SSR and SR Updates
16/04/2026
Bayan gyaran Makarantar GGSS Gandun Albasa tare da samar da kujeru da kayan karatu, a karo na farko dukkan ɗaliban da s**a zana jarrabawar Qualify sun samu nasara gaba ɗaya.
Jimillar ɗaliban da s**a ci jarrabawar sun kai 701, wanda hakan ke nuna irin ƙoƙari da jajircewar Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wajen tabbatar da ingancin ilimi a jihar Kano
Wannan na Zuwane a wata Ziyara da Director KERD Hajiya Rabi Inuwa Hussain, tare da Ma’aikatan Hukumar domin yiwa Daliban Albishir Na Gagarumar Nasarar da S**a Samu
Tabbas Dolene mu godewa Allah da ya bamu Abba Gida-Gida Allah ya kara masa Nasara.
Amir Abdullahi Kima
Chairman SSR/SR Forum Kano State.arar
14/04/2026
KWAMISHINAN SHARI’A NA JIHAR KANO YA DAUKI NAUYIN DALIBAI 301 DOMIN KARANTAR NCE A MUNJIBIR
Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Abdulkarim Kabiru Maude,SAN, ya ɗauki nauyin ɗalibai 301 domin su ci gaba da karatun NCE a Makarantar Kano State College of Education and Preliminary Studies (KASCEPS), reshen Munjibir.
Hakan na kunshe ne a jawabin Kwamishinan da ya gabatar yayin taron bikin da aka gudanar a harabar makarantar, inda ɗalibai, malamai, da manyan baki s**a halarta domin shaida wannan gagarumin tallafi da kwamishinan ya bayar.
A Jawabin nasa, Kwamishinan ya bayyana ƙudurin sa na ganin ya tallafawa ilimi ba tare da yankewa ba, inda har ya bada wasiyya cewa ko da Allah ya karɓi rayuwarsa kafin ƙarshen wannan shiri, iyalansa su tabbatar sun cire kuɗin makarantar ɗaliban gaba ɗaya har su kammala karatunsu.
Haka kuma, ya yi alƙawarin cewa bayan sun kammala karatun NCE, zai ci gaba da ɗaukar nauyinsu domin su ci gaba da karatu a matakin jami’a, domin ƙara inganta rayuwarsu da makomar al’umma baki ɗaya.
A Lokacin da take jawabi, Malama Jamila Mansur Chiranchi, Shugabar Laburari ta Makaranar, wacce ta wakilci shugaban Makarantar, Dakta Auwal Farouk, ta jinjinawa Kwamishinan bisa wannan karamci da hangen nesa da ya nuna, wanda ta bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na inganta ilimi da tallafawa matasa domin su cimma burinsu na rayuwa.
Wasu daga cikin waɗanda s**a yi jawabi sun bayyana cewa wannan shiri zai taimaka matuƙa wajen rage yawan ɗaliban da ke fuskantar ƙalubalen kuɗin makaranta, tare da ƙarfafa gwiwar sauran masu hannu da shuni su ma su bada tasu gudummawa wajen bunƙasa ilimi a jihar.
Haka kuma, ɗaliban da s**a ci gajiyar shirin sun nuna matuƙar farin ciki da godiya ga Kwamishinan, tare da alƙawarin mayar da hankali kan karatunsu domin su zama masu amfani ga al’umma da ƙasa baki ɗaya.
Taron ya gudana cikin yanayi na farin ciki da nishadi, inda aka yi addu’o’i da fatan alheri ga Kwamishinan da kuma ɗaliban da s**a samu wannan dama.aime ama arayar.
Amir Abdullahi Kima
Senior Special Reporter on Ministry of Justice to the Executive Governor of Kano State Alhaji Abba Kabir Yusuf
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano