Vanguard Hausa
Rundunar Tsaron Kasar Iran Tace Cigaba Da Hare-haren Izraela a Gaza da Lebanon Zai Jawo Matakin da Zai Shafin Mashigar hormus 👇
01/06/2026
Yaudarar POS: Yadda Wani Matashi Ya Tafi da Naira Dubu 86,400 Cikin Dabara
Wata matashiya mai sana’ar POS ta shiga cikin tashin hankali bayan wani saurayi ya yi amfani da dabara wajen karɓar kuɗi fiye da yadda ya cire daga asusunsa.
Rahotanni sun nuna cewa saurayin ya je wajen POS domin cire kuɗi har Naira dubu casa’in da shida (₦96,000). Matashiyar ta karɓi katin ATM ɗinsa, ta saka adadin kuɗin a na’urar POS sannan ta miƙa masa domin ya saka lambar sirrinsa (PIN).
Yayin da yarinyar ke ƙirga kuɗin da za ta ba shi, saurayin ya yi amfani da damar da ya samu wajen sauya adadin kuɗin daga ₦96,000 zuwa ₦9,600 bayan ya saka PIN ɗinsa.
Ba tare da ta lura da abin da ya faru ba, ta kammala ƙirga kuɗin ta ba shi Naira dubu casa’in da shida (₦96,000). Bayan ya tafi ne ta sake duba bayanan cinikin (transaction) inda ta gano cewa a zahiri an cire Naira dubu tara da ɗari shida (₦9,600) kacal daga asusun saurayin.
Hakan ya sa ta yi asarar Naira dubu tamanin da shida da ɗari huɗu (₦86,400) sak**akon wannan dabara da ake zargin saurayin ya yi amfani da ita.
Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce tare da zama darasi ga masu sana’ar POS da su riƙa tabbatar da adadin kuɗin da aka saka a na’ura kafin da bayan abokin ciniki ya kammala saka PIN ɗinsa.
01/06/2026
Malaman Makarantu a Jahar Oyo Sun Yi Barazanar Tsayawa Aiki Har Sai An Ceto Dalibai 46 Da Aka Sace
Wani rubutu da ya bazu a kafafen sada zumunta ya jawo muhawara bayan ya bayyana cewa kungiyar malamai ta jihar Oyo (NUT) ta bukaci malamai su daina zuwa aiki har sai an kubutar da yara 46 da masu garkuwa da mutane s**a sace.
Marubucin sakon, Salisu Yakubu RN RNT, ya nuna takaicinsa kan yadda yake ganin al'ummomin Arewa ke mayar da martani ga matsalolin tsaro idan aka kwatanta da yadda wasu yankuna ke hada kai wajen neman hakkokinsu.
Ya bayyana cewa an sha fuskantar hare-hare, kashe-kashe da sace-sacen mutane a Arewacin Najeriya, amma bai ga irin tsauraran matakan matsin lamba ga gwamnati da ake dauka a wasu wurare ba.
Sakon ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu s**a goyi bayan ra'ayin marubucin, yayin da wasu s**a ce ya k**ata a guji kalaman da za su iya haifar da rarrabuwar kawuna, a maida hankali wajen nemo mafita ga matsalolin tsaro da s**a addabi kasa.
"Tsaro da kare rayukan jama'a hakki ne na kowa, kuma ya k**ata al'umma su hada kai wajen neman mafita cikin lumana da fahimtar juna," in ji wasu daga cikin masu sharhi kan lamarin.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano