DAN MANYA
13/12/2025
*SUNNONI GUDA TAKWAS(8) DA IN A KA BARSU A SALLAH ZA A YI SUJADAR RAFKANUWA*
1- Karatun surah(wacce a ke yi bayan an karanta fatiha).
2-Sirranta karatu a in da a ke sirrantawa ko bayyana karatu a in da a ke bayyanawa.
3-FaÉ—in: "Sami'allahu liman hamidahu", (in a ka barshi sau biyu).
4-Kabbara(ban da ta harama), in a ka bar guda biyu zuwa sama.
5-Tahiyyar farko.
6-Zama domin tahiyyar farko
7-Tahiyyar karshe
8-Zama domin tahiyyar karshe
Idan mai sallah ya bar wani abu cikin ababen da a ka lissafa a sama zai yi sujuda biyu kafin sallama(ƘABLIY).
Wanda ya bayyana karatu a in da a ke sirrantawa zai yi sujuda biyu bayan sallama(Ba'adiy)
Wanda ya sirranta karatu a in da a ke bayyanawa zai yi sujada biyu kafin sallama(Ƙabliy).
Madogara:
ترقيع الصلاة- سجود السهو على المذهب المالكي(39) و-المقدمة العزية للجماعة الأزهرية (105-104)
13/12/2025
*Manzon Allah ï·º yace: Idan ka aikata mummunan aiki, ka biye bayansa da kyakkyawa, zai goge shi. Ahmad ya ruwaito.*
Allah yasa mudace
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Kutama
Kano