Jaridar Azurfa
05/02/2026
WATA SABUWA: Ta Rabawa Manyan Hadimanta su 10 Naira Miliyan Daya kowannensu Domin Siyan Filaye a Zariya.
A wani mataki na nuna tsantsar kulawa, hangen nesa, da jajircewa wajen gina makomar Masu mata hidima, Fitacciyar mai Fafutukar tallafawa Mabukata da Marayu dake Zariya,Barrister Aysha Ahmad Mohammad (Addah) ta rabawa manyan yaranta guda goma 10 tallafin kuɗi har Naira Miliyan Daya 1,000,000,kowannensu wanda Jumla ya k**a Naira miliyan 10 domin su sayi filaye don tanadin gaba da cigaban rayuwarsu.
Wannan gagarumin tallafi ya zo ne a matsayin wani bangare na tsarin Addah Aysha na ƙarfafa yaranta domin su fara tanadi tun da wuri, tare da koya musu muhimmancin saka jari, mallakar kadarori, da dogaro da kai a nan gaba.
A cikin jawabinta, Addah Aysha ta bayyana cewa wannan mataki yana daga cikin burinta na ganin yaranta sun samu ginshikin rayuwa mai dorewa, tare da basu damar gina rayuwarsu bisa tsari mai kyau da hangen nesa.
“Ina son yarana su fahimci muhimmancin tanadi tun suna ƙuruciya. Mallakar fili ko gida yana daga cikin ginshikan tsaro da cigaban rayuwa, shi yasa na ga ya dace in tallafa musu tun yanzu,” in ji Addah Aysha.
Ta kara da cewa iyaye na da alhakin shirya ‘ya’yansu domin gobe, ba wai kawai ta hanyar ilimi ba, har ma da kayan more rayuwa da tsare-tsaren tattalin arziki da za su taimaka musu su dogara da kansu a nan gaba.
Cikin wadanda S**a Rabauta dun hada da Babban Mai Taimaka mata akan Kafofin Sadarwar Zamani Saifullahi Lawal Imam,da Babban Hadiminta kuma Direbanta Abbana H Abubakar,da P.A dinta Hajjo ,da Alamin Sunusi,da Fatima Hassan,Da Khady Suraj,sai Hajiya Uwale,Da Samira Abubakar da Jamilu Suleiman Bizara,wadanda dukkansu Manyan Hadimaine a Gareta.
Matakin Addah Aysha ya samu yabo daga al’umma da dama, inda ake kallonsa a matsayin abin koyi ga iyaye da shugabanni wajen kula da iyali da tsara makomar yara.
Masu sharhi sun bayyana cewa wannan tallafi ba kawai taimako ba ne, har ma darasi ne mai muhimmanci game da hangen nesa, jajircewa, da muhimmancin gina makoma tun daga yau.
18/05/2025
🚨🚨 Luka Modric ya shaidawa Real Madrid cewa a shirye yake ya rage albashinsa domin cigaba da zama a kungiyar a kakar wasa mai zuwa,
Jaridar Marca. 🤍🤜🏻
Wasu na ganin ya k**ata tsohon nan ya tashi ya bawa yara damar bugawa. Shi kuma ya nace.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kaduna