Mairakumi

Mairakumi

Share

MAIRAKUMI 🐪
Muryar Jama’a | Gaskiya ita ce Manufar mu
Politics • Awareness • Arewa Voice
For a Better Nigeria 🇳🇬

Muna Nan Tare Daku Kwana bakwai Awa Ashirun Da Hudu 24/7 Tashar MAIRAKUMI Taku Ce Labarai Da Dumi Dumin Su

09/10/2025

DA DUMI-DUMI: Gargaɗi ga ƙasashen Afirka musamman Najeriya da Arewa: A yi hattara da magungunan tari daga Indiya

Gwamnatin Indiya ta gano wasu manyan matsaloli wajen gwajin magungunan tari da wasu kamfanonin ƙasar s**a ƙera, bayan da aka danganta mutuwar yara 17 da shan magungunan da s**a ƙunshi sinadarin diethylene glycol, wani guba mai haddasa lalacewar koda, jijiya da ma mutuwa.

Rahoton majiyar Muryoyi ta jaridar Reuters ya bayyana cewa magungunan da ake bincike sun haɗa da Coldrif, Respifresh, da RELIFE, waɗanda aka samu da sinadarin da ya fi na daidaitaccen ƙima sau 500.

Muryoyi ta ruwaito wannan matsala ta janyo hankalin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wadda ta yi gargadin cewa Indiya ba ta kula sosai wajen gwajin magungunan kafin su shiga kasuwa, abin da ke iya sa su yadu zuwa ƙasashen waje, ciki har da ƙasashen Afirka.

Masana sun ba da shawarar cewa jama’a su daina siyan magunguna ba tare da shawarar likita ba, kuma su tabbatar cewa kowanne magani da suke saya yana da rajista daga hukumar NAFDAC domin guje wa haɗarin guba da mutuwa.

KUN SAN MAGUNGUNAN?

28/09/2025

Ka fara kawo karshen Ta'addanci a Nageriya Kafin Neman muƙamin tsaro a majalisar Dinkin Duniya -Jam'iyyar ADC ga Shugaba Tinubu.

Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta soki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan yadda ta ke neman samun kujera ta dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UN Security Council), alhali kuma ana fama da matsalar tsaro a cikin gida.

ADC ta ce kafin gwamnatin Tinubu ta nemi irin wannan matsayi a duniya, ya kamata ta mai da hankali kan magance matsalolin tsaro da tsare-tsaren da s**a addabi ‘yan Najeriya – musamman hare-haren ‘yan ta’adda, garkuwa da mutane da kuma matsalolin rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

Jam’iyyar ta kuma yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta zuba jari sosai a fannin tsaro, ta ƙarfafa dakarun tsaro, sannan ta samar da hanyoyin da za su kawo sauƙi ga rayuwar al’umma kafin ta yi irin wannan babban buri a matakin duniya.

28/09/2025

"A Jigawa dai, lalacewar siyasata ba ta kai na kula gajiyayyen maula kamar Nafi'u Osamatu Kogga ba, ni Dankuda Kabo duk girmanka a Jigawa, idan ka taba Danmodi, zan taba Iyayan gidanka duk girmansu" - Jamilu Dankuda Kabo.

16/02/2025

Tabbas El Rufai ya taimaka min wajen zama shugaban kasa - Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jinjinawa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai, wanda ya bayyana shi a matsayin mutumin da ya bada gagarumar gudummawa wajen samun nasararsa a zaben da ya gabata. A sakon da ya aike masa na taya shi murnar cika shekaru 65 a duniya, Tinubu ya bayyana El Rufai a matsayin jigo wajen kafa jam'iyyar APC, wanda ake yaba masa saboda fasaharsa da kuma jajircewa. A saƙon da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya rabawa manema labarai, Tinubu ya yabawa tsohon gwamnan akan kokarinsa na gina dimokiradiya da yiwa kasa aiki da kuma goya matasa wajen koya musu dabarun mulki. Shugaban ƙasar ya ce El Rufai baya ga taimakawa wajen kafa APC, ya kuma taimaka wajen samun nasararta a zaben shugaban ƙasa na shekarar 2015 da 2019 da kuma 2023.

📷 Daily Trust

Want your business to be the top-listed Media Company in Hadejia?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Hadejia