Computer Da Hausa

Computer Da Hausa

Share

Ku duba YouTube channel ɗin mu don samun bidiyoyin da muka yi.

25/06/2025

Kwana Biyu!

11/04/2025

A wannan bidiyon (minti 3), zaku ga yadda zaku iya yin designing flyer cikin sauƙi — ba tare da amfani da manyan effect-editing ba. Wannan basic editing ne: saka shapes, rubutu, colours, da hotuna. Yana da sauƙi kuma kowa zai iya yi.

Ku duba bidiyon a comment section.

22/03/2025

A 2024, na yi muku cikakken bayani akan Microsoft Word, wanda ya haɗa da yanda zaku koya typing na Hausa, Turanci, da Larabci, tare da duk wani editing da ake yi a MS Word ko ake yi ma wata takarda ko wani document, da kuma yanda ake amfani da keyboard, da yanda ake sakama computer wani yaren da bata da shi.

Waɗannan abubuwan da kuka koya, sune ake amfani da su wajen haɗa takardu (documents) a Microsoft Word na makarantu ko kasuwanci ko kungiyoyi da sauransu.

A bidiyoyin da zan yi kwanan nan zaku koyi yanda ake abubuwa kamar haka:

1️⃣ Rubuta Wasiƙa (Letter) – Formal, informal, official, & personal letters.

2️⃣ Ƙirƙirar CV – Takardan neman aiki

3️⃣ Aikin Project na makaranta
• Shafin Take (Cover/Title Page)
• Shafukan Farko - Preliminary pages (Acknowledgment, Dedication, Abstract, TOC, da sauransu)
• Body (Main Content Formatting)
• Conclusion
• References

4️⃣ Ƙirƙirar Takardun Makaranta
• Tambayoyin Jarabawa (Exam Questions & Answer Sheets)
• School Reports & Assignments
• Ƙasidu

5️⃣ Ƙirƙirar Takardun Kasuwanci
• Invoice da Receipt

6️⃣ Ƙirƙirar Bayanai na Kungiyoyi da Ma’aikatu
• Meeting Agenda & Minutes
• Reports

Waɗannan skills ne wanda duk wanda ya koya Microsoft Word ya kamata ya iya, domin sune mutane suke biyan kuɗi s**e a yi musu, kuma amfanin koyon skills ɗin kenan, ya zama wata hanya ce da kuɗi ke shigowa hannun ku bayan kun bada lokacinku kun koya.

Waɗannan wasu daga cikin abinda ake yi da Microsoft Word kenan, masu buƙatar koyon wani abun, su rubuta a comment section.

Want your business to be the top-listed Media Company in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Kaduna
800213

Opening Hours

Monday 09:00 - 19:00
Tuesday 09:00 - 19:00
Wednesday 09:00 - 19:00
Thursday 09:00 - 19:00
Friday 09:00 - 19:00
Saturday 09:00 - 19:00
Sunday 09:00 - 19:00