Sunnatur-Rasul
27/05/2018
03/03/2018
Riga Babu Wuya 002 (Agaji Mai Dorewa da Agaji Mai Yankewa)
Babu Kunya Ba Tsoro A Yau
Mun Yi Niyyar Bayyana Gaskia
-Marigayi Abubakar Ladan
Kafin nan don Allah in baka karanta rubutun da yagabata ba to baka bukatar karanta wannan, domain karanta rubutun da ya gabata danna link dake kasa:
https://www.sunnahnewsnigeria.com.ng/?p=2990
AGAJI MAI YANKEWA:
Abinda Yasa Ake Raina 'Yan Agaji
1. Wasu daga 'yan agajin basu tsayawa suyi karatu ko kuma Sana'a ballantana su iya daukan nauyin dawainiyyarsu, su kuma da s**a baiwa masallatai rayuwar su masallatai baza su iya daukar nauyin su ba, hakan yake sa su koma maula ko wani Abu makamancin hakan.
2. Karatu: idan dan agaji ya tsaya yayi karatu to tabbas shima wataran zai ga 'yan agaji suna agaza masa domin yayi karatu, amman kash mafi yawa tunanin su shine suyi ta yin gaba a harkar agajin kadai yana tare da malam wane idan ya tsufa kuma ya zama tare da Dan gidan malam wane da ya zama malami.
Mafi yawa daga maluman mu basu yi wani agaji ba in ka gansu ma da kayan agaji wani dalili ne kawai ma'ana na ado ne ba wai aikin again s**a yi ba, malaman da Tun tasowarsu yan agaji ne kuma s**a zama Malamai to tsiraru ne, sai dai in malami yana son karawa kansa wata inkiya sai ya fada agaji, sunan wannan agajin AGAJI MAI 'YANCI domin su babu wanda suke takewa baya hassalima babu wani training da suke zuwa sai kaji an basu wani mukami ma a tafiyar, Allah sarki talaka.
'Ya'yan Malamai Basa Agaji:
Mafi yawa Malamai basu yarda 'ya'yan su suyi agaji ba, suma yanzu idan akace ka kawo 'ya'yan wani malami dake agaji to tsiraru ne, akwai wannan babban malami wataran ina tare dashi sai 'yan agaji s**a zo wurinsa dansa karami yana zauna sai yace "Abba nima ka sani a agaji" sai malam yace "kai yi mana shiru agajin banza aikin wahala, makarantar za kayi ko agaji? Kar na kara jin irin wannan"
Abinda ya tsaya min a rai matuka malam ya juyo sai jikinsa yayi sanyi aka cigaba da gaisawa ya manta da 'yan agaji a wajen.
Tabbas idan Allah ya hada Dan agaji da Malamai marasa tsoron Allah to shima yaga ta kansa, ba zasu taimakeka kayi Sana'a ko kayi karatu ba sai da su taimakeka ka cigaba da dawainiyya dasu da iyalansu.
Shin Ko wanne agaji ne mai Dorewa?
Sai a rubutu na gaba.
Bara na rufe da wadannan baitoci na Mal. Abubakar Kantama a wakarsa mai taken "Sai I. Kowa ya tallafa islamu ya kan iya cigaba"
"Wallahi Ku tashi mu yunkura, Ku mu farga mu bar sanyin jiki
Mu rike duka umarnin gwani makadaicin sarki khaliqi
Duk wanda yake kin Taimakon musulunci ya rasa arziki
Kowas saki reshe ya rike ganye bamu san manufarsa ba.
Addinin nan da dukkan musulmi Ke tunkaho dashi
Da bazarsa muke rasa wasu na neman photo dashi
Kuma yanzu musulumi sai s**ai masa ko in kula s**a yada shi
Yau an rasa masu kula dashi kowa hidimarsa yasa gaba.
Basheer Journalist Sharfadi
Sharfadi.com
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Address
Bauchi
Jos
ABUJANIGERI