MATAN Sunnah

MATAN Sunnah

Share

16/01/2019

https://youtu.be/SQbD4H8wm0c

Me ake nema a wajan mace in Islam Sheikh Ahmad Tijjani Gurumtum

04/12/2018

MATAN SUNNAH.
abin mamaki ya tabbata ga macen datake suturta jikinta saboda tsoron sanyi, amma bata suturta jikinta saboda ALLAH.
For more visit

chat.whatsapp.com

Dake AKe Consultancy 26/04/2018

DAKE AKE GLOBAL CONSULTANCY

Sunan shirin: BAYAN DUHU

DAGA TASKAR: Hadiza Balanti chediyar yan gurasa

SHIMFIDA:
Dukkan Godiya da yabo da kirari da jinjina da bambadanci da roko tare da daga hannu sama sun kebantu ga Allah madaukakin sarki, sarki Allah mahalicci, mahakurci, makadaici, mawadaci, majibinci, mabuwayi, mai Rahma mai jin kai, wanda bai haifa ba kuma ba’a haifeshi ba, sannan babu wani abin halitta da ya zama kini ko tamka a gareshi.

Tsira daraja da aminci su kara tabbata ga masoyin mu mai ceton mu Annabi dan gatan Allah cikamakin Annabawan Allah da Manzonni, manzo Sallallahu alaihi wa sallama, tare da alayensa da dukkanin sahabbansa da salihan bayi masu bin tsarin koyarwarsu sau da kafa cikin kyautatawa har izuwa ranar karshe.

Yan uwana masu albarka muna karanta muku gaisuwa ta kauna da addu’a tare da fatan alkhairi a gareku, da farkon fara haduwarmu daku a yau, a wannan sabon shiri mai albarka na BAYAN DUHU

“Allah ka taimakemu akan duk abinda zamu zaiyano ya zama daidai ga mai karatu kuma ya amfanar dasu, musamman yan uwana mata.

Allah muna rokonka kar ka jarabcemu da abinda ba zamu iya ba, kuma Allah abinda muka sani kar ka sa ya zama musiba a garemu Amin”.

Allah Subahanahu wa ta’ala ya halicci mace a matsayin jinsi mai zaman kansa, mai dauke da martabobi bila-adadin, darajarta tana misaltuwa ne a matsayin sutura wadda ta zama wajibi a kula da ita kasancewarta ginshikin rayuwa kuma gishirin al’umma, mace alkibla ce mai zaman kanta dangane da koyarwar addinin musulunci.
____________________________
IN DAI ANA BIYE DAMU CIKIN NUTSUWA DA FAHIMTA, ABINDA YAFI WANNAN BAYANI YANA NAN TAFE A MAKON GOBE, IN SHA ALLAH, DA FATAN ZA'A YI MANA ADDU'A.
____________________________
Zaku iya kasancewa tare damu da dukkan aikace-aikacenmu, ko tuntubarmu ko aiko da shawarwari da tambayoyi, ta wadannan hanyoyin dake kasa;

https://www.dakeake.com

https://www.twitter.com/dakeake

https://www.instagram.com/dakeake

https://m.facebook.com/dakeakeglobal

htt

Dake AKe Consultancy We make a woman feel like a real woman

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Kano