Umar Sobeka

Umar Sobeka

Share

Photos from Umar Sobeka's post 27/04/2023

Sarki Leopold || Makashin Baƙaƙen Fata Ƴan Afirka Miliyan Goma...

"Ku sare kawunan mazajen, ku rataye su a cikin kauyuka, ku yi jima'i da matan gida, ku rataye yara da mata a kan giciye."

-Inji Sarki Leopold ||

Sarki Leopold II na Belgium ga hafsan hafsoshinsa, yana nufin mutanen da ya yi wa mulkin mallaka a Kongo.

Ga hoton wani yaro nan da Ƴan Mishan turawan mulkin Mallaka s**a Guntulewa hannu a zaluncin da s**a dinga tafkawa a ƙasar ta congo ƙarƙashin jagorancin Matsiyaci Sarkin Belgium na wancan loƴaci Leopold ||.. Shekarar " 1890-1910 " Shekara ɗari da sha biyu..

Mai martaba Sarki Leopold II.

Bayani:

Ƙasar Kongo ƙasa ce a Afirka ta Tsakiya Wadda ƙasar "Belgium" ta ƙwata da ƙarfin soja zamanin Sarki Sarki Leopold II Belgium wanda taron Berlin na 1885 ya kafa kuma ya amince da shi. A cikin shekaru 23 (1885-1908)
Leopold II ya mulki Kongo, ya kashe 'yan Afirka miliyan 10 ta hanyar Yanke hannaye da al’aura, da yi musu bulala har lahira, yunwa ta kashe su da aikin tilastawa, Ƙwacen yara da karɓar kudin fansa da kona Ƙauyuka. Wani abin ban mamaki na wannan labari shi ne cewa Leopold na biyu ya aikata wadannan ta'asa Batare da ko da taka kafarsa a ƙasar Kongon ba. A karkashin gwamnatin Leopold II.

Hoton dake Ƙasa na wani Mutumine da ke Kallon yadda aka yanke ƙafar ƴarsa , Saboda bai Yi aiki tuƙuru ba a kamfanin da yake aiki mallakin turawan mulkin mallaka na belgium Mai suna "ABIR Company" Cikakken Sunan kamfanin shine ( the Anglo-Belgian India Rubber Company daga baya aka canjawa kamfanin suna zuwa Compagnie du Congo Belge) ..

K**ar Yadda Shahararriyar Marubuciyar nan "Alice Seeley" Ƴar Ƙasar Amurka mazauniyar birnin Los Angeles " ta Rubuta a Littafinta Mai suna "Don’t Call Me Lady: The Journey of Lady Alice Seeley Harris:"

"Sun Yankewa ƴar Ma'aikacin Hannu Sunan Yarinyar Boali daga baya kuma matarsa sannan s**a yankewa matar tasa al'aura daga baya ta Mutu... inji baturiya "Alice Seeley wadda ta kai ziyarar gani da ido a wancan loƙacin da abubuwan suke faruwa".

Wani limamin Katolika Mai suna "Tswambe" Ya faɗa cewa Shugaban Sojojin Sarki "Leopard || Mai Suna
" Léon Fiévez" Ya bawa Sojojin nasa Umarni Cewa "

"Duk gawarwakin da aka Kashe dole ne ku datse hannayensu.. Yana so ya ga adadin hannayen da kowane soja ya yanke, ya kawo su cikin kwanduna...Kauyen da ya ƙi ba da roba da Cocoa za a share shi gaba daya daga doron Ƙasa...

27/04/2023

Kafin Kayi aure a wannan loƙaci Ya k**ata kasan da wannan ..

Kwanon Shinkafa ƴar Hausa Naira 1800 Ne Gwangwani Man gyaɗa 250 Maggi ɗaya Naira 10 Biredi Wanda Mutum biyu zasu iya Ci Naira 250 Taliya 450 ..

Sabulun Wanka 200 Na Wanki 200 Kuɗin Ruwa Jarka ɗaya naira 50 a ƙalla ka sayi jarka biyu kullum naira ɗari..

Sai Ka Buga a sati ɗaya Kai da amarya da ƴan ƙannen amarya masu kawo ziyara zaku iya lashe Kwano Huɗu na shinkafa Kuɗinta Zai K**a naira 1850 ×4 Zai k**a Naira 7400..

Biredi 250 a ƙalla ku siya sau biyar a sati Kuɗinka Zai K**a 1250..

Taliya a ƙalla ka sayi Guda Uku a satinnan kuɗinka zai k**a 1350..

Kuɗin Ruwan sha na wanki dana wanka a ƙalla jarka biyu a rana naira ɗari sau 7 ya k**a ɗari bakwai a sati..

Sabulun wanka da na wanki ,Maggi , Kayan Miya, Gas ko gawayi , Man girki Kuɗinsu zai K**a Naira 6000 A sati..

Shinkafar Sati Ɗaya - 7400
Biredi na Sati Ɗaya- 1250
Taliyar Sati Ɗaya-1350
Kuɗin Ruwa-700
Su kayan miya da sabulun wanka da wanki, gawayi ko Gas , Man girki -6000

Total ɗin Sati ɗaya duka- 16,700
Total ɗin wata ɗaya-66,800

Wannan lissafi kada ka manta ba'a saka wasu abubuwa ba da yawa k**ar kuɗin magani na rashin lafiya, kuɗin kayan kwalliya, auduga ta mata yayin Al'ada, Kuɗin taransifot na zuwa wajen aiki ko kasuwa na maigida, Ƴar madara ta watsawa a shayi, ɗan naman miya, gasu nan dai birjik..

Shi yasa Muke gayawa samari da babbar Murya idan baka samun a ƙalla dubu hamsin a wata ka haƙura da aure kaga dai lissafin dubu sittin ma tayi kaɗan, wannan kuma shine ƙarshen lissafi wanda ba kowacce mace ce zata iya yadda ta zauna a haka ba...

Nayi Nan 🚶🚶

Adam Husaini Abubakar

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Northwest
Kano