Muhammad salisu daneji

Muhammad salisu daneji

Share

12/12/2019

KISHIYA A KASAR HAUSA, wata musulma ce tayi kawance da wata Kirista a social media har takai suna ziyartar Juna, ran nan sai wannan musulmar take shawartar kawarta da ta amshi musulunci sai kawar tace ta yarda amman da sharadi idan har zata amince mata ta auri mijinta saboda yana da kamun kai, ga kudi, ga kyau ga ilmi ga.... Sai musulmar tace ke wasa fa nake maki ai damu da ku duk lalube ake kawai kirike naki yama fi dacewa dake.

14/07/2019

Mahawara)
Kaine kana Tafiya,Sai ka tsinci Makudan kudade acikin jaka
kimanin Naira Milyan Ashirin (20,000000)
Sai aka gane suna wajenka,
Akayi akayi ka mayar Kaqi.
Sai aka Yankema hukuncin shekara Goma a magarkama.
Bayan ka yi shekara tara da Wata sha Daya kenan saura
wata daya ka kafita daga Magarkama,
Sai mamanka ta gane inda ka 6oye kudadennan.
Kawai sai Ta sankamesu ta baiwa Hukuma tace:
Ga kudadenku Ku sakarmun Yaro na
Wai idan kaine ya Zakayi????

27/06/2019

Da da uba
Wani Bazazzage ne ya kira dansa da yake karatu a jami’a. Ga yadda hirarsu ta kasance:
Baba: Musa, kana
ina ne yanzu haka?
Yaro: Baba, ina dakin makaranta a kwance.
Baba: Madalla! Na ji ana cewa dalibai suna ta
zanga-zanga da kone-kone a makarantarku, to wallahi kar ka kuskura ka bi su ka san dai irin tarbiyyar gidanku.
Yaro: Idan Allah Ya yarda ba zan bisu ba baba.”
Baba: Yauwa dan arziki sai an jima.
Bayan minti 15, ya sake kiran yaron ya ce da shi: “Wai mene ne dalilin yin wannan zanga-zangar?
Yaro: Wai saboda hukumar makaranta ta kara mana kudin
makaranta daga Naira dubu 30 zuwa Naira dubu 300.
Baba: Iye! Yanzu kai kana
ina?
Yaro: Ina kwance a daki.
Baba: Ashe kai mahaukaci ne? Tashi ka bi su!

25/06/2019

'NIGERIA SAI A HANKALI
Anyi hatsari a wani t**i. Mutane 5 s**a jikkata, mutane 6 s**a mutu. Sai Ministan lafiya yayi
alkawarin naira dubu biyar ga duk wanda ya jikkata. Naira miliyan 6 ga duk wanda ya rasa ransa. Da jin haka sai daya daga cikin wadanda s**a jikkata yayi zunbur ya tashi ya kwanta cikin matattu. Sai daya daga cikin matattun ya ce
Mallam karka kawo mana rudu, an rigada an'irgamu. Ka tashi ka koma cikin wadancan.

24/06/2019

GODIYAR ANGO.

Wani ango ne ana walimar bikinsa a gaban ’yan uwa da abokan arziki, bayan an kammala sai aka ce ya tashi ya yi jawabin godiya. ANGO: Godiya ga Malam Hashimu dillalin gidaje, wanda ya ba mu aron gidan da za mu zauna kafin mu samu na haya. Ba zana taba mantawa da Hajiya Tasallah Mai Adashi ba, wadda ta ba ni daukar farko don in kai kudin auren. Godiya ga Asabe Dillaliya, wadda ta ba mu bashin atamfofi da shaddodi da muka saka a lefe. Allah Ya saka wa kanwata Basariyya, da taimakonta ne na fita kunya, inda ta ba mu aron akwatunan lefenta muka saka kayan a ciki, bisa yarjejeniyar mayarwa bayan an gama biki da mako 2. Allah Ya bar zumunci, Ya ba mu ikon cika alkwurran da muka dauka. Ba zan manta Atiku Mai Wanki Da Guga ba, da ya ba ni aron kaya domin in saka a wannan rana. Mun gode.

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Ja'en Sharada Phase III
Kano