AP Hausa

AP Hausa

Share

Muna Ɗauke Da Duk Wani Shirye Shiryen Da S**a Shafi Baƙon Mu Na Mako Dama Na GwarzayEn Shikara.

09/01/2022

Kar ku bi jam'iyya ko addini a zaɓen 2023 - Sarki Sanusi

Khalifan Tijjaniyya na Najeriya Sarki Muhammadu Sanusi II, ya bukaci wadanda s**a cancanci kaɗa ƙuri’a su je su yanki katin zaɓe gabanin babban zaben 2023.

Yana magana ne a wajen taron shekara-shekara na tunawa da ranar haihuwar mazon Allah Annabi Muhammad.

Sanusi ya yi kira ga jama’a idan zaɓen ya zo su zaɓi shugabanni na gari ba tare da la’akari da siyasa ko addini ba.

“Idan matasanmu s**a samu aikin yi, tattalin arzikin kasar baki daya zai inganta. Mafi mahimmanci, mu ba jam’iyya ba ce, amma ba za mu iya naɗe hannayenmu mu yi watsi da siyasa ba.

“Duk dan Attijaniyya daga shekara 18 zuwa samanamiji ko maceje ka karbi katin zabe. Allah yana umurce ku da ku dogara ga hannun muminai amintattu. Yanzu muna wani lokaci da jama’a ne ke da ikon naɗa shugabanni, ƙuri’arku ita ce ƙarfin ku, kuna da nauyi a kanku’’ inji Sarki Sanusi.

Hausa Online News

08/01/2022

Likitan Da Yake Yiwa Mata Maganin Muni A Amurka 1930s.

'Micrometer,' wanda kuma aka sani da 'beauty calibrator,' wata na'ura ce da aka tsara a farkon shekarun Alif da Ɗari Tara da Talatin (1930) da babban masanin kyay Max Factor ɗan ƙasar Poland ya ƙera don taimakawa wajen gano wuraren fuskar mace wanda ke buƙatar ingantawa.

Zane na 'Beauty Micrometer' ya kasance ƙaton ƙarfe ne wanda ke auna gefuna na fuskar mace tare da sassauƙaƙƙen sassan ƙarfe waɗanda s**a yi daidai da yanayin fuskar mutum. Akwai yiwuwar a sami gyare-gyare Ɗari Ukuda Ashirin da Biyar (325), a fuskar mace.

Hausa Online News

Photos from AP Hausa's post 08/01/2022

INNAA LILLAAHI WA INNAA ILAIHI RAAJI'UN😭

DA DUMI DUMINSU: Gobara Ta Tashi A Kasuwar Nguru Dake Jihar Yobe

Rahotanni daga jihar Yoben Najeriya na cewa gobara ta tashi a babbar kasuwar Nguru da ke jihar.

Waɗanda s**a shaida lamarin sun bayyana wa BBC cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe takwas na safiyar Asabar.

Sun kuma bayyana cewa gobarar ta tashi ne daga sashen ƴan takalma da kuma ƴan robobi kuma ta laƙume shaguna ba iyaka.

Tuni dai jami'an kai agaji da kuma na kashe gobara s**a isa wajen domin kashe gobarar.

Mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin inda ya ce tuni jami'an kashe gobara da matasa s**a haɗa hannu inda suke ƙoƙarin kashe gobarar.

Haka kuma ya tabbatar da cewa ƴan sanda da sauran jami'an tsaro sun isa wurin domin tabbatar da tsaro.

~BBC Hausa

Photos from AP Hausa's post 06/01/2022

2023: APC ta sulhunta Goje da gwamnan Gombe, Yahaya

Kwamitin Shugabacin Jam'iyar APC na Wucin-gadi, ƙarƙashin jagorancin Mai Mala Buni ya sulhunta tsakanin Gwamna Muhammad Yahaya na Jihar Gombe da kuma abokin burmin sa na siyasa, tsohon gwamnan jihar, Sanata Ɗanjuma Goje.

Jami'in Yaɗa Labarai na Buni, Mamman Mohammed ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba a Abuja.

Ya ce Buni, da Shugaban Kwamitin Sulhu na APC, Sanata Abdullahi Adamu da Kashim Shattima, mamba a kwamitin, su su ka jagoranci sulhun.

Sanarwar ta ce wannan shine karon farko da manyan ƴan siyasar na Gombe su ka haɗu tun bayan da rigimar siyasa ta ɓarke tsakanin su a shekarar bara.

Buni, wanda shine kuma Gwamnan Jihar Yobe, ya baiyana jin daɗin sa game da sulhun da a ka yi.

Ya kuma ci alwashin sulhunta duk masu ruwa da tsaki a APC domin ƙarfafa jam'iyar yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe ta 2023.

04/01/2022

Bayan shafa ta tsanaki, al'aurar mace na fara kumbura domin nuna shiryawa ko amincewa da sabon sakon da aka aike mata, hakan na sanya mahaifa ta share hanya yayin da miji da mata ke karasa sauran aikin.

📸 AP Hausa

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


Kano