Taskar Alheri Media

Taskar Alheri Media

Share

Muna tare da ku daga Abuja har zuwa Sakkwato.

Photos from Taskar Alheri Media's post 05/05/2026

YANZU YANZU: An Rantsar da Murtala Sule Garo a Matsayin Mataimakin Gwamnan Jahar Kano

An rantsar da Murtala Sule Garo ne yayin wani ƙwarya-ƙwaryan biki a gidan gwamnatin jihar a ranar Talata 05/05/26, inda sabon mataimakin gwamnan ya ce zai yi aiki tuƙuru don ciyar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf gaba dama Jahar Baki Daya.

Naɗin Garo na zuwa ne bayan murabus ɗin da Comrade Aminu Abdussalam ya yi a watan Maris.

Photos from Taskar Alheri Media's post 04/05/2026

Gwamnan Jihar kano abba kabir yusuf zai Rantsar da mataimakinsa Wato Murtala sule Garo a gobe talata 04/05/26

Hakan na dauke ne cikin wata Sanarwa da mai bawa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, ya fada

Sanarwar ta ce za'a gudanar da bikin rantsuwar ne da karfe 11 na safe a zauren Coronation Hall da ke gidan gwamnatin Kano.

01/05/2026

Gwamnan Kano abba Kabir yusuf yayi alkawarin biyan bashin duka ragowa kudin da yan fansho suke bi kafin wa’adinsa na farko ya kare

Gwamna Abba Kabir Yusif ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi a wajen bikin ranar ma’aikata ta duniya, wanda aka gudanar a filin wasa dake kofar mata.

Gwamna Yusif ya ce gwamnatin sa ta gaji bashin kudin ‘yan fansho da yawan su ya kai naira biliyan 48 daga tsofaffin gwamnatocin da s**a gabaci ta shi, sai dai kawo yanzu ya biya kimanin naira biliyan 32, inda ya rage saura biliyan 16.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Zoo Road, Kumbotso LGA
Kano
700101