FARIN GIDA TV
08/05/2026
Yanzu-Yanzu:
An yi garkuwa da manyan ’yan siyasa a Jigawa, Hon. Abba Anas Laushi da Hon. Ali Gantsa, a hanyar Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa, a daren jiya ne wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne s**a sace jigo a jam’iyyar ADC, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Guri, kuma tsohon ɗan majalisar tarayya tare da tsohon Kwamishinan Ilimi na Jihar Jigawa, Hon. Abba Anas Adamu Laushi, tare da amininsa Hon. Ali Gantsa.
An ce lamarin ya faru ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga Abuja.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani daga hukumomin tsaro ba dangane da yadda lamarin ya faru ko kuma inda aka kai su.
Al’umma da magoya bayansu na ci gaba da kira ga jama’a da su sanya su cikin addu’a domin Allah Ya kuɓutar da su cikin ƙoshin lafiya.
Farin gida TV
JARRABAWAR TANTANCE BUKATAR MALAMAI (TTNA)
Shugaban Hukumar Ilimi ta Matakin Farko ta Jihar Jigawa, Farfesa Haruna Musa, yana sanar da daukacin malamai cewa za a ci gaba da gudanar da jarrabawar tantance bukatar malamai a ranar Asabar, 04/04/2026.
Muhimman Bayanai:
Wadanda s**a riga s**a yi jarrabawar a baya kuma s**a yi submitting successfully, ba su da bukatar sake zuwa.
Domin tabbatarwa, za su iya duba exam slip dinsu da misalin karfe 5:00 na yamma.
Cibiyoyin da aka samu matsaloli, musamman a Federal University Dutse (Centre One), za a sake jarrabawar gaba daya.
Wadanda s**a fuskanci matsalar na’ura a Gumel, su duba dashboard dinsu domin sanin ko za su sake jarrabawa ko a’a.
Cibiyoyin Jarrabawa (Centres):
Dutse Zone: Federal University Dutse (har da Ringim – an tanadi centres guda 3)
Hadejia Zone: Bilyaminu Usman Polytechnic (a maimakon NITDA)
Gumel Zone: Jigawa State College of Education, Gumel
Kazaure Zone: Hussaini Adamu Polytechnic
Babura & Garki: Federal University of Science and Technology, Babura
Kafin Hausa: Sule Lamido University
Ana bukatar dukkan malamai su fara cire exam slip dinsu, wanda zai nuna cibiyar jarrabawa da lokacin rubuta jarabawar.
Za a fara fitar da exam slip daga yau da misalin karfe 5:00 na yamma.
Sanarwa daga:
Farfesa Haruna Musa
Shugaban Hukumar Ilimi ta Matakin Farko
Jihar Jigawa
27/03/2026
Shugabanin Matasan APC Uku Sun Mutu akan hanyarsu ta zuwa babbar taron APC
Wasu matasan APC uku daga Ogbadibo, jihar Benue, sun rasu a hatsarin mota a hanyar Makurdi zuwa Lafia yayin da suke zuwa taron jam’iyya na APC.
Sauran da ke tare da su sun samu raunuka kuma suna jinya. Allah Ya jikansu da rahama.
Abdullahi Isawa
26/03/2026
INNALILLAHI WA'INNA'ILAIHI RAJI'UN 😭
Allah sarki rayuwa kwana ya Kare
Wata mata kenan a ASIBITIN Murtala da ke Kano yadda ta haifi Yara Biyar amma tarasu bayan ta haife su 😭😭... Yar baiwa kenan muna mata Addua Allah yaji kanta da Rahama Yasa Aljannar Firdausi ta zama makomarta Ameen ya hayyu ya qayyum
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Hadejia General Hospital Road
Hadejia