Labaran Hausa 24/7
03/10/2024
Masarautar Saudiyya Ta Tabbatar Da Nadin Limamai Na Dindindin guda hudu A Masallatai Masu Alfarma!
Limaman Sune...
Masallacin Makkah: Sheikh Badr Al Turki da Sheikh Waleed Ash Shamsan.
Masallacin Madina: Sheikh Abdullah Al Qurafi da Sheikh Muhammad Barhaji.
Ƙungiyar Marubutan Arewa "Arewa Media Writers" Reshen Ƙaramar Hukumar Dukku Dake Jihar Gombe, Ta Ƙaddamar Da Gagarumin Taron Launching Din Shafin Yanar Gizo Wato Website Da Ta Baiwa Ƙungiyar "Dukku Community Progressive Association DCPA" kyauta
Dukku Community Progressive Dukku Community Progressive Association
17/07/2022
NDLEA ta k**a wata mata za ta yi safarar miyagun ƙwayoyi zuwa Oman
Hukumar hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa, NDLEA ta k**a wata mai suna Opoola Mujidat, da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi zuwa Oman, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Legas.
An k**a ta ne bayan hukumar ta k**a wasu fasinjoji biyu da ke tafiya Oman a ranar Litinin, 11 ga Yuli.
Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce an k**a fasinjojin biyu, Raji Babatunde Kazeem da Akinbobola Omoniyi kafin su hau jirgi.
“Fasinjojin, Raji Babatunde Kazeem da Akinbobola Omoniyi, suna tafiya tare zuwa kasar Oman dake Gabas ta Tsakiya a cikin jirgin kasar Habasha a ranar Litinin 11 ga watan Yulin shekarar na ta 2022 inda jami’an NDLEA s**a tare su a filin jirgin.
"A binciken da aka yi a cikin jakunkunan su, an gano kullin tabar wiwi da aka boye a cikin wata jaka dauke da kayan abinci, wanda Kazeem ke dauke da ita.”
“Nan da nan Kazeem da Omoniyi s**a sanar da jami’an yaki da miyagun kwayoyi cewa Mujidat da ke kusa da wurin ce ta ba su jakar da ke dauke da haramtattun kayan a filin jirgin, nan take kuma aka k**a ta.”
A cewar sanarwar, Mujidat ta yi ikirari cewa ta kawo kayan ne da nufin fasinjojin biyu su bawa mijinta dake can a kasar Oman din.
~Daily Nigerian Hausa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Digital
Gombe