Angarar Bahaushe
Hausa, a matsayin yare ko kabila, sha-kundum ce!
A iya yin wata gidauniya ko kungiya domin bunkasa yare, al’adu da kabilar Hausa. Amma yin wani abu wai Kungiyar Hausawan Nigeria, ci baya ne ga Hausa da Hausawa. Musamman a matsayin kasa Nigeria ko Arewa inda Hausawa s**a fi kowa yawa da karfi.
Su kuma masu yiwa jama’a register da kokarin basu ID card na shaidar zama Hausawa, yan kasuwa ne kawai.
Hausa yare ne kuma kabila mai hadiye yaruka da kabilu ta yadda da dama daga wadanda ba Hausawa ba uslan, yanzu sun rikide sun zama Hausawa kuma suna alfahari da hakan. Duk da a zahiri hakan ci baya ga wadancan kabilun. A yanzu haka, Hausa ta kashe yaruka da dama.
Wannan ya bawa yaren wani irin tasiri fiye da sauran yarukun Afrika ta yamma. Saboda haka kayyade wannan kabila da yare mai albarka, da kokarin fitarda wasu daga cikinta abu ne wanda bana jin zai yiwu.
Daga Barr Abba Hikima
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Kano