Akafsan Channel
AKAFSAN is an organization of intellectuals whose activities, engagements and responsibilities are mainly dedicated toward Promotion of Peace, Unity and Academic Excellence. As such, members of the association are required to be the good ambassadors, and do the needful actions for realization of the AKAFSAN vision.
22/04/2026
AN DAWO DA SHEIKH ABDULJABBAR KANO BISA UMARNIN KOTU - Laraba, 22 ga Afrilu, 2026.
A ƙoƙarin ci gaba da sauraron shari’ar babban Malamin Addinin Musuluncin nan (Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara), yau Laraba 22/04/2026 an dawo da shehin Malamin Jihar Kano, bayan umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara (Court of Appeal) mai zamanta a Sakatariyar Audu Bako, a Kano ta bayar.
Matakin ya biyo bayan tsarin shari’a da ke gudana tsakanin malamin addinin da Gwamnatin Jihar Kano, inda kotun ta amince da ci gaba da shari’ar bayan wani lokaci na duba ƙorafe-ƙorafe da aka gabatar a gabanta.
Masu lura da al’amura sun bayyana cewa dawowar shari’ar na nuna wani muhimmin mataki a cikin wannan lamari, wanda ya jawo hankalin jama’a a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.
Ana sa ran zaman kotu na gaba zai ƙara fayyace muhimman batutuwan shari’a tare da tsara matakan da za a bi a gaba.
A dakace mu zuwa gobe, muna tafe da rahoton zaman shari'ar Inshaa Allahu ta'ala.
SHAWARA:
Masu neman ayi adalci a Shari’ar Malam Abduljabbar, a maida hankali wurin yin addu'o'i da neman taimakon Allah.
07/04/2026
SABON RAHOTO: KAN SHARI’AR SHEIKH ABDULJABBAR KABARA
Sheikh Abduljabbar Ya Miƙa Sabuwar Buƙata Zuwa Kotun Daukaka Kara a Kano...
Fitaccen malamin addinin Musulunci a birnin Kano, Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara, wanda ke tsare a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, ya sake gabatar da wata sabuwar takardar ƙorafi a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kano.
Rahotanni sun nuna cewa malamin ya ɗauki wannan mataki ne bayan wani sako da ya bayyana cewa ya samu ta wayar tarho daga Shugaban Sashin Shari’a (H.O.D Litigation) na kotun a ranar 31 ga watan Maris, 2026, wanda ya kunshi sanarwar cewa za a aiko masa da takardar sanarwar ranar zaman kotu.
CIKAKKEN BAYANAI KAN TAKARDAR ƘORAFIN:
A cikin takardar ƙorafin mai shafuka biyar, wadda aka gabatar wa kotun a ranar Talata, 7 ga Afrilu, 2026, ta hannun wakilan kwamitin shaidunsa, malamin ya nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da shari’arsa.
Daga cikin muhimman batutuwan da ya gabatar sun hada da:
1. Sauya Masa Wurin Tsarewa: Malamin Ya koka kan yadda aka sauya masa wurin tsarewa daga gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano zuwa Kuje a Abuja tun ranar 14 ga Oktoba, 2025, ba tare da ba shi damar ɗaukar muhimman takardunsa na shari’a ba.
2. Batun Takardun Shari’a: Sheikh Abduljabbar Ya bayyana cewa tsawon watanni biyar bai samu cikakken bayani kan halin da takardunsa suke ciki ba, tare da zargin cewa ba a ba shi damar tantance su ba kafin sauya masa Matsuguni.
3. Ƴancin Kare Kai: Malamin ya jingina buƙatarsa da tanadin Sashe na 36 (6) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), yana mai neman a ba shi damar kare kansa da kansa a gaban kotu.
MANYAN BUƘATUN DA AKA GABATAR:
A cikin korafin, Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara ya roƙi kotun da ta yi la’akari da waɗannan buƙatu kafin a ci gaba da sauraron karar:
1. A mayar da shi zuwa gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano domin ya duba halin da takardunsa suke ciki.
2. A ba shi damar sake tsara ko mayar da duk wasu takardu idan aka samu sun bace ko an sauya su.
3. A dakata da ci gaba da shari’a har sai ya tabbatar da sahihancin takardunsa, tare da karɓar cikakkiyar sanarwar ranar zaman kotu da kuma takardar izini na halarta domin gabatar da hujjojinsa.
KAMMALAWA:
Malamin ya jaddada cewa tun bayan tsare shi da akayi a ranar 16 ga Yuli, 2021, bai aikata wani laifi ba, inda ya roƙi kotu da ta yi masa adalci wajen duba bukatunsa.
Zuwo lokacin kammala wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga kotun dangane da wannan sabon korafi.
SOURCE:
https://www.facebook.com/share/p/1CYVL5H6xQ/
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the organization
Telephone
Website
Address
Gwale
Kano
700103