Juma concept
18/11/2025
Da Dumi-Dumi: An ji ƙarar harbe-harbe a shelkwatar PDP
A yanzu haka ana cikin ɗar-ɗar a shelkwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja kan yunkurin gudanar da taruka biyu daban-daban a lokaci guda.
Kwamitin Zartarwa na Kasa (NWC) da aka zaba a Ibadan, fadar jihar Oyo, da kuma bangaren da ministan Abuja, Nyesom Wike, ke goyon baya, duka sun tsara gudanar da taruka a yau.
Sakataren jam’iyya na kasa na bangaren Wike, Samuel Anyanwu, ya isa Wadata Plaza tare da wasu mambobin bangaren nasa.
Bayan dan lokaci, mambobin bangaren Taminu Turaki suma sun isa hedkwatar amma aka hana su shiga.
Sai dai gwamnonin jihohi biyu sun tilasta shiga, amma lokacin da sauran mambobin bangaren s**a yi kokarin shiga, jami’an tsaro s**a harba bindiga tare da sakin hayakin barkewa domin tarwatsa su.
lamarin ya haifar da rudani inda mutane s**a ruga neman tsira.
Yayin da yake jawabi ga 'yan jarida a ofishinsa kafin zuwan bangaren na biyu, Anyanwu ya ce karuwar tsaro al’ada ce domin hana tashin hankali da rikici.
18/11/2025
YANZU-YANZU: Kakakin Majalisar Jihar Taraba Hadi Da Wasu Daga Cikin ’Yan Majalisar Jam'iyyar PDP Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC A Hukumance
31/10/2025
Natasha Ta Gayyaci Akpabio Zuwa Bikin Kaddamar da Ayyuka a Kogi
Dangantaka tsakanin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan (PDP, Kogi ta Tsakiya) da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ta fara samun sauƙi bayan Akpoti-Uduaghan ta aika da gayyata ga Akpabio domin halartar bikin kaddamar da ayyuka a yankinta.
Gayyatar, wacce aka rubuta da hannunta, ta kuma haɗa da sauran sanatoci, kuma an karanta ta a zauren majalisar yayin zaman ranar Alhamis da Akpabio kansa ya karanta.
A cewar wasikar, bikin zai gudana ne a ranar Lahadi a Ihima, Jihar Kogi, domin bikin cika shekaru biyu da Akpoti-Uduaghan ta yi a majalisar dattawa.
“A yayin bikin cika shekaru biyu a matsayin Sanata mai wakiltar al’ummata, ina gayyatar sanatoci abokaina da su zo bikin kaddamar da ayyuka a Jihar Kogi,” in ji wasikar.
An bayyana Plot 101, Jimoh Akpoti Street, Ihima, Okene a matsayin wurin taro, inda aka ba da shawarar cewa sanatocin da ke tafiya ta jirgi su sauka a Obajana Airstrip kafin su ci gaba zuwa Ihima ta hanya.
Bayan karanta gayyatar, Akpabio ya taya ta murna a gaba da kowa da cewa:
“Ina taya ki murna a gaba.”
Wannan mataki na nuna sabon yanayi na sulhu bayan rikicin da ya barke a watan Fabrairu kan rabon kujeru a majalisar, wanda ya jawo dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida daga aiki a ranar 6 ga Maris.
Tun bayan dawowarta a ranar 24 ga Satumba, Sanatar ta fara sake shiga hulɗa da Akpabio a zauren majalisa, ciki har da bayar da gudunmawa a muhawara da dokoki. Amma wannan gayyatar ce ta fi nuna mataki kai tsaye na sulhu da shugabancin majalisar.
31/10/2025
HOTUNA: Yanda dandazon ɗaruruwan sojoji su ka yi wa Janar Christopher Musa rakiya yayin bankwana da barikin soja na Mogadishu Cantonment wanda ke unguwar Asokoro a Abuja bayan rantsar da sabon Babban Hafsan Hafsoshin tsaron Najeriya a jiya Alhamis.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Zoo Road Kano
Kano
8000