Labarai A Yau

Labarai A Yau

Share

Manoma TV Tasha ce da aka samar domin kawo muku sahihan Labarai na Noma da Kiwo da kuma koyar da dabarun Noma na zamani tareda wayar da kan Manoma akan Sauyin Yanayi da sauransu.

24/01/2026

RASHIN INGANTACCEN IRIN SHUKA NA RAGE YAWAN AMFANIN GONA A NAJERIYA - MASANI

Harkar noma a Najeriya na ci gaba da fuskantar koma baya sakamakon yadda manoma da dama ke shuka irin shuka marasa dacewa, saboda rashin samun sahihin bayani, inji wani kwararre a fannin noma.

Daraktan Gudanarwa na Gidauniyar Foundation for Sustainable Smallholders Solutions (FSSS), Isaiah Gabriel, ya ce ci gaba da amfani da irin shuka marasa dacewa na daga cikin manyan matsalolin da ke shafar samar da abinci a ƙasar nan, duk da cewa ana yawan yin watsi da batun.

Gabriel ya bayyana cewa manoman kananan gonaki da dama ba tare da sani ba suna shuka irin da bai dace da nau’in ƙasarsu, yanayin ruwan sama, ko kuma halin sauyin yanayi da ke yankunansu, lamarin da ke haddasa ƙarancin amfanin gona, lalacewar shuka, da asarar kuɗi.

“Manoma da dama a Najeriya har yanzu suna dogaro da tsofaffin irin shuka ko kuma irin da bai dace da yankunansu na noma ba. Hakan ya samo asali ne daga raunin ayyukan jami’an wayar da kan manoma da kuma ƙarancin samun ingantaccen bayani na noma,” in ji shi.

A cewarsa, matsalar ta fi tsananta a tsakanin kananan manoma da su ne ginshiƙin tsarin samar da abinci a Najeriya, amma ba su da isassun damar samun sahihan irin shuka ko shawarwarin kwararru. Ya ƙara da cewa sauyin yanayi ya ƙara tsananta matsalar, domin canjin yanayin ruwan sama da hauhawar zafin rana na buƙatar irin shuka masu jure yanayi.

24/01/2026

The statement quoted the Director-General of the Kebbi State Investment Promotion Agency, Dr. Muhammad Kabir Kamba, as saying that foreign investors from Europe and Asia have already indicated interest in attending the festival, following Governor Idris’ recent overseas engagements.

“We are expecting a large turnout of investors who are keen to explore the state’s abundant natural resources and forge partnerships with the government and people of Kebbi State,” Dr. Kamba said.

Read full story in the comment section!!!

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Zoo Road
Kano
700222