Ambato Foundation Plateau State Chapter

Ambato Foundation Plateau State Chapter

Share

19/03/2026

FADAKARWA AKAN SALLAR IDI

Ita Sallar Idi Sunnah ce mai girma, wadda ake yi domin nuna godiya ga Allah bayan kammala azumin watan Ramadan.

👉 Lokacin ta:
Ana yin Sallar Idi ne daga hudowar rana har zuwa zawali (kafin rana ta kai tsakiyar sama).
👉 Hukuncin ta:
Sunnah ce mai ƙarfi ga duk musulmi maza da mata su halarta.
👉 Idan aka rasa ta:
Ba a rama Sallar Idi idan mutum ya rasa ta ko kuma lokacin ta ya wuce.
👉 Abubuwan da ake so a yi kafin fita sallah:
• Yin wanka
• Sanya kaya masu kyau
• Cin wani abu (kamar dabino) kafin fita
• Yin takbiri (Allahu Akbar…) har zuwa lokacin sallah
👉 Muhimmanci:
Sallar Idi tana haɗa al’umma, tana ƙara ƙauna da zumunci, kuma tana nuna farin ciki da ibada.

Allah ya karɓi ibadunmu, ya sanya mu cikin masu rabauta. Ameen.

©Ambato Foundation Social Media

11/03/2026

SALLOLIN DA AKE GABATARWA NA CIKIN DARAREN WATAN RAMADAN.

DARE NA ASHIRIN DA UKU (23)

Rakaa Hudu (4) Sallama Biyu (2), kowace Rakaa Fatiha da
Izajaa 5,
Kulhuwa 5.

Bayan an idar YA HADI 100.

ALLAH YA KARBI IBADUNMU🤲🏻

© Ambato Foundation Social Media (AFSOM)

08/03/2026

SALLOLIN DA AKE GABATARWA NA CIKIN DARAREN WATAN RAMADAN.

DARE NA ASHIRIN (20)

Rakaa Goma (10) Sallama Biyar (5), kowace Rakaa Fatiha da
Inna Anzalnahu 1,
Kulhuwallahu 3.

Bayan an idar YA SHAHIDU 100.

ALLAH YA KARBI IBADUNMU🤲🏻

©Ambato Foundation Social Media (AFSOM)

Want your organization to be the top-listed Non Profit Organization in Jos?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Bauchi Road, Jos North.
Jos