Akcccosa 2018 Chapter

Akcccosa 2018 Chapter

Share

20/02/2024

Ɗaya daga cikin Manyan dalilan da suke ƙara rura wutar hauhawar farashi shine yayatawa da zuzutawa. Bad news travel fast kuma suna da negative effect. Idan an rage yaɗawa sai a ragewa mummunan labarin kaifi. Idan farashin abu ya tashi ana tallatawa amma idan ya sauka sai a yi gum. Saboda: إِنَّ الْإِنسَانَ خُلِقَ هَلُوعًا
إِذَا مَسَّهُ الشَّرُّ جَزُوعًا
وَإِذَا مَسَّهُ الْخَيْرُ مَنُوعًا
Kuma:
وَأَمَّا الْإِنسَانُ إِذَا مَا ابْتَلَاهُ رَبُّهُ فَأَكْرَمَهُ وَنَعَّمَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَكْرَمَنِ
وَأَمَّا إِذَا مَا ابْتَلَاهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَهَانَنِ
كَلَّا ۖ بَل لَّا تُكْرِمُونَ الْيَتِيمَ
وَلَا تَحَاضُّونَ عَلَىٰ طَعَامِ الْمِسْكِين

Wanda bai taɓa ta'ammali da Dollar ba sai kaga yana posting ɗin price update idan ya hau, ko a tunanin sa hakan alfanun mai zai haifo? Oho! Shi yasa abun yake ƙara ta'azzara, ana ƙara shiga ruɗani, shi kuma ruɗani ko tsoro yana ƙarawa abinda ake ciki ƙarfi ne.

Idan farashi ya ƙaru akwai wa'yanda deep down they are happy saboda sadistic nature ɗin son ganin al'umma a wahala tunda suma suna ciki kuma sun saba da wahala tun can, "ai mutuwar yawa kaka ce" ko kuma suna da kaya a ƙasa. Shi yasa idan farashi yayi sama sune kan gaba wajen yayatawa cikin salon farin ciki da dariya kuma su ƙara farashi nan take! Amma idan yayi ƙasa sai su yi gum kuma ba zasu saukar da farashin kaya ba. This is not funny, the situation we are in this country is not funny and laughable at all.

Tsoro da complain sun zama dole dan yanayin ba daɗi kuma shi complain idan an yi shi yana rage raɗaɗi saidai a yi ƙoƙari ayi controlling ɗin yawan yinsa kuma a rage, saboda idan ana yi da yawa ana ƙara kambama abun ne. And remember you attract what you fear too.

Ƙasashen da s**a ci gaba ma sun yi facing abinda ya fi wannan kuma sun wuce wurin A China an taɓa yunwar da har gawarwaki an ci, a 1944 1 Yuan daidai yake da 1 Dollar a ƙasar amma kafin 1947 (span of 3 years) sai ka sa Yuan 12,000 zaka siyi 1 American Dollar. A America lokacin "Great Depression" mutane har ƴaƴan su sun siyar. Muma zamu fita daga wannan yanayin idan muka yi aiki tuƙuru In Sha Allah ba tare da mun kai nan ba. Mu yi ta nema ba k**a ƙafar yaro. Sannan Kada mu manta da taimakon juna da sadaka, duk rintsi ka taimaki wanda ka fi haka zalika kada mu manta da addu'a.

Masu riƙe da madafun iko su ji tsoron Allah su duba halin da al'umma take ciki su yi abinda ya k**ata. Yan kasuwa an san suna ƙoƙari kuma su ci-gaba da rangwantawa masu siye su ci-gaba da nema kuma su yi uzuri ga masu siyar wa. Mu ci-gaba da juriya, tsimi, tanadi da kuma dabarun da zasu cire mu cikin wannan yanayi kuma mu amfana da lessons ɗin da yazo kuma zai zo da su.

Aliyu Ibrahim Haidar

Photos from Akcccosa 2018 Chapter's post 29/01/2022

A new Computer geek in the family. We can add BSc. to his name. Yusuf Musa Lameen (Liman) Has successfully completed his BSc. In computer science. May Allah bless the knowledge to be useful to him and to humanity.

20/12/2021

Alhamdulillahi Allah ya sauki Asiya Abdullahi Kantudu lafiya. Allah ya raya bisa tafarkin annabi🙏 Yan KCC sai girma suke

Want your school to be the top-listed School/college in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


P. M. P 3117 Aminu Kano Way
Kano