Fasihiya

Fasihiya

Share

Photos from Fasihiya's post 25/05/2026

ZAƁEN FIDDA GWANI TINUBU YA SAMU GOYON BAYA MAI KARFI A SOKOTO.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu gagarumar nasara a zaɓen fidda gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Sokoto tare da sauran sassan ƙasar nan.

Bayan kammala tattara sakamakon zaɓen, shugaban tawagar gudanar da zaɓen APC a jihar Sokoto, Shine Mai Girma Gwamna Dr. Ahmad Aliyu Sokoto, Inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’u dubu dari uku da ɗaya (301,001), lamarin da ya nuna cikakken goyon baya daga wakilan jam’iyyar a jihar.

Zaɓen ya gudana cikin lumana da tsari, yayin da magoya bayan jam’iyyar s**a bayyana farin cikinsu kan sakamakon da aka samu.

✍️ Ashir Mai Jama'a Bado
--->Daga Sokoto
--->24 May 2026

Photos from Fasihiya's post 24/05/2026

SHUGABA TINUBU YA KARBI BAKUNCIN SANATA WAMAKKO A LEGAS

Yadda Mai girma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar 22 ga Mayu, 2026 ya karɓi bakuncin jagoran jam’iyyar APC a Jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, a gidan zamansa da ke Jihar Legas.

Ziyarar Taron ya mayar da hankali ne kan haɗin kan jam’iyya da kuma cigaban ƙasa a Najeriya.

Ziyarar ta kuma nuna kyakkyawar alaƙa da ke tsakanin Shugaban Ƙasa Tinibu da tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Kuma Jagoran Jam'iyar APC sanata Wamakko.

✍️ Ashir Mai Jama'a Bado
--->Daga Sokoto

22/05/2026

Najeriya da Poland Za Su Hada Kai Kan Tsaro da Bunƙasa Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na yin aiki kafada da kafada da ƙasar Poland wajen inganta harkokin tsaron cikin gida da bunƙasa tattalin arziki.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi Mataimakin Firaministan Poland, Krzysztof Gawkowski, a ofishinsa da ke Abuja ranar Alhamis.

Tunji-Ojo ya ce Najeriya na da burin anfani da ƙwarewar Poland wajen kula da iyakoki da kuma dabarun tsaron cikin gida da s**a tabbatar da nasara a ƙasar.

Ya ce gwamnatin Najeriya na sa ran yin haɗin gwiwa da Poland musamman a fannoni kamar horas da jami’ai, amfani da fasaha, tsaron yanar gizo da sauran muhimman fannoni.

“Mun yi imani cewa haɗin kai da koyo daga juna ne hanya mafi dacewa wajen rage rauninmu tare da ƙarfafa bangarorin da muke da ƙwarewa,” in ji shi.

Ministan ya tabbatar wa baƙin cewa ziyarar ba za ta zama ta al’ada kawai ba, domin za ta zama tubalin da za a gina dangantaka mai ɗorewa tsakanin ƙasashen biyu.

Ya kuma bayyana cewa ana shirye-shiryen kai ziyara ƙasar Poland domin ƙara zurfafa tattaunawa da gwamnatin ƙasar da kuma ɓangaren kasuwanci masu alaƙa da ma’aikatar harkokin cikin gida.

Tunji-Ojo ya ƙara da cewa manufofin tattalin arzikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na nuna cewa gwamnati na fahimtar hanyoyin gina tattalin arziki mai ƙarfi.

A nasa jawabin, Mataimakin Firaministan Poland, wanda kuma shi ne Ministan Harkokin Dijital na ƙasar, Krzysztof Gawkowski, ya ce Najeriya ƙasa ce mai tarin albarkatun tattalin arziki, yawan jama’a da kuma damar ci gaban fasaha.

Ya bayyana Najeriya a matsayin muhimmiyar abokiyar hulɗa wajen gina dangantaka mai ɗorewa tsakanin ƙasashen biyu.

Gawkowski ya ce Poland a shirye take ta taimaka wa Najeriya ta hanyar ƙwarewarta a fannoni kamar kirkire-kirkire, fasahar zamani, gina ababen more rayuwa da kuma sabbin dabarun fasaha.

Haka kuma ya bayyana fatan ganin Ministan Harkokin Cikin Gida na Najeriya ya kai ziyara Poland domin ƙara ƙarfafa alaƙar ƙasashen biyu.

20/05/2026

Yadda Ake Maida Arewacin Najeriya Cibiyar Zuba Jari Ta Hanyar Manufofin Shugaba Tinubu

Daga Aliyu Samba

Arewacin Najeriya yana fuskantar gagarumin sauyi na tattalin arziki wanda ke mayar da yankin wata babbar cibiya ta zuba jari da kasuwanci a Afirka ta Yamma. Wannan ci gaba ba ya rasa nasaba da tsare-tsare da kudaden shiga na musamman da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke turawa yankin ta karkashin tsarin Renewed Hope Agenda.

Gwamnatin tarayya ta mayar da hankali ga samar da ababen more rayuwa, bunkasa makamashi, da inganta fannin noma domin janyo hankalin masu zuba jari na gida da na waje.

1. Manyan Ayyukan Hanya da Sufuri (Infrastructure)
Ayyukan Hanyoyi na Musamman: Cikin ayyukan guda 260 da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya ke aiwatarwa a fadin kasa, yankin Arewa maso Yamma kadai yana da guda 48 da ake gudanarwa a yanzu. Wannan ya hada da hanyar Kaduna Western Bypass da ta shafe shekaru 22 tana mace wadda yanzu ta kusa kammala, da kuma amincewa da gina hanyar Mando zuwa Birnin Gwari ta kilomita 122 akan kudi N178 billion.
Sufurin Jirgin Kasa na Zamani: Aikin layin dogo na Kaduna-Kano-Katsina-Maradi (Jamhuriyar Nijar) wanda ke da tsawon kilomita 203 yana cigaba da gudana. Wannan layin dogo zai hada kasuwannin Arewa kai tsaye da tashar jirgin kasa ta cikin kasa ta Dala Dry Inland Port da ke Kano, lamarin da zai saukaka jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje.
Babban T**i na Sokoto-Badagry Super Highway: Wannan babban t**i mai tsawon kilomita 1,068 zai hada Arewa da Kudancin kasar ta fannin kasuwanci da zuba jari.
2. Juyin Juya Hali a Fannin Noma da Ruwa
Domin tabbatar da cewa Arewa ta kasance jagaba wajen samar da abinci da albarkatun masana'antu, gwamnatin Tinubu ta zuba biliyoyin nairori a fannin banruwa da raya karkara.

Aikin Banruwa na Garko: Gwamnatin ta hanyar asusun kiyaye muhalli (Ecological Fund) ta zuba kudi har Naira Biliyan 27 don samar da dandalin noman rani na zamani.
Taimakon Masu Noma: An kafa cibiyar fasahar noma ta Agricultural Incubation Centre mai fadin hekta 10 ta hanyar hukumar NASENI don koya wa matasa da manoma dabarun kasuwancin noma na zamani.
3. Fadada Fannin Makamashi da Gas (Energy Sector)
Bayan aiwatar da dokar masana'antar man fetur (PIA), gwamnatin Tinubu ta samar da sabbin sauye-sauye don amfani da iskar gas (Natural Gas) wajen gudanar da masana'antun Arewa.

A taron makamashi na Nigeria International Energy Summit (NIES), an bayyana cewa samar da iskar gas a cikin gida ya zarce 2 BSCFD a karon farko, kuma ana amfani da wannan damar wajen samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana (Solar energy projects) wanda Hukumar Makamashi ta Najeriya (ECN) ke kafawa a sassan Arewa don rage tsadar gudanar da masana'antu.

4. Lafiya da Habaka Jari na Dan Adam (Human Capital)
Zuba jari ba zai dore ba idan babu koshin lafiya da ilimi ga al'umma. Shi ya sa gwamnatin tarayya ta amince da gina manyan asibitoci da cibiyoyin kwarewa:

Abubuwan more rayuwa irin su asibitin kwararru na Bola Ahmed Tinubu Specialist Hospital mai gado 300 a Kaduna, da asibitin koyarwa na Aminu Kano Teaching Hospital (inda ake gina cibiyoyin cututtukan zuciya da na yara), suna tabbatar da cewa ma'aikata da masu zuba jari za su samu kyakkyawan tsarin kiwon lafiya.

Bugu da kari, shirin Renewed Hope Baby Support (RHBS) wanda Hukumar Raya Shiyyar Arewa Maso Gabas (NEDC) ta kaddamar yana taimaka wa mata da yara ta hanyar hada harkar lafiya da rajistar zama dan kasa, wanda ke zama ginshikin gina al'umma mai inganci.

Me Yasa Za A Zuba Jari a Arewacin Najeriya Yanzu?
Kamata ya yi masu zuba jari su gane cewa kudaden shiga da gwamnatin tarayya ke samu bayan cire tallafin mai da gyaran tsarin canjin kudi ana tura su ne kai tsaye zuwa ga ayyukan raya kasa. Kamar yadda gwamnonin yankin (kamar na Kaduna da Jigawa) s**a tabbatar, karuwar kudaden shiga daga gwamnatin tarayya ya ba su damar bude sabbin yankunan masana'antu da hanyoyin karkara.

Yanzu ne mafi kyawun lokaci ga masu zuba jari na gida da na kasashen waje za su karkata akalarsu zuwa Arewacin Najeriya, domin samun moriyar saukin sufuri, yalwar makamashi, da kasuwa mai fadi da gwamnatin Shugaba Tinubu ta shimfida.

Photos from Fasihiya's post 20/05/2026

Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji zai ƙara amincewar jama’a da tsarin haraji – Ministan Yaɗa Labarai

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyar ta ta gina tsarin gudanar da haraji mai tsare gaskiya, tare da mayar da hankali kan buƙatun ’yan ƙasa, a wani ɓangare na Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja yayin ƙaddamar da gidan yana na hukumar da kuma cibiyar karɓar kiran waya kyauta ta ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji.

Ministan ya bayyana ƙaddamar da sababbin dandalan a matsayin wani babban mataki na ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin haraji a Nijeriya.

Ya ce: “Wannan wani babban mataki ne wajen ƙarfafa amincewar jama’a da inganta samun damar amfani da ayyuka tare da tabbatar da adalci a tsarin gudanar da haraji na Nijeriya.

"Ingantacciyar hanyar sadarwa da haɗin kan jama’a suna da muhimmanci wajen tabbatar da nasarar irin waɗannan sauye-sauyen tattalin arzikin.”

A cewar Idris, gwamnatin Shugaba Tinubu tana ci gaba da aiwatar da muhimman sauye-sauye domin ƙarfafa tara kuɗaɗen shiga, tabbatar da ɗorewar tattalin arziki da kuma bunƙasa cigaban ƙasa.

Ya ce: “Ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da jajircewa wajen gina tattalin arziki mai ƙarfi, mai ɗorewa kuma mai wadata ta hanyar muhimman sauye-sauye masu ma’ana.”

Ministan ya ce haraji yana taka muhimmiyar rawa wajen cigaban ƙasa ta hanyar samar wa gwamnati kuɗaɗen da ake amfani da su wajen bunƙasa ababen more rayuwa da kiwon lafiya da ilimi da sufuri da tsaro.

Sai dai ya jaddada cewa tsarin gudanar da haraji ba zai yi nasara ta hanyar tilastawa kawai ba, sai an gina shi bisa amincewar jama’a da gaskiya da adalci.

Ya ce: “Tsarin gudanar da haraji ba zai yi nasara ta hanyar tilastawa kawai ba. Dole ne ya samu goyon bayan jama’a tare da kasancewa bisa gaskiya da adalci da kuma ingantacciyar sadarwa.”

Idris ya bayyana cewa ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji wata muhimmiyar gada ce tsakanin masu biyan haraji da hukumomin haraji, domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya na samun damar gabatar da ƙorafe-ƙorafe cikin gaskiya da ƙwarewa.

Ya yaba da ƙaddamar da cibiyar karɓar kiran waya kyauta da kuma shafin gidan yana na hukumar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa sadarwa da samun bayanai da ayyuka.

“Ƙaddamar da cibiyar karɓar kiran waya kyauta tana nuna aniyar gwamnati ta kawar da matsalolin sadarwa tare da tabbatar da cewa ’yan Nijeriya za su iya neman bayanai da gabatar da tambayoyi da kuma warware ƙorafe-ƙorafen su ba tare da wata wahala ko ƙarin kuɗi ba.”

Ministan ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a kan haraji domin ƙarfafa biyan haraji da kuma inganta kishin ƙasa.

“Wayar da kai kan haraji ba wai don tara kuɗaɗen shiga kawai ba ne, don gina al’adar haɗin kan ƙasa da ɗaukar alhaki tare ne,” inji shi.

Ya yi gargaɗin cewa yaɗa labaran ƙarya da rashin ingantacciyar sadarwa suna hana sauye-sauyen gwamnati samun karɓuwa tare da haifar da rashin amincewa daga jama’a.

Ya ce: “Yaɗa labaran ƙarya da rashin isasshiyar sadarwa s**an haifar da rashin amincewa da kuma ƙin karɓar sauye-sauye. Wannan yana nuna muhimmancin amfani da kafafen yaɗa labarai yadda ya kamata da kuma ci gaba da wayar da kan jama’a.”

Ministan ya sake tabbatar da cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta ci gaba da tsare aiki tare da Ofishin Tax Ombud da sauran hukumomin da abin ya shafa domin wayar da kan jama’a kan sauye-sauyen haraji da haƙƙin masu biyan haraji da hanyoyin warware ƙorafe-ƙorafe.

Ya ƙara da cewa ingantacciyar sadarwa za ta taimaka wajen fahimtar rawar da haraji ke takawa wajen tallafa wa Ajandar Sabunta Fata da ci gaban ƙasa.

Ministan ya taya Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji murnar ƙaddamar da sabbin dandalan tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da haɗa kai domin gina tsarin haraji mai gaskiya da inganci wanda zai amsa buƙatun ’yan Nijeriya.

Taron ya samu halartar Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Mista Taiwo Oyedele; Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Didi Esther Walson-Jack; Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji, John C. Nwabueze; da sauran manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Kano