Albarkatv
24/10/2025
MAI HASKE NE A CIKIN DUNIYAR ALHERI
Na rayu da mutane iri daban-daban tun daga yarinta zuwa girma na— na hadu da masu hali iri-iri: masu kirki, masu tausayi, da masu son kai. Amma gaskiya, ban taɓa ganin irin Abdul Amart Maikwashewa ba.
Mutum ne da zuciyarsa ta ginu a kan adalci, halacci, taimako, da kyakkyawar niyya.
A hulɗarsa da mutane, gaskiya da adalci su ne ginshiƙansa.
Yana kallon kowa da idon mutunci, yana yanke hukunci bisa gaskiya, ba tare da son rai ba.
A rayuwarsa, kirki, kyauta, da taimako sun zama al’ada.
Yana haɗa zumunci, yana gina abokantaka, kuma yana yafe wa waɗanda s**a saɓa masa domin zuciyarsa ta fahimci cewa yafiya tana kawo natsuwa.
Tausayin na ƙasa da shi ya zama abin alfahari.
A dalilinsa, wasu sun samu muhalli, wasu sun samu abin hawa, wasu sun yi aure da kwanciyar hankali.
Akwai kuma waɗanda Allah Ya basu waraka daga rashin lafiya ta dalilin taimakon sa.
Iyalai da dama da s**a rasa mafaka, yau suna cikin farin ciki da murmushi saboda kulawarsa da gudunmawarsa.
Allah Madaukaki ya yi bushara da irin waɗannan mutane a cikin Al-Kur’ani mai girma, inda Ya ce:
> “Wa man ya‘mal mithqāla dharratin khayran yarah.”
(“Duk wanda ya aikata koda ƙwayar zarra ta alheri, to zai gan ta.”)
— Suratul Zalzala: 7
Haka kuma Allah Ya ce:
“Inna alladhīna āmanū wa ‘amilus-sālihāti innā lā nuḍī‘u ajra man aḥsana ‘amala.”
(“Lalle waɗanda s**a yi imani s**a aikata ayyukan ƙwarai, ba za Mu ɓata lada ga wanda ya aikata alheri ba.”)
— Suratul Kahf: 30
Wannan shi ne Abdul Amart Maikwashewa — mutum mai imani, tausayi, hangen nesa, da adalci.
Halinsa ya zama darasi ga matasa, abin koyi ga shugabanni, kuma haske ga al’umma baki ɗaya.
A gaskiya, tsohon abokina ne, amma saboda irin kyawawan halayensa, tausayi, da kulawa da yake nuna wa mutane — yanzu ya zama ɗan uwa a zuciyata.
Allah Ya ƙara maka lafiya, natsuwa, da albarka a dukkan al’amuranka.
Allah Ya saka maka da alkhairi a duniya da lahira.
Barka da Juma’a — Allah Ya amshi ibadunmu, Ya sanya mu cikin waɗanda ake yi musu rahama a yau.
30/08/2025
🚀 Jastaheer Data Website & Lite App Are Now Live! 🎉
👉 Sign up today and enjoy:
✅ Cheap Data & Airtime
✅ Utility Bills (Electricity, TV, Exam Pins & More)
✅ Referral Bonuses 💰
✅ Secure Wallet System 🔐
🔗 Join here:
👉 https://www.jastaheerinformationtechnology.com/jastaheerdata/signup/?ref=jabirstahir
Be among the first to enjoy fast, secure, and reliable services. 💡🔥
08/06/2025
Ya Allah Mai rahama, Mai jin ƙai, Mai iko akan komai…
Muna roƙonka da sunanka Mai girma da siffofinka masu daraja, ka albarkaci Jagora ka yawaita masa ni’ima a cikin rayuwarsa, ka tsare shi daga dukkan sharri da fitintinu, ka cika zuciyarsa da hikima, fahimta, da haske a dukkan al’amuransa.
Ka sanya albarka a cikin ayyukansa da burinsa, ka cigaba da ba shi damar zama jagora mai tsayawa akan gaskiya da adalci, wanda yake amfanar da jama’a da al’umma gaba ɗaya.
Ya Allah, muna roƙonka da rahamarka, ka gafarta wa iyayensa marigayi, ka sanya su cikin rahamarka mara adadi, ka sanya kabarinsu ya zama dausayin Aljanna. Ka gafarta musu kurakuransu, ka daukaka darajarsu a cikin Aljannar Fiddausi.
Ka albarkaci ’yayansa da ‘yan uwansa, ka sanya su su zama madogararsa da farin cikinsa. Ka ba su tarbiyyar da ta dace, ka tsare su daga sharrin zamani, ka buɗe musu kofofin alheri da arziki, ka sanya su cikin bayinka na ƙwarai.
Ya Allah, ka cika zuciyar Jagora Abdul Amart da haƙuri da ƙwarin gwiwa bisa rashin iyayensa, ka saka musu da alheri bisa irin kulawa da tarbiyyar da s**a bashi kafin rasuwarsu.
Allahumma, ka ba shi nisan kwana cikin lafiya da ɗaukaka, ka sanya masa nasara a cikin duniya da lahira.
Barka Da Sallah Jagora 01
15/04/2025
Jagoran Futa Kunya!
, jagora mai jan matasa a jiki, yana ƙarfafa su wajen dogaro da kai da neman halak cikin gaskiya da rikon amana.
Jiya da kan sa ya jagoranci al'ummar sa tattaki daga Kano zuwa Katsina domin bude Dageji Media, kamfanin ɗaya daga cikin matasan da yake massa Aiki. Wannan ba ƙaramin abin alfahari bane—samun jagora kamar Abdul Amart wata baiwa ce da dole mu gode wa Allah.
Muna roƙon Ubangiji ya ƙara masa ƙarfin guiwa da nasara a dukkan al’amuransa.
Yanzu haka Dageji Media ya fara aiki!
Ku garzaya zuwa Kofar Kaura Underground, Maikudi Abdullahi's House, Katsina State domin cin moriyar Aiki na zamani.
02/01/2025
Kada ka tilasta wa mutane son ka, Allah ya riga ya so ka fiye da ajizancinka.
02/01/2025
“Lokacin da kuka cutar da mutane masu zuciyar kirki, ba za su yi kururuwa ba, za su ci gaba da jin zafi a ciki. Za su yi shuru a hankali ba za su dawo ba. Ba za su daina zama nagari ba, ba za su ƙara amincewa da kai ba. Wannan shi ne daidai lokacin da kuka rasa su. " ✨
25/11/2024
In the name of Allah, the Most Gracious, the Most Merciful, we begin this new film project with humility and hope. We seek Your guidance, O Allah, in every step we take, and ask for Your blessings upon this endeavor. Grant us creativity, wisdom, and unity among the team. May this project be a source of success, inspiration, and positive impact. Protect us from challenges beyond our ability and make this journey smooth and fruitful. Ameen.
23/11/2024
Allah Duk Wanda yayi Sanadin Farin Cikin mu.
Allah ya Dauwamar Da farin Ciki a cikin Zuri'ar sa. Allah ya baka Aljannah maɗaukakiya
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano