Lessons in 1 Minute
14/05/2026
Rannan Na hau Keke Napep zanje Unguwa sai wasu Mata guda biyu s**a shigo ana tafiya suna hirarsu ta duniya da ni dai inata jan Carbina.
Siririyar ta cewa" Lukutar Ke kin yiwa Zee jaje kuwa?
Lukutar tace" me ya faru da ita?
Siririyar tace" bakisan kwanan gida taje ba aka samu matsala tayi targade
Lukutar tace" Dama matsalar kwanan gida kenan yanzu sauro yayi yawa matukar baki da maganin sauro sai kin kwaso Maleria
Siririyar tace" Hakane yanzu fa kwanan gida a matsala ne gwanda Kwanan Waje yafi tsaro musamman idan babanku baya gari.
Da naji hirar tasu tayi nisa, sai na ɗauko wayata na danna kira kamar da gaske kiran Wani nake sai nace" Hello!! Nisa'u a ajiye Waya?
Muka ci gaba da tafiya har aka zo inda zasu sauka bayan sun sauka daga Napep ɗin, sai Direban Napep ɗin ya kasa yin shiru yake ce min malam kaga zamani ko?
Yanzu dubi Yara ƴaƴan Musulmai ne s**a gwammace kwana a waje fiye da gidajen Iyayensu har suna hirar a t**i basa jin kunya.
Ni dai Nayi masa shiru saida aka zo inda zan sauka na bashi ƙudinsa nace" masa Baba duk sadda kaji ance maka Kwanan Gida ana nufin kwanan Hotel
Su waɗancan Matan da kaji suna maganar Kwanan Gida suna nufin Ƙawarsu ce ta kwana a Hotel aka kamata amma ba'a kulleta ba kuma iyayenta basu sani ba shine targaɗen da tayi.
Ni kuma da kaji na buga waya nace a Ajiye Waya" ina nufin suyi shiru saboda nazata ka fara gane hirar da sukeyi ne. Ashe ma kai Ciki Ne Ba Waje Ba.
Mai Keke Napep ɗin kawai sai a ɗora hannu a kansa yace" LAILALAHA ILLALLAHU Ashe Duk Ƴan Iska Uku na kwaso bansani ba nake ta kiranka da Malam kana amsawa...!😂
Kawai sai Nayi gaba ina jan Carbina Nabarshi iya mamaki.🥴🚶
01/05/2026
3 Signs of Fake Friends
New musician | Sabuwar ma'aikaciya
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano