SARAUNIYA
Big shout out to my new rising fans! Muhamadu Sada
04/09/2025
Buɗe Wa Ma'aikatan Masana'anta Wuta: Rundunar Ƴan Sanda Ta Gayyaci Shugabar Algon
Daga Yasir Kallah
Rundunar Ƴan Sandan jihar Kano ta gayyaci shugabar ƙaramar hukumar Tudun Wada, kuma shugabar ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano (ALGON), Sa'adatu Salisu, kan zargin jagorantar wasu ƴan daba wajen kai farmaki a kan wasu ma'aikatan wata masana'anta da ke aiki a ƙaramar hukumar.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta yi rahoton cewa ma'aikatan masana'antar Tasarrufi General Enterprise ne s**a shigar wa da hedkwatar ƴan sandan jihar Kano da ke Bompai ƙarar shugabar ƙaramar hukumar kan zargin bai wa wasu ƴan daba umarnin kai musu farmaki da adduna, tare da umartar odilanta da ya buɗe musu wuta, wanda kuma hakan ya jawo mutane da yawa s**a jikkata da samun rauni.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, ya bayyana cewa rundunar ta fara bincike a kan lamarin tare da aika gayyata ga dukkan waɗanda batun ya shafa, ciki har da shugabar ƙaramar hukumar.
Kiyawa ya kuma ce, “An shigar da ƙorafi a kan shugabar Algon ɗin. An gayyaci dukkan shaidun da kuma wadda ake zargin. An kuma yi kiranye ga odilan shugabar ALGON ɗin da ya je hedkwatar ya bayar da bayani a kan abin da ya faru."
29/11/2023
Zanga-Zangar Unguwar Kurna: Yadda Ɗan Sanda Ya Harbe Salisu Player
Daga Isyaku Kabir Rio
"Jiya a can Ƙasan Layi faɗa ya rincaɓe tsakanin wasu yara har aka karya wa mutum biyu a hannu. Ana cikin rikicin ne wani yaro ya mari wata yarinya. Ganin hakan ne ya sanya yayan yarinyar ya ce Wallahi ba za su yarda ba, sai sun ɗau fansa. Shi ne ya je bakin titin Ƴan Doma Motors ya ɗauko ƴan daba domin su zo su ɗaukar wa ƙanwarsa fansa.
"Shi ne cikin daren nan ƴan daban s**a shigo domin ɗaukar wa ƙanwar abokinsu fansar marin da aka yi mata. To a dalilin haka ne aka sanar wa ƴan sanda s**a shigon cikin unguwar s**a kora yaran. To sai yaran s**a fito saman unguwar suna zage-zage, suna barazana ga mutane, suna saka mutane gudu, masu shaguna suna rufewa.
"To a daidai lokacin ne matasan unguwarmu, nan kan gadar gidan mai unguwa waɗanda suke bai wa unguwarmu tsaro s**a yi shiri domin hana waɗannan 'yan Dldaban shigowa cikin unguwar tamu su yi sata ko su ji wa mutane ciwo. A daidai lokacin matasan unguwarmu s**a tanadi duwatsu domin su ba su da makami irin na ƴan daba.
"Can muna tsaye sai muka hango mutane sun taho ana ta gudu. A daidai lokacin ne shi marigayi SALISU PLAYER ya ce min, "RIO ga su nan fa. Mu gudu, ƴan daba ne." Sai na ce masa 'wallahi ba inda za ni. Su zo mu gan su. Cikinsu babu wanda ba mu sani ba.' Ni ma na riƙe dutse a hannuna. Muna tsaye tare da ni akwai Deeni Amana. Shi kuma SALISU PLAYER sai ya gudu. Ashe bai tsira ba daga harbin tsinannen Ɗan Sanda😭😭
"Muna tsaye ayarin ya zo ya same mu. Waɗansu matasa ne da masu manyan kaya a jikinsu suna ihu ɗauke da makamai irin su katako, adda, barandami. Suna tafe suna ɗuɗɗura ashariya. Ganin haka sai su kuma waɗannan matasan masu kula da unguwa s**a sa musu jifa da duwatsun nan suna cewa ƙarya ne. Kawai a take a wurin sai na ji harbin bindiga daga cikin ƴan daban. Ashe wai ƴan sanda ne a cikinsu suna tare.
"Wallahi billahillazi ba mu ankara ba sai gani na yi a gabana an harbi ɗan uwana USMAN IG. Harsashin ya gogi hannunsa ya wuce cinyar SARKI ZILADAINI. Saii ya kara harba bindigar, shi ne ya kashe SALISU PLAYER 😭"
03/11/2023
Falana Ya Koka A Kan Hukuncin Shari'ar Kano, Ya Ce Alƙalai Na Hukunta Masu Zaɓe A Kan Kura-Kuran Da INEC Take Yi
Fassarawa: Yasir Kallah
Babban lauyan nan mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam na Nijeriya, Femi Falana, SAN, ya koka a kan hukuncin shari'ar kotun sauraren ƙararrakin zaɓen kujerar gwamna ta jihar Kano wadda ta soke nasarar gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Idan ba a manta ba, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya, INEC, ta bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar gwamna ta jihar Kano da aka kaɗa a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Da yake jawabi a wani shiri na gidan talabijin ɗin Channels, Falana ya ce: "Bai kamata ka hukunta masu zaɓe a kan kura-kuran da INEC ta yi ba. Hakan ne abin da ya faru ba da jimawa ba a Kano, inda aka ce jami'an INEC ba su maka ƙuri'u dubu 65 ba."
Ya ƙara da faɗin cewa: "Muna kira ga alƙalai da su rungumi adalci, adalci na haƙiƙa, ta hanyar da ba za ka iya hukunta masu zaɓe a kan kura-kuran da INEC ta tafka ba."
A dangane da tsari na doka, matuƙar an ƙirga ƙuri'un sannan an bayyana wanda ya samu nasara, "Ba za ka iya ƙalubalantar ingancin takardun zaɓen ba".
"Saboda haka, ina ganin waɗannan ne wuraren da alƙalanmu ya kamata su koma baya su gyara," inji Falana.
31/08/2023
Guguwar Juyin Mulki: Tsoro ya sa shugaban ƙasar Ruwanda ya kori manyan sojojin ƙasar
A ranar Laraba, Paul Kagame, shugaban ƙasar Ruwanda, ya bayar da umarnin yi wa wasu sojojin ƙasar ritaya. Sojojin da ritayar ta shafa sun ƙunshi janar guda 95 da ƙananan sojoji 930.
Na gaba-gaba a cikin jerin sunayen sojojin shi ne Janar James Kabarebe, tsohon ministan tsaro, kuma tsohon babban hafsan tsaron ƙasar.
An wallafa sunayen sojojin da aka yi wa ritayar a kan sahihin shafin yanar gizon jami'an tsaron ƙasar a ranar Laraba.
Sanarwar ta fito bayan juyin mulkin da aka ƙaddamar a ƙasashen Niger da Gabon.
Kafin a yi masa ritaya, Janar Kabarebe ya kasance mai bai wa shugaban ƙasar shawara na musamman a kan tsaro.
Wasu kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun bayyana cewa wasu daga cikin sojojin sun cimma shekarunsu 65 na ritaya yayin da wasunsu kuma aka zarge su a kan aikata wasu laifuka.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
M 31 Farin Bene, Yan Awaki Road, Unguwa Uku, Tarauni LGA
Kano
234