ka ganshi ba Magana ta future

Matashi lafiyayye ga shi jobless
Ka gan shi kawai cikin komensa hopeless
Rashin aikinsa ya maisai speechless
Talaucin rayuwa ya ba shi torture

Matasa yanzu dole ku kara himma
Ku dau ilimi da kiwo ku riki noma
Ku bamu hatsi da shinkafa da nama
Cikin noma Arewa ta ke da future

Cikin noma ake samun abinci
Da shine ma ake korar talauci
A samu kudi a samu dadin mutunci
A kan haka sai mu rungumi agriculture

Da shi aka wa talauci alleviation
Da shi aka ba wa yara nutrition
Da shi ne maganin duka inflation
Na duke yana da big nomenclature

Cikin noma matasa na da aiki
Akwai access to 'ya'yan nan na banki
Akwai damammaki ninkin ba ninki
Idan kuka bar shi kun ga akwai fracture

Cikin noma da tarun employment
Akwai damammaki fiye ma da government
Idan burinmu shi ne fa development
Dukanmu kawai mu koma agriculture

Matasa dole ne mu yi calculation
Mu wa juna fada mu yi motivation
Mu dau noma da kiwo da education
Da su ne za mu zam mun samu future

Idan dai har muna son yin mutunci
Idan niyyarmu magance talauci
Da motsi don mu ba wa kanmu 'yanci
Ashe to wajibi ne canza culture

Zaman banza da shirme yanzu dole
Da wasanni da chatting duk mu kyale
Idan kuma mun ki ma sha gwale-gwale
Talauci zai zamo a gare mu nature

Today mun kwashi lakcar Dakta Tilde
Ta allura a kan aiki a ladde
Idan muka dau nasihun nan na Tilde
Fa tilas ne mu zam mun canza culture

Idan burinka shi ne employment
Idan ka so ka tashi ka fara movement
Idan da ba bu mai maka encouragement
A yau dai ga shi nan an baka lecture

Bayanai ga su an maka su laziza
Tunani yanzu na san za ya canza
Ka dage don ka ba wa kanka izza
From now sai ka koma agriculture

Amir Lamido nan ne za ni huta
Ina fata ilahu ya ban fahimta
Ya kara min tsayawa kan bajinta
Ya sa ni cikin wadanda suke da future

Amir Lamido
11/10/21

Amir

Want your business to be the top-listed Business in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Kano
00234