Mujallar Wasanni
27/01/2025
Da dumi-dumi: Al Nassr ta fara tattaunawa domin daukar Victor Boniface daga Bayer Leverkusen.
Tattaunawa ta fara akan dan wasan na Najeriya, Al Nassr na aiki domin ganin ta dauki dan wasan da zai maye mata gurbin Anderson Talisca.
Al Nassr zata dauki babban dan wasan gaba wanda zai yi wasa a kusa da Cristiano Ronaldo. Yanzu sun fara tattaunawa akan Victor Boniface.
27/01/2025
Gabaki ɗaya wasanni guda 18 da za'a fafata a dare ɗaya 🤯
Watau ranar Laraba mai zuwa 🍿
Ƙarfe 9:00PM
Wani wasa kake fatan ganin yadda zai ƙarke?
Mujallar Wasanni
27/01/2025
Daga wata majiya tace Manchester United na duba yiwuwar kawo Victor Osimhen aro idan har zai zaije wata kungiya a wannan watan na janairu da aka bude musayar yan wasa.
Duk da kungiyarsa ta Napoli na sha'awar siyar dashi kai tsaye sai dai man utd bata bukatar siyansa kai tsaye sai dai aro.
Inda Napoli ta kara da Chelsea yunkurinta na kawo Alejandro Garnacho a wannan watan sai dai batayi nasarar hakan ba yayin ake sa ran Napoli zata bude tattaunawa da kungiyoyi akan yarjejeniyar Victor Osimhen a wannan watan.
26/11/2021
Mauricio Pochettino 'bai taba cewa zai bar' ba PSG, in ji Leonardo.
Mauricio Pochettino zai ci gaba da kasancewa a matsayin kocin Paris St-Germain kuma "bai taba cewa zai tafi ba" a yayin da ake rade-radin zai tafi Manchester United, in ji daraktan wasanni na kungiyar Leonardo.
Kwangilar Pochettinoa PSG za ta kare a a shekarar 2023,
"Ba ma son Pochettino ya tafi," in ji Leonardo.
"Bai taba cewa zai bar kulob din ba kuma babu kulob din da ya tuntube mu."
Leonado ya kuma ba su tuntubi Zinadine Zidane ba domin zama koci a PSG.
Manchester United na gab da daukar koci dan kasar Jamus Ralf Rangnick a matsayin.
United ta mayar da hankali wajen daukar kocin rikon kwarya domin maye gurbin Solskjaer, wanda aka kora daga aiki ranar Lahadi bayan sun sha kashi a hannun Watford da ci 4-1 a gasar Firimiya.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kwanar Dala Road
Kano