Arewa Hausa Online
31/07/2024
Leda Tana Daya Daga Cikin Abinda Ke Janyo Ambaliyar Ruwa a Najeriya inji Hajiya Zubaida Umar
Daga Bello Ahmadu Alkammawa
Ganin damina ta fadi a mafi yawancin jihohin dake Najeriya, Hukumar Ba Da Agajin Gaggawa Da Kiyaye Aukuwar Annoba Ta Kasa karkashin jagorancin Hajiya Zubaida Umar ta dauri damarar fuskantar kowacce irin barazana da matsalolin ambaliyar ruwa zai kawo a kasar, ta hanyoyin wayar da kan al'umma domin su ba da ta su gudumuwa ta hanyar yashe magudanar ruwa da kuma sanya idanu sosai wajen ganin yara da sauran mutanen dake unguwanni da karkara da kuma birane sun daina jefa ledodi a magudanar ruwa saboda yin hakan yana daya daga cikin abubuwan dake janyo ambaliyar ruwa a kasarnan.
Da take tattauna da Sashen Hausa na Gidan Rediyon BBC Landan, Hajiya Zubaida ta bayyana cewa ana hasashen cewa Jihohi 33 da Kanannan Hukumomi 135 ne za su fuskanci ambaliyar ruwa a wannan shekara da mu ke ciki. Ta bayyana cewa duk da yake ba dukkanin jihohin dake Najeriya su ke da ofisoshin hukumar ba, wannan bai hana mutane su kasance cikin shirin ta kwana musamman wuraren da s**a saba da wannan matsalar kowacce shekara, ta kuma nemi ofisoshin hukumar na jihohi da su kasance cikin shiri domin fuskantar matsalar idan ta taso ka da su yi kasa a gwiwa har sai matsalar ta riske su. Ta bayyana cewa aikin hukumar ya hada da tallafawa da kuma wayar da kawunan al'umma dangane da matsalolin ambaliyar ruwa da mak**antan haka.
Gimbiyar ta Mutanen Gwandu ta bayyana cewa tuni Hukumar ta sadu da hukomin Sojojin Ruwa da 'Yan Sandan Ruwa tare da dukkanin ofisoshin hukumar dake jihohin kasarnan inda kowa a yanzu yasan muhimmiyar rawar da zai taka domin samun nasarori akan wannan matsalar da take tafe.
"Muna karbar rahotanni daga jihohin dake da ofisoshin hukumar kowacce rana domin sanin halin da su ke ciki domin sanin irin yadda za mu mayar da su tarihi Insha Allah, bugu da kari yanzu haka muna rike da rahoton hukumomin yanayi da hasashen ambaliyar ruwa saboda haka, musan aikin dake gaban mu, muna kuma cikin shirin ta kwana domin da taimakon Allah mu mayar da matsalar tarihi", inji ta.
Domin sanin halin da su wadannan jihohi da ake hasashen za su samu Iftala'in ruwan sama a wannan shekarar su ke ciki tuni ita da jami'an ta s**a ziyarce su, hasalima sun zagaye dukkanin jihohin kasarnan inda a kowacce jiha s**a sadu da gwamnoni da sarakuna domin su wayar da kawunan al'umma dangane wannan matsalar da hanyoyin da za a bi ta zo da sauki daya daga cikin su itace daina zuba shara a magudanar ruwa, tare da kaucewa sanya ledodi wadanda ke toshe hanyoyin ruwa. Ta kuma sadu da masu sarafa jiragen Kwale-kwale da kamun kifi da dukkanin wanda ke da rawar da zai taka domin kawowa mutane daukin da ya dace domin ganin a kawar da matsalar cikin sauki ta hanyar kaiwa wadanda matsalar ta shafa agaji cikin lokaci. Yanzu haka motocin hukumar dake jihohi a cikin shiri su ke, hasalima hukumar ta samar da rigunan ruwa da sauran kayayyakin da ake nema na agaji a dukkanin jihohin kasarnan musamman inda ake da tunanin afkuwar matsalar.
Gimbiyar ta Mutanen Gwandu ta bayyana cewa tana kokari sosai tare da taimakon Allah wajen ganin ayyukan hukumar a karkashin jagorancin ta sun samar da canje-canjen da za su mayar da matsalolin ambaliyar ruwa da taimakon gaggawa ga mutane tarihi ta hanyar ba da cikakkiyar kulawa ta musamman a kowanne lokaci ba sai a lokacin damina ba, domin ganin wadanda matsalar ta rutsa da su ba su dauki dogon lokaci ba, a sansani da ake samarwa domin fakewa kafin a ciwo kan matsalar ba.
Hajiya Zubaida Umar ta nemi mutanen kasar da su hada hannu da ofisoshin hukumar dake jihohin su wajen kai rahoton da zai taimaka a samu bakin zaren matsalolin ambaliyar ruwa da mak**antan haka idan sun taso cikin sauki.
Alkammawa ya rubuta daga Titin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Kaduna Numbar Salula 07030399110
08/07/2024
Mun Nemi A Yi Binciken Gwamnatin El-Rufa’i A Bainar Jama’a, Majalisar Kaduna Ta Ki – Tsohon Kwamishina •An Ce Mun Ce Alhali Ba Mu Ce Ba A Rahoton Majalisar •A Tarihin Kaduna Ba A Taba Samun Kundin Mika Mulki Irin Na El-Rufai Ba •Masu Kitsa Rikicin Siyasar Sun Boye Fuskokinsu Tsohon kwamishina a gwamnatin Malam Nasiru el-Rufai, ALHAJI JAFARU SANI, da aka dama da shi har tsawon shekaru takwas shi...
06/07/2024
An Nada Malam Ibrahim Rilwan Mohd A Matsayin Sabon Garkuwan Matasan Arewa Daga SHEHU YAHAYA Kungiyar Dalibban Najeriya da hadin gwiwar Kungiyar Matasan Arewa a yau sunyi wani gangami domin karrama Malam Ibrahim Rilwan Mohammed Shugaban Gidauniyar IRM dake Abuja. Taron ya…
04/05/2024
Ƙungiyar 'Yan Jarida Ta Nada Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Kaduma Muqamin Uban Kungiya
Daga SHEHU YAHAYA
Kungiyar wakilan gidajen jaridu na ƙasa reshen jihar Kaduna (Correspondents Chapel) ta naɗa shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Alhaji Sani Liman Kila a matsayin uban Ƙungiyar.
Da yake jawabi a wajen taron nadin da ya gudana a ofishin Shugaban ma'aikatan a fadar gwamnatin jihar Kaduna, shugaban kungiyar wakilan 'Yan Jaridar Alhaji Abdulghaffar Alabelewa yace la'akari da irin kauna da gudummuwa da Sani Kila ke ba 'yan jarida a faɗin jihar ne ya sa kungiyar ta karrama shi da mukamin uban Ƙungiyar.
Shugaban 'yan jaridar ya ƙara da cewar 'yan jarida a Jihar Kaduna a yanzu suna gudanar da ayyukan su cikin walwala da natsuwa saɓanin yadda abubuwa suke a baya inda ya bayyana hakan a matsayin kokari na shugaban Ma'aikatan fadar gwamnatin.
A jawabin sa shugaban Ma'aikatan fadar gwamnatin Alhaji Sani Liman Kila ya godewa Ƙungiyar 'yan jaridar bisa ga wannan karramawa da s**a yi mishi, inda ya bada tabbacin yin aiki kafada da kafada dasu.
"Yan jarida mutane masu muhimmanci a cikin al'umma waɗanda suna iya buɗewa da rufewa duk lokacin da s**a ga dama, wannan karramawa da s**a yi mini ta zama abin alfahari a gareni kasancewata mutum na farko da ya samu irin wannan matsayi, ina baku tabbacin kofofin mu za su kasance a buɗe gareku a kowane lokaci".
17/08/2023
Wa zai gane wannan hoton?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the establishment
Telephone
Website
Address
Sultan Bello Road
Kaduna