Yan Pi Network

Yan Pi Network

Share

16/03/2025

America sun zama masu faɗa aji da gindaya dokoki wanda dole sai kabi indai kanaso ka zauna lafiya a duniya, Kuma sun tara kuɗaɗe masu yawan da s**a gina ƙasarsu ta yadda duk talaucinka zakai rayuwa mai ƙyau saboda tsarin yana taimaka maka.

A gefe guda kuma ga uban bashi har na doller trillion 34 zuwa 35 ana binsu, Kuma har yanzu basu daina karɓa ba koma ajikin su dan ana hasashen nan da 2030 bashin zai iya kaiwa doller triliyan 45 indai basu daina karba ba, wanda ake tunanin indai s**aci gaba da tafiya a haka nan gaba komai saiya dagule musu tun daga kan harakar Security, Lafiya, da Ilimi na kasar duk ba lallai a iya ci gaba da gudanar dasu ba.

Tambaya; su waye suke bawa kasar america bashi da har yakai wannan adadin? Kuma me yasa suke karɓa.

Amsa; gwamnatin ƙasar tana kashe mahaukatan kuɗi don ingantawa ƴan ƙasarta rayuwa fiye da abinda take karɓa daga hannunsu na haraji wato "TAX" sannan tana amfani da wani bangare na bashin don shiga siyasar wata ƙasa da daure wa ta'addanci da iskanci gindi, Amma yawanci tana ciyo bashi ne don cike gibin inganta rayuwar yan ƙasa da daidaita tattalin arzikin ta hanyar ansa daga manyan kamfanunuwa na ƙasar da bankuna ƙarƙashin tsarin (Govenment IOUs) da s**a tsara.

Ana hasashen OVER 75% na kuɗin da ake bin gwamnatin ƙasar america na bankuna da kamfanonin ƙasar ne da kuma asusun ƴan fansho da kuɗin masu saka hannun jari a ƙasar, Sai kuma sauran sana ciyowa daga manyan ƙasashen duniya da kasuwanci da siyasa yake haɗasu dasu k**ar england, japan, chaina, da sauransu.

Tambaya su masu bawa america bashi ba suda hankali ne da zasuci gaba da basu? Amsa; Sun gama kashe musu zuciya ne akan ƙara musu kudin ruwa da sukeyi shiyasa ba zasu daina basu ba, Kai daga cikin wanda america take cin bashin su ta zauna lafiya hadda

(FRS) "federal reserve system" babban bankin ajjiyar kudi na duniya.

Tayaya zasu iya biyan wannan bashin?
Kuma tunda suna da lasisin buga doller su kashe ta a ƙasar da suke so ba tare da sunyi barking ɗinta da komai ba, meyasa ba zasuyi printing adadin da suke so ba su biya kowa kuɗinsa kawai su huta.

Amsa; Zasu iya mana idan s**aga dama, amma hakan zai jawo mummunan "inflation" a duniya kuɗaɗe da yawa zasu rasa value ta yadda ko wace ƙasa saita sake yiwa tattalin arzikin ƙasar ta garambawul, ita kanta doller saita rasa value ɗinta hakan yasa dan dole s**a hakura sakaci gaba da karɓar bashi don dai daita tattalin arzikinsu.

Dan yanzu haka ma madadin suci gaba da buga doller janyeta sukeyi a hankali suna rage mata yawa, Saboda dama daɗe da fahimtar lokaci yana nan zuwa da zasu daina bautar da mutane da doller.

Wannan shine babban dalilin da yasa s**a fara shirya "Plan B" tun daga kan bitgold zuwa bitcoin da pi network.

Want your business to be the top-listed Computer & Electronics Service in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address


N0_590 Dantata By Kabuga Street
Kano