Daily Observer Hausa
02/11/2022
Sa6ani Tsakanin Garo Da Doguwa: Jam'iyyar APC A Dunkule Take - Mataimakin Gwamna
Mataimakin Gwamnan Kano kuma 'Dan takarar Gwamna a jam'iyyar APC mai mulki Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da lamarin da ya afku na sa6ani tsakanin 'Dan takarar mataimakin gwamna Alhaji Murtala Sule Garo da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai ta tarayya Hon. Alhassan Ado Doguwa.
Mataimakin Gwamnan yace abinda ya farun a daren ranar Litinin a gidansa dake Miller Road a Unguwar Bompai tsakanin jiga-jigan jam'iyyar biyu, lamari ne mara dadi, sai dai yace sa6ani ne da kan iya faruwa tsakani, sak**akon ajizanci na 'Dan Adam, a saboda haka yace suna bin dukkan makatai na kiyaye afkuwar hakan a nan gaba.
Dr. Nasir Yusuf Gawuna wanda yayi magana ta bakin babban Sakataren Yada labaran sa Malam Hassan Musa Fagge, yace Jam'iyyar APC a dunkule take a matsayin uwa daya uba daya.
A saboda haka ya bukaci magoya baya daga bangarorin jagororin biyu da su mutumta dokokin jam'iyyar ta hanyar kiyaye lafuzan su, cewar nasarar jam'iyyar APC itace abin sanyawa gaba domin cigaban jihar Kano da al'ummar ta.
02/08/2022
Muna taya Hon. Abubakar Musa DK mataimaki na musamman a bangaren kafar sadarwa ta zamani, ga mataimakin Gwamnan Kano, Dr. Nasir Yusuf Gawuna, murnar auren sa da aka daura a ranar Asabar din karshen makon da ya gabata, tare da amaryar sa Haleematu Sadiya.
Muna rokon Allah ya sanya alkhairi a cikin auren, ya kuma azurta su da zuriyya dayyiba. Haka zalika muna addu'a ta fatan alkhairi ga dukkan auren da aka daura.
18/12/2021
Majiya- Daga Shafin Shugaba Buhari
Yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yanka cake ranar Jumu'ah a kasar Turkiya domin bikin murnar cikar sa shekaru 79 da haihuwa.
A cewar shugaba Buhari k**ar yadda ya wallafa a shafin sa na Facebook, ya bayyana cewa a halin yanzu yana jiran zuwan shekarar 2023 ne inda wa'adin mulkin sa zai kare ya koma gida mahaifar sa domin cigaba da kulawa da gidan gonar sa.
Kafin hakan, shugaban yace daga yanzu zuwa wancan lokacin zaiyi dukkan mai yiwuwa wajen kyautata Najeriya da rayuwar al'ummar cikinta, ta hanyar tafiyar da ayyukan sa k**ar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.
Sai dai da dama al'umma na ganin cewa abin kunya ne da takaici aga shugaban yana irin wadannan bukukuwa, alhalin al'ummar da yake jagoranta na fuskantar nau'uka daban-daban na barazanar tsaro, kuma musamma yadda aka hango shugaban cikin hoto a kasar ta Turkiya ya daga wuka ya dabawa cake din mai dauke da hoton Tarayyar Najeriya, wanda hakan ya dada saka shakku a zukatan mutane na irin salon soyayyar sa ga kasar.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano