Aminchi Tv
31/05/2026
Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, ya bukaci tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, da kada ya amince da tikitin takarar shugaban ƙasa da wani ɓangare na jam’iyyar PDP ya ba shi domin zaɓen 2027.
Keyamo ya ce wannan ɓangaren jam’iyyar ba ya da sahalewar hukumomin da s**a dace, yana mai gargadin cewa amincewa da irin wannan tikiti na iya haifar da ruɗani da ce-ce-ku-ce a harkokin siyasa.
31/05/2026
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana cewa Rabiu Musa Kwankwaso ba zai zama mai kallo a gefe ba idan s**a samu nasara a zaɓen 2027.
Obi ya ce mataimakin shugaban ƙasa zai kasance muhimmin abokin aiki a tafiyar da mulki da yanke manyan shawarwari, domin tabbatar da haɗin kai da ingantaccen shugabanci a ƙasar nan.
31/05/2026
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta sanar da k**a harsasai 380 na bindigogin soja a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, tare da miƙa wanda ake zargi da kayayyakin da aka k**a ga hukumomin tsaro domin ci gaba da bincike.
A cewar hukumar, jami’an ta sun k**a wani mutum mai suna Sunusi Musa mai shekaru 30 a yankin Jere da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar 24 ga Mayu, 2026, kuma ana zargin sa da ɗaukar harsasan zuwa jihar Katsina.
Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cewa harsasan da aka k**a nau'in 7.62mm ne, waɗanda ake amfani da su a bindigun sojoji.
Ya ce wannan nasarar na daga cikin ƙoƙarin hukumomin tsaro na dakile yaduwar mak**ai da harsasai ba bisa ka’ida ba.
A wani samame daban a jihar Kaduna, jami’an NDLEA sun k**a wasu ma’aurata, Musa Sunday da Mercy Sunday, tare da wani mutum mai suna Salomi Ezekiel bayan sun kwace buhuna 100 na tabar wiwi masu nauyin kilogram 1,246 a yankin Gonin Gora.
31/05/2026
Gwamnatin Ostiraliya ta amince da sayen jiragen ruwa na yaki masu amfani da mak**ashin nukiliya guda uku da aka riga aka yi amfani da su, a karkashin sabuwar yarjejeniyar tsaro ta AUKUS da ke tsakaninta da Amurka da Birtaniya.
A tsarin farko na yarjejeniyar, an tsara cewa Ostiraliya za ta karɓi jirgi biyu da aka yi amfani da su daga Amurka, sannan kuma ta samu guda ɗaya sabo daga nau’in Virginia-class. Sai dai sabon tsari da aka yi wa kwaskwarima yanzu ya sauya wannan shiri, inda aka fi karkata ga sayen jiragen da aka riga aka yi amfani da su.
Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa tsaron yankin Indo-Pacific, tare da ci gaba da haɗin gwiwar soji tsakanin ƙasashen uku domin daidaita ƙarfin tsaro a yankin.
31/05/2026
Gwamnatin Norway ta bayyana cewa ta yi wa Malaysia uzuri dangane da matakin da ta dauka na soke lasisin fitar da makami na Naval Strike Missile (NSM) da aka shirya kai wa rundunar sojin ruwan Malaysia. Sai dai ta jaddada cewa har yanzu tana kan matsayinta na dakatar da yarjejeniyar.
Ministan Tsaron Malaysia, Mohamed Khaled Nordin, ya bayyana cewa Oslo ta yi bayanin dalilan da s**a sa ta soke lasisin fitar da mak**an, inda ta ce matakin ya samo asali ne daga sabon tsauraran dokokin fitar da wasu fasahohin mak**ai masu matukar muhimmanci.
A cewar rahotanni, an riga an biya kusan kashi 95 cikin 100 na kudin yarjejeniyar tun kafin a dakatar da ita, lamarin da ya jawo cece-kuce da kuma matukar damuwa a Malaysia, musamman ganin cewa mak**an na da muhimmiyar rawa a shirin sabunta sojojin ruwan kasar.
Malaysia na ci gaba da nuna rashin amincewa da wannan mataki, tare da nazarin yiwuwar neman diyya ko daukar matakin shari’a kan lamarin.
A nata bangaren, Norway ta ce matakin ya shafi tsare-tsaren tsaro ne da kuma takaita fitar da fasahohin mak**ai zuwa wasu kasashe, tare da jaddada cewa tana son ci gaba da kyakkyawar dangantaka da Malaysia duk da wannan sabani.
Shin kuna ganin ya dace ƙasa ta soke yarjejeniyar mak**ai bayan an kusa kammala biyan kuɗi, ko kuwa hakan rashin adalci ne ga ƙasa mai saye?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano