Al-afaf Media
Ya'juj da Ma'juj (يَأْجُوجُ وَمَأْجُوجُ) Malama Zainab Ja’afar Mahmud
Ranar Addu’a
26/05/2026
RANAR ARFA RANAR ADDU'A
A yau rana ce mai girma, ranar da ake yawaita addu’a, istigfari da neman gafarar Allah.
Ranar da Allah yake ‘yanta bayinSa daga wuta fiye da kowace rana.
Ka ɗaga hannuwanka cikin tawali’u, domin Rahamar Allah tana kusa da masu roƙo
26/05/2026
RANAR ARFA RANAR ADDU'A
-Ranar da Allah Ya cika addini da ni'imarShi ga bayi.
-Ranar farin ciki ga mahajjata.
-Ranar da azumtar ta yake kankare zunuban shekara biyu.
-Ranar samun gafarar Allah daga zunubai.
-Ranar da Allah ke alfahari da bayinSA da ke filin arfa.
-Ranar da Allah Ya fi 'yanta bayinSA daga wuta a cikinta.
-Ranar da addu'a a cikinta take kasancewa mafi alkhairin addu'a.
ABIN LURA:
LAILATUL ƘADRI an sakaya gane ta, amma RANAR ARFA a bayyane ta ke.
LAILATUL ƘADRI Mala'iku ne ke sakkowa saman duniya, yayin da RANAR ARFA Allah Mai tsarki da ɗaukaka da kanSHI yake sakkowa saman duniya.
Rana ce ta bijirar da buƙatu a ƙofar Allah, burace-burace, damuwoyi, rashin lafiya, neman nasara, kai duk wata buƙata da bawa yake da ita yau ga ranar roƙo da bara a fadar Allah, kar mu yiwa kawunanmu rowa 'Yan uwa!!!
Mu yiwa kanmu da 'Yan'uwanmu addu'o'i na alkhairi. Allah Ya datar da mu baki-daya amin.
✍🏽Zainab Ja'afar Mahmud
8th Zhul-hijjah 1443A.H
7th July 2022
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
1987