KOGON GANO
29/06/2026
Da yawan gidajen jaridu ba gaskiya s**a rubuta ba a kan zaman kotu da aka yi yau. Sahihin zance shi ne, kotu ta bada umarnin a kai mata littafai 58 da aka yi amfani dasu aka yankewa Malam Abduljabbar hukunci a kotun kofar kudu don ta nazarce su. Wannan shi ne gaskiyar abunda ya faru. Duk abunda yake sabanin wannan ku watsar dashi.
Daga: Muhammad Galadanci
27/06/2026
Har Da Shehu Ahmad Tijjani (R) Cikin Masu Tsine Wa Makasan Jikokin Manzon Allah !!!
Saifullahi Murtala Jibia
Ina mai ba ku haƙuri 'yan uwana tijjanawa 🙏
Tayaya, wanda ya karanta wannan, ba zai ɗauki Batijjanen dake cewa, wai Malam Abduljabbar (H) Ɗanshi'a ne, kawai saboda wulayar sa , ga Ahalingidan Manzon Allah (saww) a matsayin MAHAUKACI KO SAKARAI BA ?
TO MENE NE SHI'ANCIN ???
Ƙaunar Annabi (saww) da Nana Faɗima (AS) da Mijinta Imamu Ali (AS) da 'Ya'yan su, Imamu Hassan (AS) da Imamu Husain (AS) da ƙin duk wanda ya cutar da su, duk girman darajar sa kowaye ?
IDAN DR. ABDULJABBAR (H) ZAI SHIGA WUTA SABODA ƘAUNAR (AHLULKISA'I), DA ƘIN KO TSINUWA GA WAƊANDA SU KA KARKASHE SU, TO SAI ABUL ABBAS MAULANA SHEHU AHMADU TIJJANI (R) YA RIGA SHI SHIGA.
HAKANAN, IDAN SHEIKH ABDULJABBAR (H) SUNAN SA (( ƊAN SHI'A )) TO TABBASSSSS, MAULANA ABUL ABBAS SHEHU AHMADU TIJJANI (R) SHI MA SUNAN SA ƊANSHI'A !!!
Yau zamu kawo maka inda Shehu Tijjani yake ɗura wa Makasan Ahlilbaiti zagi tare da tsinuwa kamar yadda Dr. Abduljabbar ke yi, zamu ji ko shi ma zaka iya ce da shi
Ɗanshi'a mai zagin sahabbai . Kuma zamu kawo maka inda yake fifita Nana Faɗima Azzahara (as) kan sayyidna Abubakar (ra) kamar yadda Malam Abduljabar ke yi , wanda ku ke cewa hakan zagin sahabbai ne ! Bisa Mas'alar nan ta gadon Annabawa da Nana faɗima AS ta ce ana yi, Sayyidna Abubakar (RA) Ya ce ba a yi. Wanda ta kai wasu daga manyan ku ke cewa, wai a faɗi kuɗin gonar gãdon da aka hana Sayyida Faɗima (AS) Suna da kuɗi za su biya 🙆!
Kai-tsaye, mu tafi cikin littafin nan wanda Dr. Abduljabbari (H) ya sharhanta, mai cike da yabon Annabi (saww) tare da jimamin kisan da aka yi wa Ahlin gidan Annabi saw wato Hamziyya littafin shehu Busiri (R) mai suna ( ILÃJUL JARĪH...) ya kawo bayanin da shehu Tijjani (R) ya yi , yayin sharhantar baiti na 331, don kafa wa wasu daga cikin Tijjanawan Hujja cewarsu, Malam ya zo da shi'anci, bisa bayanan da yake yi a kan cutarwar da wasu tsinannu s**a yi wa Ahlilbaiti, ta hanyar shayar da su guba, tare da tsinke ma su kanu zulman 😭😭😭😭😭 !!!!
" وبريحانتين طيبهما منـــــك الذي أودعتهما الزهراء "
Mu tafi shafi na (4) kuma fasali na huɗu(4)Inda Malam (H) ya ƙulla fasali mai bayani cewa tsakanin Nana faɗima (AS) da kuma Sayyidna Abubakar (R.A) wa ya fi a gurin Shehu Ahmaduttijani (R) ?????
{ أيهما أفضل عند الشيخ التجاني الزهراء أو الصديق}
A cikin wannan 👆 fasali Malam ya kawo yadda Shehu Tijjani (R) Yake nuna girman Imamu Hassan da Hussain (AS) tare da fifikon su a kan kowa , inda har yake kafa hujja da maganar Malik (ra), daga shafi na huɗu zuwa na biyar yake cewa :
حتى حكي عن مالك (رض) عنه قال: أما أنا فلا أفضل أحدا على بضعته صلى الله عليه وسلم .
Shehu Tijjani (r) ya ce , Maliku (r.a) ya ce
" NI BA NA FIFITA KOWA A KAN TSOKAR MANZON ALLAH (SAW) " ( wato Faɗima )
A nan magana ce dunƙulalliya ya yi amma ga Shehu Tijjani zai yi mana ƙarin bayani.
يشير إلى ما اجتمع عليه الأمة من تفضيل أبي بكر على فاطمة رضي الله عنها،أخبر عن نفسه أنه لا يقول بذالك وسكت.
Inji Shehu Tijjani ya ce : Manufar Maliku ita ce, bai yarda ba da wannan ijma'in da al'umma ta yi cewa Abubakar (ra) ya fi Fadima (AS). Wato haka Maliku yake nufi a cikin ransa amma bai faɗa ba sai ya yi shuru.
ثم قال :- وظهرت كرامتك بما أظهرت في الحسن والحسين وهما المرادون - بريحانتين اللذين أودعتهما الظهراء- فإنهما خرجا من بطنها رضي الله عنها و عنهما، و ظهرت تخصيصه (ص) لها حين أنزل الله عليه : إنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ البَيتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرََا '
Haryau, girmanka ya bayyana da abin da ya bayyana a kan Imamu Hassan da Imam Hussain (AS) waɗan da Shehu Būsīrī yake nufi da ( rīhãnataini ) waɗanda Fadimatu (AS) ta haifa. Domin su (Hasan da Husain) sun fito ne daga cikin cikinta (AS). Kuma Annabi (saww) ya nuna kebantar ta da wannan ayar ( Innama yuridullahu.......) lokacin da aka saukar masa da ita (saw) sai ya nuna ko suwaye Ahlilbaiti a aikace.
فهناك جمع (ص) فاطمة وعليا والحسن والحسين وهو معهم (ص) واشتملت عليهم كساء واحد وهو (ص) معهم . فقال (ص) حينئذ :- " اللهم هؤلاء أهل بيتي فطهرهم تطهيرا " فخصهم بذالك دون أهل البيت كلهم.
Inji Shehu Tijjani fa ! Ya ce : Annabi (saw) sai ya tattara Nana Faɗima, da Aliyu da Hassan da Hussain , ya san ya bargo ya lullube su tare da shi cikin bargon, Ya yi addu'a ya ce , Ya Ubangiji ga Ahalingidana Ka tsarkake su tsarkakewa'". Wato Annabi (saw) ya kenbance su, iya su huɗu da shi na biyar , ba tare da musharaka da duk wani iyalin gidansaba. Inji Shehu Tijjani !
ويؤيد ما قاله مالك بعدم تفضيل أبي بكر علي فاطمة، أنه صلي الله عليه وسلم ، دخل عليهما يوما - يعني فاطمة - فوجد الحسن والحسين بين يديها و علي هناك نائما في ناحية، فقال (ص) إنكِ و هذين وذالك النائم معي في درجة واحدة في الجنة. ولم يكن لأحد من النبيين والمرسلين فضلا عن غيرهم .
Shehu Tijjani ya ce : daga dalilan da suke ƙarfafar magabar Maliku cewa Abubakar bai fi Fadima ba ( yardar Allah ta tabbata a gare su ) Watarana Annabi (saw) ya shiga gurin Nana Faɗima (as) sai ya taras da Hassan da Hussaini a tare da ita, Imamu Ali kuma yana barci a gefe . Sai Annabi Ya ce (( Ke Faɗima da waɗannan 'Ya'yan naki da wancan mai baccin , daraja ɗaya za mu zauna gidan Aljannah. Wannan falala babu ɗaya da ya same ta daga Annabawa da Mursalai daga wasunsu. Anan Shehu Tijjani ya tsaya ya cigaba da sharhantar baiti na gaba. Kenan Shehu Tijjani shi ma ya zagi sayyidna Abubakar kuma ya zama ƊANSHI'A KENAN ????????????????????
GA INDA SHEHU TIJJANI YAKE TSINE WA MAKASAN AHLILBAITI 🙆♂️🙆♂️🙆♂️ !!!
Mu tafi fasali na biyar (5) daga shafi na (6) Za mu ga Malam (H) ya ƙulla wani fasali mai taken , Matsayar Shehu Tijjani a kan tsine wa Yazidu Dan Mu'awaiya .
{ موقف الشيخ التجاني من لعن يزيد بن معاوية }
صرح الشيخ التجاني تحت شرح البيت ٣٣٣ من الهمزية بلعن يزيد بن معاوية وإليكم بلفظه بالحروف :-
Malam (H) ya ce yayin da Shehu Tijjani (r) yake sharhantar baitin Imamu Busiri na cikin Hamziyya wato baiti na 333 ya yi bayani ƙarƙashin wannan baiti da tsinuwa ga Yazidu ɗan Mu'awiyata . Ga baitin 👇
من شهيدين ليس ينسيني الـطــف مصابيهما ولا كربلاء
A cīgaba da sharhantar wannan👆baiti da Shehu Tijjani ke yi yake cewa :
"من شهيدين ليس ينسيني...." البيت أشار بهذا إلى أنهما مقتلان معا ، أما الحسن ، فقتله اليزيد بن معاوية وذالك أنه بعث إلي زوجته إن سقته سما قاتلا أعطاها مئة ألف، فسقته سما قاتلا ، عليها وعليه لعنة الله !!! فهذا الشهيد الأول .
Shehu Tijjani ya ce , abin da Shehu Busiri yake nufi, Imamu Hassan da Hussaini duk kashe su aka yi . Shi Imamu Hassan wato Yazidu ne ya kashe shi, ya aika wa matar sa da guba yace idan ta saka wa mijinta Zai ba ta dukiya. Ita kuwa ( BINTU ƘAISU) sai ta saka wa Imamu Hassan ɗin guba a abinci ya ci ya yi shahada. ALLAH YA TSINE MA TA ALBARK, ITA DA YAZIDU ! Wannan shi ne shahidi na farko inji Shehu Tijjani.
والشهيد الثاني السيد الحسين، قتل بالطف من كربلاء ، وهو مكان مشهور بساحل الفرات ناحية العراق وهناك قتل في خمسمأة رضي الله عنه وأرضاه، فهم ثلاث وثمانون من بني هاشم ، منهم سبعة عشر من أولاد علي رضي الله عنه . والقضية مشهورة لا نطيل بذكرها.
Amma Shahidi na biyu shi ne Imamu Hussaini wanda aka kashe shi a wani guri da ake ce wa Ɗaffu daga Karbala zuwa dai inda Shehu Tijjanin yake cewa :
والطف هو مكان خاص بكربلاء فيه قتل رضي الله عنه قتله عسكر يزيد أميره عبد الله بن زياد ، هو الذي بعث الجيش إلي الحسين ليقتلوه ، فقتله الشمر بن ذي الجوشن، عليه لعنة الله والملائكة والناس أجمعين، ...
Shehu Tijjani (ra) ya ce : Gwamnan Yazidu Abdullahi Bn Ziyad shi ya aika da rundunar yaƙi don a kashe Imamu Hussaini. Sannan sai Shamru Bn Zil Jaushanu ya kashe Imamu Hussainin. ALLAH YA TSINE MA SA ALBARKA, DA MALA'IKU, DA MUTANE BAKI-ƊAYA, INJI SHEHU TIJJANI FA ! zuwa ƙarshe inda Malam ya yi ta kawo ragowar baitukan da Shehu Tijjanin ya sharhanta da yake tsine wa Makasan Ahalin gidan Manzon Allah (saww). Idan wannan shi'anci ne kenan Shehu Tijjani ma ƊANSHI'A NE ???????
Ina tare da Shehu Tijjani da kuma Shehu Abduljabbar Nasiru Kabara Kano %%%.
🇳🇬
Yaumul Jabbariyya tana tafe kuma bana ta musamman ce 2 ga watan july.
22/06/2026
Zaman Kotu na yau Litinin 22/6/2026. Sheikh Abduljabbar kabara da Gwamnatin Kano State.
Ministry sun nemi a qara musu lokaci sakamakon yau basu shirya ba, anan kotu ta basu dama zuwa ranar 29/06/2026, kwanaki 7 kenan.
Insha Allah Maulana Amirul Wa'izeena (H) yana akan nasara tabbatacciya alfarmar Shugaba (SAWW), don haka kada muyi qasa a gwyiwa wajen cigaba da addu'o'in da muke yi tare da kaucewa duk wani abu da zai haifar da fitina ko sa6a dokar Allah da dokar qasa, dama ba'a sammu da hakan ba.
~ Jilani Makwarari Aljabbary
21/06/2026
Dangane da Shari’ar Maulanah Amirul Wa’iziyna (H) ga lazumi da kowane ɗan makaranta ake so yayi a daren yau.
Zaka karanta ayar مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ kafa 17 sai ka roki Allah bukatar(samun rinjaye da tabbatar adalci akan Shari’ar) sai ka kara karantawa ita wannan ayar مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ kafa 107 sai ka kara tsayawa ka roki Allah bukatar sai ka kuma kara karantawa kafa 1007 sai ka kara rokon Allah bukatar a rufe da yiwa Annabi S.A.W salati da ya'yan ɗakin sa.
Muna rokon Allah rinjaye da samun galaba akan wadannan azzaluman kada kuma a manta da markar Hasbunallahu wani’imal wakilu.
~ Muhammadu Hafizu Yusuf
Part cikin martani xuwa Baba impossible tare Da 100029605396598:2048:Shareef Abduljlalal Habibu Part 15
Part cikin martani xuwa Baba impossible tare Da 100029605396598:2048:Shareef Abduljlalal Habibu Part 14
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Gano Maiduguri Road
Kano