TASKA

TASKA

Share

10/06/2023

Gwamnatin Nigeria ta harmata ayyukan kasuwanci na Binace

Hukumar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya ta haramta ayyukan kamfanin hada-hadar kuɗaɗen intanet na Binace a ƙasar.

Matakin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet.

Hukumar hada-hadar hannayen jari ta ƙasar ta ce kamfanin na Binance bai yi rajista da ita ba, a don haka ne ta ce ta haramta ayyukan kamfanin a fadin ƙasar.

Sanarwar ta kuma gargaɗi 'yan ƙasar da ke mu'alama da kamfanin da su dakata, in ba haka ba kuwa duk abinda ya same su to su kuka da kansu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ''An nusar da hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Najeriya game da shafin intanet da kamfanin Binace ke gudanarwa, inda yake neman 'yan Najeriya da su zuba jari kan harkar hada-hadar kuɗin intanet na cyrpto a shafin nasa da wasu manhajojin wayar hannu.

Kan haka ne hukumar ce bayyana wa 'yan ƙasar cewa ''kamfanin 'Binance Nigeria Limited' ba shi da rajista da hukuma, kuma baya aiki da dokokin hukumar kula da hannayen jari ta ƙasar, don haka duk abin da ya samu mutumin da ke mu'amala da kamfanin to ya kuka da kansa''.

Hukumar ta kuma shawarci 'yan ƙasar da su guji zuba jari a harkar hada-hadar kuɗaɗen intanet ta crypto a kamfanonin da ba su da rajista da hukumar.

Hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Najeriyar ta buƙaci kamfanin 'Binance Nigeria Limited' da ya gaggauta dakatar da ayyukansa a faɗin ƙasar.

Hukumar ta kuma ce za ta bayyana matakan ladabtarwa da za ta ɗauka kan kamfanin da wasu takwarorinsa marasa rajista a ƙasar.

Ta ƙara da cewa za ta yi aiki tare da hukumomin da lamarin ya shafa a ƙasar domin ɗaukar mataki game da batun.

A makon da ya gabata ne dai Hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta Amurka ta shigar da ƙarar kamfanin na Binance a gaban kotu.

A ranar Alhamis ne kuma kamfanin ya ce ya dakatar da hada-hada da kuɗin dala na Amurka bayan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka a kansa.

Wannna mataki dai ka iya kawo cikas ga kasuwar hada-hadar kuɗi ta intanet wato crypto a Najeriya, musamman ganin cewa a baya-bayan hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta ƙasar ta haramta ayyukan kamfanin Paxful.

17/07/2022

PRESIDENT BUHARI MOURNS FRONTLINE APC WOMEN LEADER, KEMI NELSON

President Muhammadu Buhari on behalf of himself and his wife, Aisha, commiserates with the Nelson family on the demise of frontline politician and advocate of the womenfolk, Chief Kemi Nelson.

The President also sends condolences to the Government and people of Lagos State, Presidential Candidate of the All Progressives Congress, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, and the Lagos APC family on the loss of "a consistent and faithful party member who devoted so much to the evolution, development, sustenance and relevance of the party in Lagos and around the country."

President Buhari notes the contributions of Chief Nelson as a former Commissioner for Women Affairs and Poverty Alleviation in Lagos State, the State Women Leader, National Deputy Women Leader of APC, and former Executive Director of the Nigerian Social Insurance Trust Fund, remarking that she was such a grassroots mobiliser and an achiever who left her footprints wherever she served.
“As the only female member of the Lagos State Governor’s Advisory Council (GAC), Kemi Nelson continued to be part of the governance structure that led to the transformation of Lagos State into the Centre of Excellence it has become,” he says.

The President prays that almighty God will grant the husband, Adeyemi Nelson and the family, friends and associates of the deceased, the fortitude to bear the loss and repose her soul.



Garba Shehu

Senior Special Assistant to the President

(Media & Publicity)

July 17, 2022

Want your business to be the top-listed Media Company in Hadejia?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address


Hadejia