Engineer lawi technology

Engineer lawi technology

Share

17/12/2023

Nima nabi sahun su Dr salisu abdulrazak sahell inayin mining na Avive, idan kashirya a samu wannan Alkhairin dakai kaima a duniyar crypto zaka iya bin wannan link din dake kasa kayi register..👇

https://m.avive.world/register/?vcode=s7quzk

Ba kudi zaka saka ba, kawai bude data zakayi kayi mining, kullun ka bude kayi Claiming wanda baifi second 10 ba kayi kagama, a haka zaka tara abinda zai baka mamaki, ana launching nasa, zakaga abun k**ar mafarki..

Allah ya bada sa'a..

19/11/2023

Na ɗauki tsawon lokaci ina bincike game da kamfanonin da ake siyar Data, amma har yanzu ban yi nasarar samo kamfanin da ake siyar da Data mai rahusa a farashi mai sauƙi ba sama da kamfanin Salfat Data ba.

Za ku iya Rigister da Kamfanin Salfat Data ta wannan link da ke ƙasa domin cin moriyar Data a farashi mai sauƙi👇👇

https://salfat.com.ng/user/signup?ref=engrlawi

Sannan bayan ka yi Rijista ta wannan link da ke sama🖕nan take za ka iya garzayawa playstore domin sauke shi a wayarka.

Dr Salisu Abdurrazak Saheel Muna godia kwarai da wannan damar aka bawa al'uma

22/10/2023

Internet baiwar Allah ta bakin Malam Albani zaria (Allah ya gafarta mashi)..

Yanzu misali kanaso kayi waya da abokinka da yake zaune jahar kano, kai kuma kana zaune kaduna, daga lokacin da ka danna lambar wayarsa ka kuma danna alamar kira, daga wannan lokacin wayarka zata tura signal zuwa ga network provider naka (MTN, Airtel, 9mobile ko Glo) ko wane kalan layi kake amfani dashi, wannan signal din zata sanar da network provider naka cewa kanaso kayi magana da abokinka, sai network providers naka su fara kokarin ganin sun hadaka dashi ta hanya mai kyau, daga wannan lokacin wayar abokinka zatayi Ringing, yana picking kafin kuji muryar juna sai wayar shi itama ta tura ma Network provider da yake amfani dasu cewa ka kira shi yanaso yayi picking.

Wadannan Signals din da suke zuwa wurin Network Providers domin sanar dasu cewa kunason zakuyi waya da juna suna kai wannan sakon ne ta hanyar Network Infrastructure irinsu cell towers da cables.

Daganan sai network provider su tura maku signal na amincewar kuyi magana da junanku kuji muryoyin juna.

Duka wannan process din yana faruwa ne very quickly, da matikar sauri, wannan fasahar itace ake kira da telecommunications, wanda a cikin wannan fasahar akwai abubuwa masu tarin yawa na ban mamaki.

Allah ya kara mana ilimi mai amfani..🙏

©(Dr) Salisu Abdurrazak Saheel

21/10/2023

Abubuwan da za'a iyayi da BVN naka idan wani ya samu..

Kamar yadda muka sani Bank Verification Number wato BVN, lambobi ne guda 11 da suke amfani wurin Identification a bankunan mu a Nigeria, domin tabbatar da asalin mai amfani da asusun banki.

Kamar yadda nasha fada cewa samun BVN naka kadai bazai wadatar ba wurin yi maka kutse a asusun ajiyarka ba, sai dai akwai wasu abubuwa da za'a iyayi dashi idan wani ya sansu.

1. Identity Verification: Bankuna da sauran financial institutions zasu iya amfani da BVN naka wurin verifying na identity naka domin tabbatar da wanda suke hulda dashi ko zasuyi hulda dashi musamman idan ka cike wani form na neman bashi ko domin yin wani transactions.

2. Account Linking: da BVN dinka wani zai iya amfani dashi wurin hadashi da asusun bankuna da yawa, amma wannan yana matikar wahala idan ba mutum yakai babban kwaro ba, kuma duk da haka sai da amincewar bankuna.

3. Fraudulent Activities: a wani bangaren kuma za'a iya samun wasu bata gari da zasu iya amfani da BVN naka wurin gudanar da ayyuka mararsa kyau wurin saka BVN dinka a matsayin Identity nasu ko yin yunkurin kutsawa a wani wuri tareda amfani da BVN naka. Amma duk da haka bankuna sunada tsaro sosai a wannan bangaren, shiyasa ba yadda za'ayi ayi maka sata da BVN naka batareda sanin banki ba.

Allah ya kyauta..🙏

©(Dr) Salisu Abdurrazak Saheel

10/09/2023

Idan Scammers ko Hac-kers s**a mallaki Account Number naka akwai wasu hanyoyi guda 4 da zasu iya bi wurin yunƙurin kwashe maka kuɗi:

1. Social engineering attempts: Ta wannan hanyar hac-ker zai iya amfani da Account number naka wurin ƙoƙarin samun information naka daga wurinka ko daga wurin wasu makusantanka, misali: za iya kiranka a waya ya karanto maka Account Number naka daga farko har ƙarshe, sannan yace maka daga bankinka yake, dan haka yana buƙatar login credentials naka da wasu personal details, da duk wasu sensitive information naka na banki, da niyar cewa za'ayi maka wani gyara ne, kai kuma saboda ya karanto account number naka hakan sai yasa ka amince dashi kuma katura mashi.

Kai tsaye zaiyi amfani da wannan damar ya kwashe komai acikin asusun naka.

Note: Duk wanda ya kiraka a waya ya karanto maka Account Number naka yace maka ka bashi wani Login credentials naka, ka kashe wayarka kawai. idan banki s**a kiraka ce maka zasuyi kaje banki ayi maka duk abinda za'ayi maka acen.

2. Phishing attacks: Idan Hac-ker ya mallaki account number naka, zai iya amfani da wannan damar musamman idan yanada Email naka ko Phone number sai ya tura maka phishing emails ko message mai ɗauke da malicious links wanda kana danna shi zai kaika fake websites nashi mai k**a da Exactly irin bankin da ka buɗe, yace maka ka cike personal information naka na banki zaka samu kyautar 100k daga banki.
kana sakawa shikenan bayananka zasu tafi kai tsaye zuwa gareshi zai iya kwashe ko nawa ne a account naka.

Note: Duk wani Email da za'a turo maka tareda wani Links ka tsaya ka natsu sosai ka duba kaga wanene sender ɗin, kuma ka tabbatar address ɗin na gaske ne.

3. Account verification attempts: Akwai websites ɗin da ake amfani da account number wurin yin verification process na canza information naka na banki, hac-ker zai iya canza password naka da sauran details naka ta waɗannan websites ɗin ta hanyar contacting customer service na bankin naka su kuma zasuyi duk abinda hac-ker ɗin ya buƙace su suyi domin duk a tunaninsu kaine.

Note: Karka biyo ni Inbox kace na faɗa maka Websites ɗin koda wasa bazan faɗa ba.
a kula sosai a duk sanda aka turo maka wani Verification code karka sake wani ya kiraka yace katura mashi.

4. Limited financial transactions: Idan Hac-ker ya samu Account Number naka da kuma wasu information naka irinsu sunanka, address naka, phone number, Sim ɗinka, da BVN, to hac-ker zai iyayin yunƙurin yin Transaction na kuɗi daga bankinka wurin yin siyayya a online, transfer na kuɗi zuwa wani account daban da saka katin waya.

Note: Mu kiyaye sensitive information namu ba kowa zaka bari yasan information naka na banki ba saboda tsaro.

A ƙarshe ina cewa, waɗannan hanyoyin guda 4 sune kaɗai hanyoyin da nasani da hac-ker zai iyayi yunƙurin kwashe maka kuɗi kuma ba lallai yayi nasara ba sai ya samu cikakken goyon bayanka, ko kuma cikakken sakakinka, Mu kula sosai mu dinga sanya strong password, unique passwords, da sanya tsarin two-factor authentication ga accounts namu domin tsare kawunanmu daga faɗawa hannun azzalumai..

Ayi sharing ma sauran yan'uwa..

Allah Yataimaka..🙏

©Salisu Abdurrazak Saheel

Want your business to be the top-listed Media Company in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Kano